Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 3

Chapter 3

A Dalilin Da Namiji Book 3 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

bayan idona ya fada kan agogon dakin da ya nuna qarfe bakwai da minti ashirin na dare, har an kira sallar magariba an idar daf da kiran sallar isha’i. Awa daya da minti ishirin kenan muna magana a waya da Abdul. “Lala lala.... mijina kaga yanda lokaci yaja kuwa ba tare da mun ankara ba?” Sai a lokacin ya watsa idanunshi da suka canza launi daga farare zuwa ja kadan da kore kore, Cike tsananin shauqin soyayya da kwantar da murya mai cike da buqatar muradin abinda zuciyar shi take so a kusa da shi yace, “Na gani matata! ke ce kika sa na manta da kowa da komai...” “Ni dai babu ruwa na mijina, yanzu dai kaje kai wanka da alwala kayi sallah, bayan haka kuma sai ka je ka ci abinci. Ni ma yanzu zan je na yi sallah.” “Umarnin ki abin bi ne a gareni matata! Amma ina roqon addu’a a sujjadarki ta qarshe, kin san addu’ar mace ga miji kar6a66iya ce a gurin Allah.” “Ai dole in yi maka addu’a mijina, a kowace sallah tawa addu’arka ta musamman ce.” “Na gode matata! Amma kin san akan abinda nake so ki yin addu’a?” “A’a, sai ka faxa mijina...” Ta amsa da zaquwa don jin ko mene ne buqatar tashi. “Ki yi min addu’ar Allah ya bani sa’ar kama wadanda suka kashe Sadiya cikin satin nan don samun damar mallakar Aisha a matsayin matar aurena a sati na gaba da za mu shiga" Sai da dariya ta qwace mata ba tare da ta shirya wa hakan ba. Cikin dariyar ta ce “Komai tsawon lokaci za ka samu nasara in Allah ya yarda mijina.” “Dariya kike min ko?” Ya tambaye ta bayan ya yi qwafa. Dariyar ce ta ci gaba da jan ta don haka cikin dariyar ta sake fadin “A’a, ni ba dariya nake maka ba, a kan me zan yi maka dariya?” “Za ki yabawa aya zaqinta duk lokacin da ki ka zo hannu yarinya tun yanzu gara ki bi ni a hankali” “Oho dai, ai Mummy na ba za ta bar ka ka ci zalin ‘yarta ba.” Ta fada bayan ta tsaida dariyar, sannan ta murguda baki kamar yana kallon ta. “Lokacin da zan ci zalin naki ai Mummynki tana can ba ta da masaniya a kan komai.” “Bye-bye mijina, ana kiran sallar isha’i...” Tana gama fadin haka ta katse wayar don jin da tayi hirar tasu ta qi qarewa. Bandaki ta shiga ta dauro alwala don ba da farali. Bata qi gabatar da addu’ar da Abdul ya roqa a gare ta ba. Domin ita kanta za ta so a ce igiyar auratayya ta shiga tsakaninsu a nan kusa don samun damar mallakar junansu har abada a matsayin miji da mata. Suna zaune da Mummy da Daddy (mijin Mummy) a kan dining table suna cin abinci, duk hankalinsu yana kan ta. Suna tarairayar ta don ta saki jiki ta ci abinci sosai. Daddy da kanshi ya zuba mata abinci mai yawa a filet ya miqo mata tare da zuba mata juice a kofi yana fadin “Baby, ki yi sauri ki cinye in qara miki, so nake yi ki yi girma sosai kin ji yarinyata?” Dariya ta qyalqyale da ita sannan ta ja abincin kusa da ita ta fara tsakura tana kallon idanunshi ta ce “Daddy idan na cinye wannan abincin ai sai a zo a gan ni. Zan dai dage in ci ko da daya bisa hudu na abincin da ka zuba min. A hakan ma wai don Mummyna ta iya sarrafa girki yayi dadi kamar zai tsinke kunne ne" Ta qarasa maganar tana kallon idanun Mummynta da tunda suka fara caftar