Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 27

Chapter 27

A Dalilin Da Namiji Book 3 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

qwace mijin da take taqama da hurawa mutane hanci a kanshi. Shigowar abokan ango da shi kanshi angon ya sa suka basar kamar babu wani abu da ya shiga tsakaninsu. An sayi bakin amarya da manyan kudade da a tayin farko ba su ja da nisa ba suka sallama suna murna a kan garavasar da suka samu. Su Hafsa ne kawai aka mai da su gidajensu, amma qawayenta na Kaduna a nan gidan Amarya suka kwana. Yana kwance a dakin da yake a matsayin nashi, bayan ya fito daga wanka misalin qarfe goma sha biyu na dare, ya kira wayar Aisha fiye da sau goma amma ba ta dauka ba, har zai yi addu’ar barci sai ya yi tunanin, idan ya yi barci ba tare da ya nemi Yasmin don jin ko tana da damuwa bai yi mata adalci ba. don haka ya latsa kiran lambar wayarta, ringing daya, a na biyu ta dauka. Jin yana jiranta a dakinshi ya sa ta dauki rigar barci ta sanya ta qara feshe jikinta da turaruka masu qamshi ta nufi dakinshi. Da farko kuka ta saka masa sannan ta fara fadin maganganu a kan irin rashin adalcin da take ganin an yi mata. Bai bari qorafin ya yi tsawo ba ya ja ta zuwa jikinshi ya rungume sannan ya zura harshenshi a cikin bakinta. Take ya kashe duk wani qorafi nata tuni ta ba da kai bori ya hau. Ta fara qoqarin mayar mishi da martanin irin wasannin da yake yi mata. “Ashe dai abin ba a shekaru ba ne…” Bai san lokacin da zuciyarshi ta ayyana masa hakan ba, domin ji ya yi komai da komai na jikin Aisha ya ninka na jikin Yasmin girma da daukar hankali. Duk yadda ta so su zarce da wasannin ya qi yarda da hakan, a qarshe ta haqura tana rungume a faffadan qirjinsa har barci mai nauyi ya kwashe ta. Shi ma da yake tattare yake da gajiya barcin ne ya yi awon gaba da shi. Zuciyarshi cike da tunani da soyayyar Aisha. Qarfe hudu daidai ya farka, a hankali ya zame jikinsa daga na Yasmin, bandaki ya shiga ya yi wanka sannan ya dauro alwala. Nafiloli ya fara gabatarwa, ya yi addu’o’i masu tsawo a kan Allah ya ba shi ikon yin adalci a tsakanin matanshi, sannan ya yi addu’a mai tsawo a kan samun nasarar kama wadanda suka kashe Sadiya. Zai fita masallaci don sallar asubahi ya tashe ta amma yana ficewa ta sake maida kai ta kwanta. Yana daga cikin matsaloli manya da Yasmin take fama da su rashin gabatar da Ibada akan lokaci (Allah ya shirya). Bai fito daga masallaci ba sai qarfe bakwai da rabi na safe, yana komawa gidan ya gan ta dai dai a kan gado tana sharar barci, alamu sun gwada qarara ba ta yi sallah ba. Sake tashinta ya yi yana tsaye a kanta har ta sauka ta shiga bandaki sannan ya canja kayan jikinshi daga jallabiya zuwa shadda ya dauki mukullin motarshi ya wuce zuwa gidan Ardo bayan ya bar mata dan short note, inda ya tabbatar za ta iya gani idan ta fito bandakin. *** Su Aisha suna zaune a falo ita da Daddy misalin qarfe tara na daren ranar Talata, sun gama cin abincin dare. Qoqarin suke su qara kwantar wa da Aisha hankali don haka duka kalaman nasu nasiha da rarrashi ya fi yawa. Tun da aka daura auren duk ta bi ta tsangwami kanta ta qi sakin jikinta, shi ne abinda yake daga