Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 18

Chapter 18

A Dalilin Da Namiji Book 3 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

dole daga yau har bayan biki” Tana gama fadin haka ta katse wayar, ta miqa wa Zainab tana murmushi ta ce “Ya ce in ba ku dubu dari da hamsin.” Tsallen murna suka fara yi yayin da Aisha ta bi su da kallo daya bayan daya tana murmushi. “Uhm, Babyna kin yi wankan kuwa?” Mummy ta jefo wa Aisha tambayar bayan ta tsare ta da idanunta. Sosa qeya ta fara yi domin ta san kwanan zancen. Cikin muryar shagwava ta ce “Mummy tunda na shiga daki Zainab ta kira wayata ta ishe ni da surutu shi ya sa ban samu na yi ba har suka iso.” “Ba ruwana wallahi Aunty, saurayi ne ta tsaya hira da shi ko da muka shiga dakin fiye da minti ashirin ko kallonmu ba ta yi ba, sai ni ce ma da na gaji da jiran ta na amshe wayar na katse bayan na yi masa tsiyar ya qyale ta su gaisa da ‘yan’uwanta.” Da sauri ta fadi haka don kare kanta tana kallon Aisha cikin tsokana. Harara Aisha ta watsa mata, tare da qwafa mai isar da saqon zan kama ki ne. Wani irin zabura Mu’azzam ya yi, wanda ya sa kowa mamaki, bai damu da irin kallon tuhumar da kowa na falon ke mishi ba ya watso idanunshi kan Aisha ya ce, “Wane irin saurayi kuma? Kina nufin har kin iya zance da wani a waya?” Harara ta watsa masa tare da murguda baki, duk a lokaci daya, sannan cikin masifa ta zabura kanshi tana fadin, “Oho, ina ruwanka?” Dariya ya yi ganin yadda ta maida masa da maganar ya ce “Allah ya huci zuciyarki, maida wuqar ba ni na kar zomon ba.” “Kanka ake ji de" Ta sake fada cikin masifa. Sannan ta maida ido kan Mummynta sai a wannan lokacin ta fahimci tun dazu idanunsu yana kan ta. Kunya ce ta kama ta don haka ta yi qasa da kai tana dariyar rashin gaskiya. “Babyna masifa ko? Da har ina tunanin za a ringa cin zalinki ashe kar ki ke kallon mutane? To maza ki je ki yi wanka za ku shiga kasuwa yanzu.” Sun sum ta miqe ta nufi hanyar dakinta don cika umarnin Mominta. Tana jin su Zainab suna yi mata dariya amma ko waigowa ba ta sake yi ba. Bayan fitowarta wanka ne kiran Abdul ya shigo wayarta, yana daf da tsinkewa ta dauka tana yamutsa fuska kamar yana kallon ta. “Matata...!!" Ya kira ta da sunan da ya fi so ya kira ta a karo na uku. Ciki-ciki ta amsa, domin ta fahimci saqon da ya ba Mummy ne ta ce sai dai ya yi haquri yake neman jaddada mata bakinshi da nata. “Matata wai don kawai na ce wa Mummy kada ta bari ki shiga kasuwa sai na zo shi ne ta ce in yi haquri, don Allah na yi laifi kenan? “A’a, ai kai ba ka laifi.” Ta amsa masa cikin gatse. “Yauwa matata. Shi ya sa a kowane bugun daqiqa na agogo nake qara son ki. Ki bari idan na zo sai mu shiga kasuwar tare kin ji ko?” “saboda me?” Ta tambaye shi cikin tsiwa tana yamutsa baki. “Saboda kada wasu mazan su kalle min ke.” “Wadannan dokokin ai ba da ni suka dace ba Modibbo, ka fi ni sanin a inda suka dace. Don haka fita daga yau har bayan bikinka sai inda mai ya qare.” “Daga magana sai cibi ya zama qari?” Ya tambaye ta cikin dariya, domin ya fahimci zallar madarar kishi ne ke cin zuciyarta. Don haka ya maida abin wasa. “Oho maka dai" “Allah ya huci zuciyar matata, ba na son