Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 20

Chapter 20

A Dalilin Da Namiji Book 3 Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tana zuba ruwan bala’i. Qarfe biyar na yammacin ranar Alhamis suna gidan Ardo, har an fara gudanar da sa lallen Amarya. Amaryar ta yi kyau sosai cikin wani material mai ruwan madara mai matuqar kyau da d'aukar ido. "Da yake amarya duk muninta ranar aurenta sai ta yi kyau kalli Aunty Yasmin kamar ba ita ba.” Zainab ce ta ke wa Aisha wannan tsegumin. Suna zaune a dakin kakarsu wacce ta haifi mahaifinta. Suna shiryawa cikin nasu kayan ankon da suka yi niyyar sakawa a yau. Dariya kawai Aisha ta yi tana kara gyada hirar fuskarta tace “Na riga ki a zuci kin riga ni a baki. Ni kaina na yi mamakin yadda ta yi kyau ashe duk qyallin amarci ne.” Dariya suka kwashe da ita gaba dayansu, sannan suka ci gaba da abinda yake gabansu. Gidan ya cika danqam da ‘yan’uwa da abokan arziqi, an sanya fararen kujeru gwanin ban sha’awa, gurin da Amarya take zaune shirin da aka yi masa daban ne, ya fi ko’ina qayatuwa da kayayyakin kwalliya iri-iri. “Kai amma wallahi kin yi kyau sosai Smally. Ina ma ni ce ke da wannan kyakkyawar sura da Ubangiji ya halitta ki da ita.” Zainab ce ta fadi haka bayan duk sun gama shiryawa cikin riga da siket na wani tattausan material baqi da dan ratsin ja a jikinshi. Sai da ta harare ta sannan ta ce “Tunda ba ki gode taki surar da Allah ya yi miki ba, ai sai ki canja halittarki.” “Ni dai ban ce haka ba, Alhamdulillahi.” Ta fada cikin hanzari. “Tabarakallah Smally, gaskiya mijinki zai kwashi gara, irin wannan cikar qirji da baya haka? Irinku idan aka aure ku ba a barinku fita saboda kyawun halittarku.” Ilham ce ta fadi hakan tana qara fesa wa Aisha turare a duk sassan jikinta. “Hmmm! Ai ni na ma rasa ta cewa... amma dai ki qara gode wa Allah kawai Smally. Bambancin ku da kyawawan Larabawa kawai fatarki da ba ta qarasa kai tasu haske ba, a hakan ma sai ina ga kamar kin fi Larabawan kyau.” In ji Maryam kenan da ta yi za zaune tana qare wa Aisha kallo daga sama har qasa. “A duk cikin taron nan ba na jin za a sami wacce ta yi ko da rabin kyan da kike dauke da shi Smally, gaskiya ke daya ce a cikin miliyan!” Nuratu ta fadi hakan. Sai da ta gama kallon su daya bayan daya, sannan ta yi fari da ido ta ce “Ku ci kanku ku sha baqin ruwa, na ci na sha ba don ku ba.” Dariya suka suka kwashe da shi gaba dayansu, har da ita da ta yi maganar. Zainab ce ta yi qwafa ta ce “Dad'ina da ke sam ba a miki gwaninta.” “Eh din! Ya za ku ringa kai ni inda ban kai ba, bayan ni sha’awar kyanku nake yi.” “Hmmm! Allah ya shirye ki Smally, ga gaskiya quru-quru, kina nuna sam ba ki gan ta ba.” “Wayyo ni.... Sorry Aunty Nurry, ga hannuna kama ki nuna min gaskiyar.” Dariya suka sake yi gaba dayansu, sannan suka dauki mayafansu da suka yi anko don hada shi da kayan jikinsu. Ita kam ba ta daura dankwalin a kanta ba, gashin kanta na nan nade a qeyarta, sannan ta dauki jan ribom ta kama da shi, mayafin mai kalar ja ta rufa a kanta. Ita kanta ta san ta yi kyau sosai, dama ya lafiyar kura, balle ta yi hauka? Tana da kyau daidai gwargwado balle kuma ta 6ata tsawon minti arba’in a gaban madubi tana