Chapter 7
Chapter 7
riga da qananan kaya sune shigar da aka raine ni da su. Ban tava sanya irin wadannan kayan ba sai da Mummy ta dinka min. Ashe dai sun yi min kyau?” Ta tambaye shi da mamaki a fuskarta. “Au, ke ba ki ga ni ba?” ya tambaye ta shi ma da mamakin a fuskarsa. “A’a ni ban gani ba, kawai dai gani na yi sun yi min yadda duk wani kaya da na saka yake min.” “Ki gode wa Allah matata, wallahi ban tava ganin yarinya mai kyanki ba, ko wani kalar kaya kika sa sai ya karvi jikinki, a kullum kamar qara miki kyau ake yi.” “Alhamdulillahi! Allah ya sa dai ba don kyaun kake so ba, ka ga idan haka ne duk ranar da ka ga wacce ta fi ni kyau za ka daina so na" Sauka daga kan titi ya yi sannan ya yi fakin din motar, ya kamo hannunta jikinshi a sanyaye ya ce “Haba matata, ki daina batun zan daina son ki, ko kin manta don ke aka halicce zuciyar Abdul-Ahad? Daina son ki yana nufin ba na raye a duniya, domin ko hauka nake yi ba zan daina ambaton sunan Aisha da irin son da nake yi mata ba. Wallahi ina son ki, so na tsakani da Allah. Ki daina kokwanto ko shakka a kan irin son da nake yi miki kin ji matata?” Tsakiyar qwayoyin idanunta ya zuba nashi idanun suna kallon juna cikin tsantsar so da qaunar juna. Ya riga da ya gama kashe mata jiki da tausasan kalamanshi, a muryarta zai gane tsantsar so da yarda da aminci da sakankancewa. Ta ce, “To na ji, mu tafi dare ya fara yi.” “Kin ji fa kika ce, matata? Ba ki ce kin yarda ba...” “Na yarda mijina.” Ta amsa mishi kai tsaye. Tada motar ya yi suka ci gaba da tafiya inda suka nufa. Ya ci gaba da cewa "Ina son ki matata, ina ma a ce an kawo min ke a matsayin matar aure na ne?” “Ai ni matar taka ce, ko ka manta abinda Ardo ya fada kafin mu fito daga gida?” “Ban manta ba, amma ai kin ji ya ce ban biya sadaki ba, kuma dubban jama’a ba su shaida ba.” “Ai ka kusa samun damar mallakar matarka in Allah ya yarda mijina.” “Allah ya nuna mana lokacin.” “Amin mijina.” Ta amsa kai tsaye ba tare da jin kunya ko tsoro ba. *** Yau kwanaki uku kena tana kwana da wayarta a bude, kuma kusa da kunnenta don tsammanin samun kiran wayar Aisha kamar yadda “Arne na kan tudu” ya alqawarta mata. Ganin kwanaki biyu sun shude ba ta samu wayar Aisha ba kuma ba ta ji wani motsi daga Arne na kan tudu ba, kamar yadda ya ce idan ba su samu nasarar shiga jikin Aishan ba to zai dauki ladan aiki a jikinta. Don haka ta yanke shawarar qara masa wasu kwanaki biyun su zama hudu kenan. Tana fatan samun nasara a muguwar buqatarta. Duk ‘yan matan da suke debe mata kewa a wannan kwanaki ukun ta hana su shiga dakin barcinta. Babban burinta shi ne idan Aishan ta kira ta su yi hirar da zai rage mata qarfin sha’awar Aishan a zuciyarta. Tana kwance ta yi daidai a kan gadon daga ita sai yaloluwar rigar barci mai bayyana surar jiki, idanunta a bude suke ta qurawa P.O.P da ya mamaye saman rufin dakin ido, tana tunanin qirar jikin da Aisha ke da shi. Lokaci zuwa lokaci tana sakarwa kanta murmushi sa’annan ta shafa tumbin cikinta cikin nishadi. Dif wutar dakin ta dauke ba zato ba tsammani, tsaki mai qarfi ta ja sannan ta janyo wayarta