kina vata ranki a kan abinda bai kai ya kawo ba.” Ya fadi hakan cikin rarrashi da salon kwantar da hankalin wacce ake so. Ajiyar zuciya ta sauke wani sanyi yana kwarara a zuciyarta ta ce “Abdul wallahi ina son ka.” “Na sani matata, amma wallahi ina miki so fiye da wanda ki ke min. Ki yi haquri, haka Allah ya qaddara sai na fara auren wata matar kafin ke. Dacin da nake ji a zuciyata wallahi ya ninninka wanda kike ji a taki zuciyar. Ki yi haquri kin ji?” Zuciyarta fes da farin ciki ta ce ”Shi kenan na ji, yanzu dai su Zainab suna jira na a falo, bari in shirya mu shiga kasuwar.” Cikin qunci da qunar zuciya ya yi mata fatan shiga kasuwa da fita lafiya, kishin da yake ji na son Aisha a zuciyarshi sam yana baqin ciki wani namiji ya kalle masa ita. Kawai don dai yana tausar zuciyarta game da aurenshi da Yasmin ne shi ya sa yake bin ta a hankali, yana hadiye kishinshi a kan ta. *** Mu’azzam irin mutanen nan ne masu saurin shiga ran mutum, saboda kirkinsu da barkwancinsu. Cikin kwanaki uku shaquwa mai tsanani ta shiga tsakaninsa da Aisha. A kullum sai ya kawo mata ziyara har gida, yana yawan siyo mata kayan qwalama tunda ya fahimci abinci bai dame ta ba. Amma ko ya kawo sai dai ta kawo filet ta zubo mishi ya ci abinshi, bai fi ta dauki guda daya ko abu biyu ba. Mummynta da dadinta suna farin ciki sosai, domin suna qaunar duk wanda zai kula musu da ita, musamman a wannan lokacin da ta fi buqatar rarrashin mutane don a taushi zuciyarta saboda auren Abdul da a kullum yake qara matsowa. A 6oye Daddy ya ba Mummynta kudi masu yawa ta je ta dauki yayyinsu mata guda biyu suka shiga kasuwa suka hado wa Abdul lefe, kai tsaye daga kasuwar gidan Ardo suka wuce da kayan, Ardo da mutanen gidan sai shi wa Daddy da Mummy albarka suke yi. suna fatan Allah ya qara zumunci da arziqi. A taqaince dai auren gata aka shirya yi wa Abdul da Yasmin, kamar yadda ake yi ga kowane da ko jika na cikin zuri’ar, mahaifin Abdul shi ya yi kayan dakin amarya masu matuqar kyau da tsada, wai don ma dai bikin ya zo a qurarren lokaci kenan! Baffah Ahmadu mahaifi ga Yasmin shi ya biya ma Abdul sadaki Naira dubu talatin kamar yadda qanin Ardo Alhaji Ibrahim ya yanka mishi. Baffa Yahaya shi ya ba ango kyautar gida mai kyau a nan Yola wanda za a saka amarya. Duk yawan zuriyarsu kowa rige-rige yake gurin yin bajinta, domin samun tabarraki daga gurin mahaifinsu. Tabbas sun yi bajinta, zuwa ranar Laraba an gama komai na shirin biki, hatta gidan Amarya da Ango an zuba komai na gani na fada. A ranar Alhamis ne ana saura kwana biyu a daura auren aka shirya za a sanya lallen amarya a gidan Ardo, da misalin qarfe hudu na yamma, kamar yadda suka saba ga duk diyar da za a aurar a cikin zuri’ar. Qarfe tara na safiyar ranar Alhamis a gidansu Aisha ta yi wa su Zainab, tun a daren ranar Laraba suka sanar da ita ta shirya za su tafi saloon a safiyar ranar Alhamis, don haka ko kafin su iso tuni ta yi wanka ta shirya. Suna zaune a kan dinning da iyayenta suna karyawa. Qarfe goma daidai suka bar gida. Mu’azzam shi ne ya dauki dawainiyar kai su duk inda za su je a motarshi, amma ta ji su Zainab suna fafin

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});