Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 6

Chapter 6

A Dalilin Da Namiji Book 3 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

darajar namiji a kan mace, da tarihin yadda Ubangiji ya halicci Nana Hauwa’u da qashin haqarqarin Annabi Adamu, da tarihin Manzanni da Sahabbai na yadda suke kula da nauyin da Allah ya dora musu na matansu. Da yadda su matan suke butulcewa mazajen, da tarihin yadda matan Annabi Muhammad (S.A.W) suka taba hada masa zafin da saida ya yi wata daya a cikin masallaci, sannan ya kawo qwararan hujjoji da suke nuni da babu yadda za a yi mace ta iya rayuwa ba tare da DA NAMIJI ba, domin halittar a hade ta ke kamar mayen qarfe ne da qarfe. Daya ba zai iya rayuwa ba sai da daya. Sai da ya gama kashe musu jiki gaba daya, masu raunin zuciya daga cikinsu irin su Fatima har sun fara hawaye, yayin da dukkansu suka yi tagumi hannu bibbiyyu cikin tashin hankali. Mummy ce ta ci gaba da janyo hankulansu ta hanyar nuna duk abinda ya faru da su a rayuwa muqaddari ne daga Allah. Tun kafin a haife su an riga an rubuta abin da zai faru da su. Ta nuna musu su daina tunanin don A DALILIN DA NAMIJI muka samu gi6i a rayuwarmu ba hakan yana nufin duk maza halayensu daya ba ne. Ana samun baragurbi daga 6angaren mazan da matan. Sannan ta nuna musu Abdul a matsayin wanda Aisha za ta aura mai yi mata soyayyar da zai iya ba da rayuwarshi a kanta. Aisha ce ta mayar musu da duk abinda ya faru da su tun daga lokacin da suka bar gida da niyyar zuwa gidan abinci ita da Sadiya. Hatta irin rasuwar da Sadiya tayi bata 6oye musu ba, sannan tai musu nuni da Abdul a matsayin wanda ya tsaya kai da fata gurin binciken wadanda suke da alhakin mutuwar Sadiya, don gurfanar da su gaban kuliya su kar6i hukuncin da ya dace da su. Kuka suke gaba dayansu, a lokacin ne suka sanar da ita ba su da masaniya a kan rasuwar Sadiya. Danye rasuwar ta dawo ma Aisha don ganin yadda suke kokawa harda Baba Jummala, ta kasa nuna dauriya hawaye kawai take tana fadin “Inna lillahi wa inna ilaihiraji’un!” Nasihar Ardo da ta Mummy da kuma jin rasuwar Sadiya sune suka taru suka saukarwa da ‘yan’uwan Aisha sanyin jiki, suka sauka dokin qiyayyar DA NAMIJI. Ko da Ardo ya nemi maida su gidajen mahaifansu babu wacce tayi musu, a take suka fara tuba ga Allah tare da daura niyyar yin sabuwar rayuwa a gaban iyayensu da fatan samun mazaje nagari, kamar yadda Aisha ta samu. Fatima ce ta fara neman a maida ta dangin mahaifiyarta ne a can qasar Nijar, amma adireshin inda suke zaune ba zai samu ba sai ta hannun qanin mahaifinta. Ardo ne ya amsa mata da cewa hakan ba zai zama matsala ba za a mayar da ita can din in Allah ya yarda. Ba su samu wata matsalaba daga mahaifa da dangin kowacce daga cikinsu, duk gidan da suka je a mutunce da karamci ake karbarsu. Iyayensu da danginsu sun yi nadama matuqa, kuma sun tabbatar masu da babu inda ba su shiga don neman ‘ya’yan nasu, Ardo shi yake qara janyo hankulansu a kan amanar 'ya'ya da Ubangiji ya danqa a hannun iyayensu. Da kuka suka rabuwa sannan Aisha ta Damqa kyautar chek na Naira miliyan biyar ga kowacce daga cikinsu. Baba jummala ce ta qara mata zuwa Miliyan goma, kuma ita ta yi alqawarin riqon Siyama da Suhaila da ta dauko su daga gidan Marayu kamar ‘ya’yanta na