Chapter 5
Chapter 5
da za kai abinda ka ga dama tunda kai ba yaro ba ne. Amma don Allah ka rage irin takurar da kake yi wa qanwarka. Ka ga ku biyu kawai Allah ya ba mu a matsayin ‘ya’ya. Babban burinmu shi ne ku hada kanku kai da qanwarka, ka ga ita yarinya ce qarama, dole kai ne za ka ringa nuna mata wasu abubuwan cikin hikima idan ta kuskure. ka yi haquri ka ji yarona?” Sai da ya gama shan qamshi kamar ba zai tanka ma uban ba sai can ya ce, “Shi kenan ya wuce Daddy, amma gaskiya bana son yadda Mummy take bada ni a gaban wannan yarinyar.” “Daga yau ba za ta qara ba da kai a gaban qanwarka ba in Allah ya yarda. Ka ringa haquri ka ji babana?” “Ya wuce.” Ya sake amsawa a taqaice yana tada jijiyoyin wuya. “Za ka hau dining ne ko in hada maka break din ka zauna a qasa?” Mummy ta tambaye shi da murmushi a fuskarta, don qara wanke laifinta tunda Daddy ya ari bakinta ya ci mata albasa gurin rarrashin shalelen nasu. “Ba yanzu zan karya ba.” Ya amsa ba tare da ya kalle ta ba don har a lokacin haushinta yake ji dangane da fadan da ta yi masa. Daddy ne ya daga ha6an Abban yana kallon ciwon da ya ji gurin damben da suka yi da abokanshi kamar yadda ya sanar da su ya ceha6an “Anya kuwa Babana ka je asibiti sun yi maka dressing gurin ciwukan nan? Na ga yau kwanaki biyar kenan amma ko alamun warkewa basa yi?” “Na je asibiti Daddy, kuma ina shan magunguna. Kawai lokacin warkewar ciwon ne bai yi ba.” “Ai don dai ka hana a dauki mataki a kan yaron ne, amma wannan ciwo da ya ji maka ai ya yi yawa, dubi yadda yake kwashe maka jiki a gurare daban-daban kamar wani kare saboda tsabar zalunci?” “Ku share kawai Mummy, shi kanshi yaron yana kwance yanzu haka a asibiti, domin cuwukan da na ji mishi sun fi wanda ya ji min.” “Shi kenan tunda haka kake so Babana...” Mummy ta fadi hakan bayan ta dawo kan kujerun falon ta zauna kusa da inda Abba da Daddy suke zaune, suna jajanta ciwukan jikin Abban, musamman na wuyanshi wanda yakushi mai girma suka fito 6aro-6aro, kuma sam ba su da alamun warkewa kamar a jiya aka ji su. *** Yadda nake murza sitiyarin motar cikin farin ciki da karsashi shi zai qara tabbatar da tsantsar farin cikin da nake ciki. Mummy tana zaune a gefe na da casbaha a hannunta tana ja lokaci zuwa lokaci tana dago kanta ta kalle ni da murmushi a fuskarta. Ina kallon motar Abdul’Ahad dauke da Ardo suna biye da tamu motar. “Babyna da alamun tunda muka shigo garin Kaduna kike cikin matsanancin farin ciki, amma farin cikinki na yanzu ya fi na kowane lokaci yawa, tunda har ya gaza 6oyuwa a fuskarki.” Dariya ta yi mai qara nuna tsantsar farin cikin da take ciki daga bisani ta amsa mata da cewa “Hmmn! Mummyna kin san ai dole in yi farin ciki. Yau fa sati daya kenan rabona da ‘yan’uwana, kuma a yau din ne za mu sake haduwa da su. Babban abinda ke qara fadada farin cikina shi ne, a yau din ne kowacce daga cikin ‘yan’uwana za a maida ita gidan mahaifinta da taimakon Ardo. Baqin cikina daya shi ne, yadda na bar gida ina tare da Sadiya, amma zan koma gida ba tare da ita ba...” Damuwa da jimami ne ya mamaye farin cikin fuskarta da zuciyarta, hawaye mai zafi ke qoqarin kawo farmaki kan idanunta amma ta matse su ba ta