Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 19

Chapter 19

A Dalilin Da Namiji Book 3 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wai duk domin ita yake yin wannan zirga-zirgar. Idan suna fadin haka sai dai ta yi dariya kawai, domin ita dai ta san ta kama dahir din ta a hannu, don haka jin su kawai ta ke. Suna cikin mota Yasmin ta kira Mu’azzam a waya tana tambayr shi yana ina? Kai tsaye ya sanar da ita yana hanyar kai su Zainab saloon. Aisha ba ta san me Yasmin ta sake cewa da shi ba, amma ta ji yana fadin “Ok, ina zuwa yanzu.” Lura da ta yi yana neman juya akalar motar su koma baya yasa ta watsa masa idanu tare da fadin “Lafiya dai ko? Na ga kana neman sauya akalar motar.” “Yi haquri qaramar qanwata, saqo zan kar6a a nan baya, guri matar yaya Abdul.” Fahimtar da ta yi Yasmin yake nufi ya sa ta kau da kai tana fadin “To, ai sai mu sauka mu nemi wata motar, tunda kana da uzuri. Ka ga bai kamata mu takura maka ba.” Kwantar da kanshi ya yi sannan ya marairaice ya ce “Haba dai, ga ni da motar za ki nemi hawa ta haya, ai ba girmanki ba ne. Wallahi ba dadewa za mu yi gurin amsar saqon ba, kuma abinda ya sa na ce zan je in amsa yanzu don dai na ga ba mu yi nisa da inda ta ke ba ne.” Kau da kai gefe ta yi ta qi tanka masa. “Tunda ba ki amince ba mu je saloon din daga baya sai in dawo in amshi saqon.” “Mu je ka kar6i saqon yanzu, amma idan ka dad'e za ka neme mu a motarka ka rasa.” Aisha ta amsa kai tsaye bayan ta faminci yana neman ci gaba da tafiya zuwa inda suka nufa. “Ai ba ma zan dad'e ba, na gode qaramar qanwata...” Ya fad'a yana murmushin tsokana, tare da kallon fuskarta don ganin ko za ta yi magana. Sha re Shi tayi. Suna isa qofar gidan da ta umarce shi ya je ya karbi saqon ya sanar da ita a waya ya iso, yana qofar gida. Aisha na zaune a kujerar mai zaman banza gefenshi don haka tana ganin duk wani shiga da fita da ake yi ta jikin get din gidan. Su bakwai suka fito daga cikin gidan suka nufo motar Mu’azzam suna hira. Da dariya a tsakaninsu. Sai da suka qaraso gurin motar Aisha ta fahimci bayan Yasmin, akwai Aunty Hafsa, da Aunty Habiba sai kuma wannan qawar tata da suka ta6a arangama a gidan Abdul tun tana zaman Kaduna. Sauran ‘yanmatan uku baqin fuska ne a gare ta. Amma a faminci qawayenta ne, qila daga Kaduna suka zo tare da ita. Tana tsaye ta vangaren direba, da alama ba ta fahimci har da Aisha a cikin motar ba, domin hankalinta gaba daya yana gidan baya na motar tana amsa gaisuwar da su Zainab suke miqa mata. “Ina saqon da za ki ba ni? Domin dai sauri muke yi.” In ji Mu’azzam da ya fahimci Aisha ta fara qaguwa da zaman jiran da take yi, sai a wannan lokacin ta duqo da kanta daidai sashin direba karaf idanunta a cikin na Aisha. Mamaki ne ya kama ta, amma sam ba ta nuna 6acin ranta ba ta ce, “Keh ‘yar gidan Aunty ba ki iya gai da manya ba ne?” Da murmushi a fuskar Aisha take mamakin wannan wulaqancin da take neman nuna mata. Ko ta manta ita din ba kanwar lasa ba ce? daman cike take da ita, dan haka ta tuna mata da wace ce Aisha ta hanyar cewa “Ayya.... ba a