cikinta. A gidan da ta mallaka mata na mahaifinta suke zaune. Ardo yayi alqawarin duk wani abu da zai taso dangane da su Siyama idan ana neman danginsu a neme shi, zai tsaya musu kai da fata kamar yadda zai tsayawa jikokinshi. Alh. Musa qanin mahaifin Fatima yayi matuqar nadama sosai, domin kuka ya ringa yi da idanunshi, sannan ya duqa har qasa yana neman afuwarta. Koda suka sanar da shi abinda ya kawo su na neman adireshin dangin mahaifin Fatima don mayar da ita can kuka ya sake sakawa yana roqon Ardo da Allah da Annabi a bar ta a hannun shi zuwa sati mai zuwa da kanshi zai kaita gurin dangin mahaifiyarta ta kwana biyu. Amma ba zai iya barin ta a can ba don yana son ya nuna mata gata a matsayinta na diyar dan uwanshi, wanda a da can bai nuna mata ba. A kallo daya za ka gane tsantsar nadamarshi da gaskiyar abinda yake fadi har zuciyarshi ne, don haka suka amince da barinta a nan bayan ita kanta Fatiman ta amince da hakan. Ba su samu kammalawa da komai ba sai ranar Asabar da yamma, jirgin qarfe takwas na daren ranar za su bi zuwa Yola, don haka suka ci gaba da shirye-shiryen komawa gida. Suna zaune a falon Abdul, Aisha da Mummynta, Ardo yana cikin daya daga dakunan Abdul yana wanka. Hira suke da Mummy akan yadda maida ‘yan’uwanta gidajensu ya kasance tsakanin jiya da yau, shigowar Abdul cikin falo shi ya katse mata maganar da take yi. Kallon-kallo suka yi a tsakaninsu sa’annan ya maida idanunshi a kan Mummy ya ce “Mummy ko za ki ba ni aron diyarki ta yi min rakiya zuwa cikin gari?” Ya tambaya yana Sosa keya, yana kara satar kallon Ayshan. “Anya zan iya ba ka aron diyata kuwa Abdul? Babyna ta gaji sosai tana buqatar hutu ka ga bai kamata ka tara mata gajiya ba.” Ta fada kai tsaye tana kallon cikin idanunshi. “Haba Mummynmu! ai don Allah na ce.” Ya sake fadi cikin salon roqo da kwantar da kai.” “Tun da ka matsa bari in tambaye ta idan za ta iya zuwa.” Ta fada, sannan ta dawo da idanunta kan Aisha ta ce “Baby wai za ki iya yi mi shi rakiya?” Maqe kafada ta yi alamun a’a. Tana tura baki ta ce “Ni dai a’a Mummy, shi kawai so yake ya qara wahalar da ni.” “Toh, ka ji Abdul. Baby ta gaji da yawa, ka yi haquri kawai.” Tagumi ya yi ya rasa hanyar da zai bullo musu. Yadda yai tagumin yai qasa da idanu ya so ya dan ba ta tausayi, shigowar Ardo dakin da sallama da maganar da yayi ya sa Abdul sakin murmushin da bai yi niyya ba. “Mutum da matarshi an tava hana shi iko da ita Aishatu?” (Yana nufin Momy, idan ba ku manta ba sunansu daya) diyarki fa an riga an ba Abdul aurenta, kuma ina daya daga cikin shaidun da suka shaida, sadaki ya rage ya biya, jama’a da dama su shaida ya dauke ta daga gabanki” Sunkuyar da kai qasa Aisha ta yi cikin matsanancin jin kunya. Mummy kuwa murmushi ta yi ta ce, “An gama Ardo tun da ka sa baki, kai kuma Abdul ka yi tuqi a hankali kuma ka dawo min da diyata a kan lokaci.” Mayafi kawai ta dauka ta yafa a jikinta, don dama ta yi wanka ta yi kwalliya cikin riga da siket na tamfar da ya yi matuqar dacewa da fatar jikinta. “Matata kin ga yadda kika yi matuqar kyau cikin wadannan kayan kuwa? Ban tava ganinki cikin kayan dinki irin namu ba, sai a jiya da yau. Shigarki daga doguwar riga sai kayan turawa.” “Doguwar

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});