da niyyar kiran daya daga cikin ‘yan matan gidan. Dawowar hasken dakin ya sa ta sakin ajiyar zuciya ta aje wayar a gefe ta ci gaba da tunanin da take yi. “Ke muguwa,,,,” Cikin tsawa mai qarfi ta ji muryar ‘Arne na kan tudu’ ya yi amsa kuwwa a cikin dakin yana qwala mata kira. A tsorace ta miqe daga kwanciyar da tayi tana waige-waige, amma ba ta gan shi ba kuma komai na dakin yana nan a inda yake. Cikin sakan biyar muryar Arne na kan tudu ta ci gaba da karade lungu da saqo na cikin dakin, da qaraji yake qwala mara kiran amma ba ta gan shi ba. Da sauri ta dira daga kan gadon, ba ta tsaya neman zani don rufe tsiraicinta da rigar barcin ta bayyana ba ta nufi qofar dakin da gudu a tsananin tsorace, niyyarta ficewa daga dakin. Duk yadda ta so bude qofar dakin ya qi buduwa, murda key din dakin take don budewa amma kamar tana sake datse qofar, kuma har a wannan lokacin Arne na kan tudu bai daina qwala mata kira cikin tsawa ba. A rud'e ta zame ta zauna a qasa jikin qofar sharaf sannan ta sanya ‘yan yatsunta duk biyu ta toshe kunnuwanta gami da rintse idanunta da qarfi, duk da ba wani abu take gani ba. Turirin zafi mai tsanani hade da tsamin barasa da hamamin warin da yake doso ta ne ya sa ta bude idanunta don gani ko me yake kusanto ta. Yana zaune a kan dan dutse mai tudu shi ba a sama ba kuma shi ba a qasa ba. Sanye da da dan yaloluwar riga wace take bayyana rama da qasusuwan jikinshi. Duk jikinshi hayaqi yake fitarwa mai hade da tururin zafin wuta. Idanun shi sun yi jawur fiye da yadda ta saba ganinshi. Da hannunshi mai dauke da rudu-rudun jijiyoyi yake watso mata daquwa sannan ya varke da wata mahaukaciyar dariya, lokaci guda ya turvune fuska gami da fashewa da kukan gyare. Saida ya tsagaita sannan ya fara magana “Keh muguwa! Kin bamu aikin da ya fi qarfinmu! Kin sa na tura dan tsumuri inda za a yi sanadin hallaka shi, to ya dawo da alwaqarin ba zai mutu shi kadai ba, don haka ya dau fansarshi a kaina ta hanyar watsa min tokar da za ta yi ajalina. Don haka ni ma ba zan mutu ni kadai ba sai tare da ke baqar muguwa.” Toka mai tsananin zafi ya watsa mata tun daga kanta har zuwa sassan jikinta. Saukar tokar a jikinta da wani azababben zafi da ta ji yana ratsa qwaqwalwarta ya sa ta yanka ihu mai tsanani yayin da shi kuma Arne na kan tudu ya bace vat! yana ci gaba da rera kukan gyare da babu dadin saurare ko kadan. Kamar yadda jikin Arne na kan tudu yake fitar da hayaqi da wari da hamami cikin minti biyu ita ma jikinta ya fara fitar da haka. Azabar da take ji a jikinta kamar ana zuba mata garwashin wuta ya sa ta ringa yanka ihu tana yage dan yalolon rigar jikinta tana jefarwa. Daga can wajen qofar dakin ‘yanmatan gidan suke dukan qofar suna qwala ihun kiran “Hajiya lafiya!?” Ina! Hajiya Danasha ta yi nisa sam ba ta san suna yi ba, ihu kawai take yi tana birgima a qasan dakin saboda azaba. A hakan ta ci gaba da kasancewa har qarfe biyu da rabi na dare, sannan rai ya yi halinsa. ‘Yanmatan gidan sam ba su da masaniyyar Hajiya ta cika, koda suka daina jin ihunta sai suka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31