tana kallon ta da murmushi a fuskarta. “Daddyn Baby ka ji ‘yarka tana tsokana ta ko?” Ta fada bayan ta mai da idanunta a kanshi, a muryarta dauke da salon shagwava. “Ai gaskiya Baby ta fada Mummyn Baby, ke din ba dama ce in dai gurin sarrafa kowane kalar abinci ya ba da ma’ana ne.” YA fada yana dariya. “Ka dai goyi bayan diyarka kenan ko?” ta sake jefa masa tambayar tana dariya. “Eh mana, ai gaskiya diyar tawa ta fada.” “Kin ji dai Mummy, Daddy ma ya san kin cancani a ba ki award ta kowane 6angare, musamman ma a gurin hada abinci. Hira suke gudanarwa cikin nishadi da fahimtar juna har suka gama cin abincin, ita ce ta kwashe kulolin abincin da filet da komai da suka yi amfani da su zuwa kicin. Kan kujerun falo suka koma da zama suna hira jefi-jefi tare da kallon T.V. “Gobe idan Allah ya kai mu za mu shiga kasuwa ni da Baby don za6a mata kayayyaki irin namu na gida (atamfa, leshi, shadda, materials) daga can sai mu wuce gurin tela mu ba da dinki. Idan lokaci bai qure ba za mu biya gaida Ardo.” Mummy ce take yi wa Daddy wannan bayanin. “Ni ba a buqatar rakiyata kenan Maman Baby?” Ya tambaya yana kallon Mummy da kallo irin na soyayya. “Ni na isa in hana ka rakiya Baban Baby? Kai diyarka ai ba zan shiga tsakaninku ba. Allah ya ba ka haquri...” Ita dai dariya kawai ta yi don ganin yadda iyayen nata suke neman soyewa a gaban diyar tasu ba tare da jin kunya ba. Hamma ce ta zo bakinta ba tare da ta shirya wa zuwanta ba, don haka ta yi haramar miqewa zuwa dakinta, har qasa ta durqusa ta yi wa su Daddy sai da safe, sannan ta sabe zuwa dakinta suna bin ta da kallo da addu’a cikin kulawa da qauna. Farin ciki fal zuciyarta don jin qaunarsu take kamar iyayenta. Shi yasa a kowace sallah da ta yi ba ta gajiya gurin roqon Allah ya ba Mommy haihuwa. Shigowar kiran Abdul cikin wayarta yasa ta share duk wani tunani daga zuciyarta sai nasa da soyayyarsa, da irin tanadin da ta yi masa idan Allah ya mallaka musu juna a matsayin ma’aurata. *** Yana riqe da wayar a daidai saitin kunnenshi duk da dai ya fahimci ta yi barci, addu’ar barci ya karanta tare da tofawa a jikin wayar yana fatan Allah ya amshi addu’arshi zuwa gareta. A hankali yake jiyo saukar numfashinta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. “Ina ma... ina ma.. a ce a yanzu haka tana kwance ne a tsakiyar faffadan qirjinshi tana barci...” tunanin da ya mamayi zuciyar shi kenan sannan ya dora addu’ar Allah ya mallaka masa Aisha a matsayin matar aure nan da dan wani qanqanin lokaci. Tuno sharadin da zai tabbatar da aurenshi da ita ya sa ya miqe ya nufi bandaki ya dauro kyakkyawar alwala yayi nafila raka’a biyu. A sujjadarshi ta qarshe yake addu’ar Allah ya sauqaqa mishi binciken da yasa a gaba, Allah ya ba shi nasarar gano inda wadannan masu laifi suke don samun cikar burin ranshi na auren Aisha. Sarqa irin wadda ‘yan iskan gayu suke sakawa a wuya wanda likita ya ba shi tare da file din binciken da suka gudanar na dalilin mutuwar Sadiya ya qura wa ido kamar mai karantar wani abu daga jikin sarqar, ba tare da sanin kowa ba ya samu wasu matasa ya sa su yi masa C.I.D na wannan kango inda aka tsinci gawar Sadiya. Ya umarce su da yin gadin

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});