hankalinsu. Abdul kuwa har yau da ake kwanaki hudu da zamowarsu ma’'aurata ta qi ba shi hadin kan da yake buqata, balle har ya yi mata bayanin da za ta fahimce shi ta daina ganin laifinshi. Ta zame mishi kurma qarfi da yaji, zai zo ya zauna bayan gaisuwa ba ta qara yarda wata magana ta shga sakanin ta da shi. Duk surutun da zai yi ba ta um bare um-um. Sai dai idan ta gaji ya fice zuciyarshi cike da damuwa, shiyasa maimakon a gan shi ya yi qiba ya yi kyau, a matsayinshi na ango, sai dan wuya yake yi. Hatta Yasmin ta rasa gane kanshi, tun ranar daurin aure da ‘yan wasanni suka shiga tsakaninta da shi ba ta sake samun ko makamancin haka ba. ta yi kuka ta yi rarrashin ta yi masifar, amma duk a banza. Duk magungunan da turarrukan da aka hada mata tana amrfani da su amma bai shiga dakinta balle ta sa ran za su yi tasiri. Shi ya sa duk ta qosa su tattara su koma Kaduna, gurin aikinshi, kuma gurin iyayenta, tunda ta samu labarin ba yanzu Aisha za ta tare ba, amma ya ce sai ranar Lahadi, lokacin an yi kwanaki takwas da daura auren kenan. Qwanqwasa qofar falon da aka yi da qarfi ya sa Aisha ta zabura za ta shige dakinta ta kulle kamar yadda ta tsira a ‘yan kwanakin nan. Duk baqin da za a yi masu zuwa ganin amaryar Abdul ba ta yarda su gan ta, sai dai ta kulle kanta a daki ba ta sake fitowa har sai ta tabbatar sun tafi. Hannunta Mummy ta danqe sannan ta yi mata alamar kada ta tashi da idanuwanta. Yayin da daddy ya je ya bude qofar tare da ba da izinin shigowa ciki. Idanun Aisha suna qasa, sallamarshi da ta jiyo ya sa ta dago da sauri tana kallon shi. A zuciyarta kuma mamaki take yi. “Lafiya a daren nan!?” Da mamakin su ma suke kallon shi sai Mummy ce ta yi qarfin halin tambayar sa. “Abdul lafiya kuwa a daren nan?” Sai da ya sami guri ya zauna, sannan ya dan yi murmushin da da gani bai kai ciki ba ya ce “Lafiya qalau.” Ajiyar zuciya Daddy ya sauke, sannan ya yi dariya ya ce “Wallahi ka kada min hanjin ciki, yanzu fa tara da rabi na dare. Wane abu ne zai fito da danyen ango waje idan ba qwaqqwaran dalili ba.” “Hmmm! Daddy kenan! Ni wallahi a da da ba ni da auren ma na fi samun kwanciyar hankali da nutsuwa, kana ganin yadda kullum nake ramewa kamar wanda ake d'iba ana miya?” Ya fadi hakan yana qoqarin lalubo idanunta don ta san da ita yake yi. Su ma da yake ba yara ba ne duk sun fahimci inda maganganun nasa suka sa ba. ita kam ko kallo bai ishe ta ba, sai ma tsaki da ta yi qasa-qasa. “Haba Abdul, kada ka ba ni kunya mana, kamar ba jarumin dan sandan nan da na sani ba?” In ji Mummy kenan tana xan murmushi. “Hmmm! Allah dai ya yi mana magani… daman Ardo ke son ganin Aisha, shi ne ya umarce ni in zo in tafi da ita.” Sai a yanzu Aisha ta daga kanta tana kallon shi cikin tuhuma, a zuciyara addu’a take Allah ya sa dai ba qarar ta ya kai ba. “Toh fa! A wannan daren yake son ganin ta?” Daddy ya tambaya yana mamaki. “Qwarai kuwa, domin cewa ya yi qafata qafarta.” Ya amsa da tabbacin idanunshi suna cikin nata. “Allah ya sa dai ba laifi ta yi ba?” Mummy ta tambaye shi, fuskarta na bayyana damuwa. “Ni ina zan sani? Idan ta je can ta ji.” Ya

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});