kwalliya. Hatta tafiyar da suke yi ta fita daban da ta sauran ‘yanmatan da suke gurin. Babu mai kushe kwalliyarsu, sai wanda zuciyarshi ke fama da cutar hassada. Duk inda suka gilma sai dai a bi su da ido ana fadin “Tubarkallah” Sai da suka bi mazaunin iyayensu da kakakninsu duk suka miqa musu gaisuwa suna saka musu albarka, sannan suka nemi gurin zama a can gaba-gaba inda za su iya ganin duk abinda yake faruwa. Mummynta ce ta sa ta dariya domin ko a yanzu da take zaune murmushi take yi, bayan ta tuna abinda ya faru tsakaninta da ita. Kanta ta dafa da hannunta na dama ta karanta Ayatul Kursiyyu da Qulhuwallahu, Falaqi da Nasi da Amanar Rasulu, ta yi wasu addu’o’i ta tofa wa Aisha, sannan ta ce “Allah ya tsare min ke diya ta, kin san bakin wasu yana da dafi. Wannan kyawun naki dole sai ina had'a miki da addu’o’i domin samun kariya” Zungurin Aisha da Zainab tayi da d'an yatsa a cinyarta ya katse mata tunanin da take yi. tayi “Wai don Allah me yake tsakaninki da Aunty Yasmin? Tun dazu ina lura da ita sai watso miki harara take yi.” Kafin ta amsa mata sai da ta kalli inda Amaryar take, karaf idanunta a cikin nata. Ba ta 6oye ba don ganin idanun jama’a a kanta, haka ta sake watso wa Aisha harara. Dariya Aisha ta yi sannan ta maida idanunta kan Zainab, ta ce “Ni kam ta ya zan yi in san abinda na yi mata Zee? Abinda na fahimta shi ne, kawai ta tsane ni matuqa, shi ya sa duk inda muka had'u sai ta yi qoqarin ci min fuska.” “Na ga kaman kishin kyau da Ubangiji ya yi miki take yi, ko kuma tana tsoron idan Yaya Abdul ya gan ki zai ce yana son ki.” “Ko ma dai mene ne a ranta a kaina can ta matse mata. Domin ba ta da yadda za ta yi da ni, na zama ciwon ido...” “Sai haquri...”Kaman Zee ta qarasa tana dariya qasa-qasa. Shigowar kiran Abdul cikin wayarta ya sa ta yi hanzarin dauko wayar ta latsa madannin amsa kiran, tun misalin sha biyun rana a lokacin suna shagon saloon ya kira yana sanar da ita jirgin qarfe biyun ranar zai hawo zuwa Yola. A dokance take da ta gan shi, shi ya sa ko dan jan-ajin da ta saba yi kafin ta dauki waya a wannan karon ba ta yi ba. “Matata kina ina yanzu?” Abinda ya fara tambayar ta kenan a dokance. Cikin dan murmushi ta ce "Ka iso ne?” "Eh, na iso yanzu. Wallahi qishin ruwan ganin ki nake yi, kina ina matata?” Farin ciki fal zuciyarta, don haka ta yi niyyar ja masa rai ta ce, “Ina gurin wanke kai.” “Wane irin gurin wanke kai kuma? Tun goma na safiyar yau fa kika fita zuwa gurin, ki yi min kwatancen gurin yanzu na taho in dauke ki.” “Maida wuqar! (ta faxi hakan cikin rarrashi). Ina wajen saka lallen amarya a gidan Ardo.” Ajiyar zuciya ta ji ya sauke mai nauyi, ya ce “Yauwa, ko ke fa babyna? Ki fito ga ni a qofar gidan.” “Ok... to bari in nemi izini gurin Mummyna" Tana gama fadin haka ta kalli Zainab da ta yi shiru tana sauraren ta, idanunta duk biyu suna kan ta. Dariya ta yi qasa-qasa, sannan ta sanya hannu ta janyo mayafinta da yake neman zamewa daga kanta ta ce, “Wannan kallon fa? Ni dai kar ki hadiye ni?” “Wai don Allah waye wannan dan nacin? Ni dai zan so in gan shi domin na fahimci kamar a cikin zuri’ar nan yake, amma duk hasashe na na kasa gano

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});