bari sun zubo ba don gudun tada hankalin Mummy. “Ki yi haquri Babyna. Mai rabawa ta riga ta raba tsakaninmu da Sadiya, inda ta tafi kowa zai je can. kin ga kenan ita da ta tafi ba ta yi sauri ba, mu da muke nan ba mu dad'e ba. Addu’a shi ne babban abinda ya yi saura a tsakaninmu da ita” Cikin taushin murya da dad'ad'an lafuzza Mummy ta ci gaba da rarrashin ta har ta haqura ta saki ranta, ta dawo da walwalarta. Da haka har suka isa qofar gidan. A bude suka tarar da gidan, kamar suna da masaniyar a ranar za ta dawo. Ita ce a gaba yayin da Mummy take biye da ita kafada da kafada. Ardo Abdul suna baya suna biye da su. A zukatansu suke al'ajabin wannan gida da girmansa da kayatuwansa. Gaba dayansu suna zaune a tsakiyar falon, sanye cikin manyan hijabai da casbaha a hannayensu. Motsin shigowar da suka ji yasa duk suka miqe tsaye, suka zubawa matakalar da za ta sada mutum da tsakiyar falon idanu. Ita ce ta fara sauka cikin falon, sannan Mummy sai Ardo da Abdul suka sauka daga karshe. “Alhamdu lillahi rabbil Alamin. Alhamdulillahi ala ni'imatihi tatimussalihat” Abinda suka hada baki gurin fada gaba dayansu kenan, sannan 'yan matan suka nufo gurin ta da sassarfa suka rungume juna suna murna. Baba Jummala kai tsaye gurin Mummy ta nufa ta kama hannun ta ta zaunar da ita a kan kujera tana mata barka da zuwa. Har qasa ta durqusa ta gai da Ardo sannan ta nufi kicin ta fara jero musu ruwa da juice kala-kala. “Siyama a taya Baba Jummala kawo wa baqi abin sha mana.” Aisha ta fada tana kallon yadda Baban ta ke shiga da fita tsakanin kicin da falo. karaf idanunta cikin na Abdul, a lokacin sauran ‘yan gidan sun koma kusa da Mummy sun duqa har qasa suna gai da ta. Da fara’a take amsawa tana tambayar sunayensu daya bayan daya suke amsa mata. Lumshe ido yayi ya bude sannan ya yi qasa da su yana aiko mata saqon soyayya. Duk yadda ta so ta share shi ta kasa, sai da ta maida masa martanin murmushin. Le66anshi ya motsa alamun furta kalmar “I love u...” Sannan ya dafa saitin zuciyarsa yana qara lumshe idanu. Da ido ta yi mishi inkiya da Ardo dake zaune a gefenshi, sannan tayi saurin dauke kai daga gare shi, don ta lura idan tana biye masa sai ya sa ta aikata abin kunya gaban su Fatima da Baba Jummala. Har qasa ta duqa ta gaida Baba Jummala kamar yadda ta saba, sannan ta sake neman guri ta zauna kusa da Mummynta, su Rahma suka fara jerangiyar gaida Aisha, sna zama qasa kusa da qafafunta. Abinda ta lura da shi shine, sam su Safiyya basu gaisa da Abdul ba, sai Ardo kawai suka gaisar da Mummy da take ‘yar uwarsu mace. Shi kanshi Ardo ta lura abinda ya sa suke gaisar da shi don dai kwarjini da Allah ya ba shi ne. Duk zafin kan mutum idan ya ji muryar Ardo ko kuma ya yi arba da shi dole ka qasqantar da kanka. Sallama irin ta addinin Musulunci Ardo ya fara bude filin falon da shi, suka amsa gaba daya sannan ya fara jero addu’a cikin harshen laraci suna sauraren shi. Sai da duk suka gama nutsuwa tare da qara mai da hankalinsu dari bisa dari kanshi, sannan ya fara janyo ayoyi da hadisan da suke nuni da yadda Allah ya dora namiji a kan mace, da yadda Allah ya fifita
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31