koya min gaisuwa ba amaryar Yaya Abdul, kamar yadda na ga ba a koya miki sallama ba.” Shiru ta yi tsawon minti daya tana maida numfashi, da alamun ranta ya vaci, amma ba ta sake kallon inda Aisha take ba, ta maida dubanta ga Mu’azzam tare da fadin, “Mu’azzam don Allah friends dina za ka kai kasuwa, ka san baqi ne ba su san kan garin ba.” Shiru ya yi na dan lokaci idanunshi kan sitiyarin motar ya ce, “Ok, to bari in ajiye su Zainab a gurin wanke kai in dawo” “Haba dai Mu’azzam! Su Zainab ai ba baqi ba ne, su yi haquri su bi wata motar zuwa inda za su je, ka ga wadannan baqi ne, kuma baqin ka Annabinka.” Shiru ya yi mata bai tanka ba sai ta maida kanta ga su Zainab, "Zee don Allah ku yi haquri ku fito zan ba ku isassun kudi ku je duk inda za ku je, kun ga su baqinmu ne, sun cancanci girmamawa daga garemu.” Aisha tana kallon fuskarsu suna qunquni ciki-ciki, domin ba a jin abinda suke cewa, lura da ta yi sun bude motar suna niyyar fita ya sa ita kuma ta sake gyara zama a kan kujera ba ta niyyar bude qofar balle har ta fita daga motar. Yasmin ce da ta gaji da jiran ta fito daga motar ta leqo da kanta ta varin direba ta ce, “Saura ke ko? Ko ba ki ji abinda nace ba ne?” Aisha ba ta kalle ta ba ta maida mata da amsar cewa “Na ji! Amma sai dai ya fara sauke ni a inda ya dauko ni sannan ya kai su inda za su je.” Izuwa yanzu ta kai matuqa gurin hassala har ta kasa boye bacin ranta cikin masifa ta ce “Da yake motar ta gidanku ce?, kin ga idan ke ‘yar halas ce ai sai ki fito ki kama gabanki.” Cikin fitsara Aisha ta amsa mata da cewar, “Ai wallahi ba inda zan fita sai dai idan shi mai motar ne ya buqaci in fice mishi daga mota.” Mu’azzam ne ya kallo Aisha, fuskarshi dauke da damuwa ya ce “Yi haquri don Allah Humaira..." Sannan ya maida dubanshi gare ta ya ce “Hadisi ingantacce Manzon Allah (SAW) ya ce “Imanin dayanku ba ya ta6a cika har sai ka so wa dan’uwanka abinda kake so wa kanka. Don haka ki bari in fara sauke su a inda suka nufa, sannan naki umarnin ya biyo baya...” “Wulaqanta ni za ka yi a kan wannan ‘yar iskar?” Ta tambaye shi tana tada jijiyar wuya, tare da nuna Aysha da yatsarta manuniya. “Babu batun wulaqanci a nan Yasmin, domin tabbas sun fi ki gaskiya.” Aunty Hafsat ce ta fadi haka, bayan ta lura cacar bakin yana neman yin tsawo kuma a qofar gida. “Zainab ku shiga ya kai ku gurin saloon din, kai kuma Mu’azzam ka dawo da sauri ka kai qawayenta kasuwa idan ka sauke su.” Aunty Habiba ce ta fad'i haka don kawo qarshen fadan. Rasa abin cewa ta yi, domin jin sun ba ta rashin gaskiya, kuma sun kunyata ta a gaban manyan qawayenta da suke tsaye a gefe sun qi tankawa balle har su shigar mata fadan. Ganin da ta yi yana neman tada motar bayan su Zainab sun koma mazauninsu ta kalle shi ta ce “Na gode qwarai, mu zuba ni da kai Mu’azzam, amma kar ka manta ba kai kadai ne mai mota a familynmu ba, kuma ka san in ban da zuwanmu nan ba ka isa ka yi min gori a kan mota ba...” Bai jira ta gama magana ba ya tada motarshi ya ja suka wuce ya bar ta

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});