Chapter 13
Chapter 13
daurin aurenmu ba, don buqatar kanka ne da kuma guje maka fada wa halaka.” Shiru ya yi yana qoqarin danne zafin da zuciyarshi take dad'a dauka a kan Yasmin, a yadda yake jin ranshi zai iya yi mata dukan kawo wuqa ya bar ta kwance a wurin. “Qarya kike yi Yasmin, ba ki isa ki raina min hankali ba, amma ina tabbatar miki za ki yi dana sani a can gaba. Kuma wannan auren da za a daura mana nan da kwana shidda ba shi zai sa in fasa auren Aisha ba, duk haukanki zakiyi ki gama, shashasha.” Qus ta yi har ya gama zazzage mata duk ruwan bala’in da ya qunso a cikinshi, domin ta san kadan daga aikinshi ne ya tsittsinka mata mari idan ta nemi yi masa rashin kunya. Don haka ta ja baki ta yi gum, sai hawaye da yake tsiyaya a idanunta. Kukan da ya ga tana yi shi ne ya dan sanyaya masa jiki, don haka ya kau da kanshi gefe ya ce “Kin san dai daga gobe har zuwa juma’a ina cikin aiki, zai yi wuya ki sake gani na a cikin wadannan kwanakin. Duk abinda kike buqata na shirye-shirye ki kira ni a waya zan aiko miki da shi. Ranar Juma’a zan wuce Yola da yamma, sai mun hadu a can.” Ba ta ce komai ba kuma ba ta daina kukan da take yi ba, sai ma qara armashi kukan nata tayi ta hanyar hadawa da shesshekar kuka da wani irin salo wanda dole ya sanyayar da jikin wanda aka yi domin shi. Ta yi nasarara tabbas, domin gaba daya ya dawo da hankalinsa kan ta. Cikin kulawa ya ce “Wai mene ne kuma? A tunanina murna ya kamata ki yi tunda burinki yana daf da cika?” Fuskarta jage-jage ta dago idanunta ta zuba a kanshi, murya na rawa ta ce “Ya za a yi in yi murna bayan Allah ya dora min son wanda sam ko daidai da qwayar zarra ba ya so na? Duk wani kuskure da kake ganin na aikata son ka shi yake tunzura ni gurin aikatawa. Me ya sa ba za ka ji tausayi na ba Yaya Abdul? Ina son ka son da har ban san iyakarshi ba, amma kar ka manta ba ni na dora wa kaina wannan jarabtar ba, Ubangiji da ya dora min shi ya san yadda zai yi da ni. Duk da ka qi yi min uziri a kan kura-kuran da na aikata, hakan ba zai hana in durqusa har qasa in ba ka haquri ba. Don Allah ka yafe min Yaya Abdul.” Take ta zame daga kan kujerar zuwa qasa ta daga hannayenta biyu sama alamun roqo tana ci gaba da jan majina da tsananta zubar da hawaye. Ta yi matuqar ba shi tausayi. Nan take ya fara tunanin idan shi ne Aisha take masa irin abinda yake yi wa Yasmin ya zai yi da ranshi? Don haka a take ya yi alqawarin daina ganin laifinta a kan duk wani abu da za ta aikata. Kamo hannunta ya yi ya zaunar da ita a kan kujera, cikin murya mai dauke da alamun rarrashi ya ce “Ni ban ce ba na son ki ba Yasmin, ke din ce har yanzu ba ki fahimce ni ba. Amma komai ya wuce, kuma daga yau kada ki sake cewa ba na son ki.” “Da gaske kana so na Yaya Abdul?” Ta tambaye shi cikin murna da zumudi. “Qwarai kuwa Yasmin, qila ma har fiye da yadda kike so na.” “Allah na gode maka... Na gode maka ya Allah. Allah ka tabbatar da soyayyata ni kadai a zuciyar Yaya Abdul.” Bai amsa wannan addu’ar tata a fili ba, da sauri ya amsa da “Ba amin ba” A zuciyarshi. Ganin yadda take murna sai ya ji sam ba ya son bata mata rai a wannan dare. “Yanzu dai kin ga dare ya yi, zan tafi. Ina fatan kin ji duk abinda na fada miki.” Marairaice fuska ta yi cikin salon shagwaba ta ce “Yanzu ba zan sake ganin ka ba har sai mun je Yola ranar Juma’a?” “Haquri za mu yi, kin san yanayin aikina, ba ni da wani ishasshen lokaci.” “Amma dai Yaya Abdul hutu za ka dauka bayan bikinmu ko?” Ta sake jefa masa wani qorafin. Ya qosa ya koma gida, domin lokacin da ya saba kiran Aisha su yi hira har sai barci ya dauke ta har ya gota da minti ashirin.” “Eh, in Allah ya yarda.” Ya amsa mata a gajarce. Ta lura da qosawarshi, da tsoron kada liqin da ta yi ya valle ya sa ta ce, “Shi kenan mijina, ina son ka sosai, don Allah ka daina qin daukar wayata a duk lokacin da na kira ka. Kuma kai ma ka ringa kira na don Allah ka ji mijina?” Ta roqe shi a marairaice. “Kada ki damu, na yi alqawarin kiranki idan na samu lokaci. Kuma zan ringa daukar wayarki matuqar kin kira a lokacin aiki bai yi min tsanani ba.” Ya fadi haka yana murmushi, sukai sallama. Farin ciki fal zuciyar ta yayin da shi kuma ba yabo ba fallasa sannan ya yi umarni a gare ta ta isar masa da gaisuwa gurin Baffanshi. Har ta qule zuwa cikin gida bai tada motar ba, kuma bai daina kallon hanyar qofar get din gidan ba ta inda ta shiga. Minti biyar bayan shigar ta cikin gidan lokacin agogon motar ya nuna sha biyu na dare saura minti goma. Motar aka danno da gudu kai tsaye aka nufi babbar qofar get din gidan, tun daga nesa ake danna hon ba qaqqautawa. Ita ta ja hankalinshi daga kan wayarshi da yake ta danna kiran lambar Aisha, amma sam ba ta dauka ba, hakan shi ya ba shi tabbacin ta yi barci. Bai gaza gane motar Abba ba ne take wannan mahaukacin gudu da hon din, kuma haske ne tar a qofar gidan. Sai da ya bari mai gadi ya bude qofar ya shiga da motar ciki sannan ya bi ta dan qaramin qofar gidan ya shiga ciki ya tsaya can kusa da fulawoyin gidan, gurin da idan wanda ya fito daga motar bai yi waige ba ba zai iya ganin shi ba, amma daga inda yake tsaye yana iya ganin komai da yake faruwa a gurin motar Abban. Sai da maigadin ya maida qofar get din ya kulle hade da sanya kwad'o ya datse, gurin motar Abba ya nufa da gudu ya bude qofar direba. A buge ya fito da Abba domin kasa tsayawa da qafafunshi ya yi sai da taimakon maigadin, fiye da rabin jikin Abban yana jingine da jikin maigadin. Sai da suka shige cikin dakin Abba sannan Abdul ya fito daga maboyarsa ya bi bayansu har zuwa jikin tafkeken windon da ke jikin falon Abban. Da yake dare ne kuma haske ne tar a cikin falon, don haka yana ji kuma yana ganin duk abinda yake faruwa. Tun daga tsakiyar falon Abba ya fara kwara amai don haka maigadin ya tsugunar da shi a qasa yana jera masa sannu, har sai da ya tabbatar Abba ya gama aman. Zagi Abba ya fara surfa masa cikin maye da buguwa amma hakan bai sa maigadin ya fasa aiwatar da abinda yake yi ba.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31