Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 14

Chapter 14

A Dalilin Da Namiji Book 3 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Kayan jikin Abban ya cire T.shirt da wandon jeans, ya bar shi da singileti fara kar da gajeren wando. Bai gaji ba ya sake tarairayar Abban har zuwa cikin dakin barcinsa ya kwantar da shi a gado, ya janyo babban bargo ya rufa mishi. Sannan ya kashe wuta mai haske ya kunna mara haske sosai. Falon ya dawo ya tattare hannun rigarshi, abinda ya fara yi shi ne lalube aljihun wandon da ya cire a jikin Abban ya kwashe duk kudaden ciki ya zuba a nashi aljihun, a gefe ya ajiye kayan, sannan ya nufi bandaki ya dauko tsintsiya da ruwa a bokiti ya kwashe aman tas ya goge gurin. Turaren ya dauko ya feshe falon gaba daya don dakushe qarfin warin giyar da ya mamaye falon. Yadda maigadin yake kwashe aman hankalinshi kwance kuma ba tare da qyanqyamin ba shi ya tabbatar wa Abdul ba yau ne karo na farko da maigadin ya fara irin wannan aikin ba. Agogon wayarsa ya kalla, qarfe daya da minti goma sha biyu na dare. Fitowa ya yi daga inda yake tsaye, ya nufi qofar falon Abba kai tsaye, A daidai lokacin kuma maigadin ya gama komai har ya kwaso kayan jikin Abba da ya cire ya nufo waje don ficewa daga falon. Cak ya ja ya tsaya jikinshi na karkarwa lokacin da ya hada idanu da Abdul-Ahad. Murmushi Abdul ya jefa mishi, sannan ya yi saurin cewa, “Inusa har yanzu ba ka kwanta ba?” Sosa qeya ya yi cikin alamun rashin gaskiya qarara, murya na rawa ya ce “Ina barci ga wanda yake aikin gadin wasu ranka ya dad'e? Alhaji Abba ne ya dawo gida baya jin dad'i don haka na taimaka masa har ya samu barci. A yanzu ne nake shirin komawa bakin get don ci gaba da aikina.” Dariya Abdul yayi kawai, don qara kwantar wa da maigadin hankali, ya ce, “Ni ma tun dazu da muka yi sallama da Yasmin ta shiga cikin gida ban samu tafiya ba, ka san al’amarin qarfen nasara ba tabbas! Ganin dawowar Abba ya sa na yanke shawarar kwana a nan in ya so gobe sai in wuce da safe. Ka je ka ci gaba da aikinka ni zan kwana tare da Abban. Allah dai ya biya ka Inusa irin wannan dawainiya da kake da mu.” Farin ciki ne ya mamaye tsoron da ya cika zuciyar Inusa maigadi. Kai tsaye ya amsa addu’ar Abdul cikin farin ciki da cewa “Amin ranka ya dad'e, ku ma Allah ya saka muku da alkhairi, domin ba don ku ba da yanzu ina garari a gari cikin marasa aikin yi. Bari in koma bakin aikina, mu kwana lafiya ranka ya dad'e” Yana gama fadin haka ya kama hanyar ficewa daga falon cikin sauri. Idanu Abdul ya raka shi da shi, a zuciyarshi yake dariyar yadda maigadin ya shiga rudani daga ganin shi. Kai tsaye bedroom din Abba ya wuce don ganin halin da yake ciki. Yana kwance dai-dai a kan makeken gadon da ya mamaye fiye da rabin dakin. Barci yake cikin kwanciyar hankali, harta bargon da maigadin ya lulluba mishi ya yaye shi can gefe daya. Da wayar hannunshi yake haska cuwukan da ya gani kwance a jikin Abba a gurare daban-daban. Mamaki ne ya kama shi, da ganin ciwukan dai ba a daren wannan ranar aka ji su ba. Amma kuma ba a dade da jin ciwukan ba domin danye ne sharaf, wani irin ruwa-ruwa suke fitarwa musamman na wuyanshi wanda nuna alamun yakushi ne sanadinsu, domin sun yi layi-layi alamun yatsu. Wutar lantarki mai haske ya kunna domin ya qara karantar ciwukan da kyau. Duk da cewa an kunna wutar bai sa Abba ya motsa ba, domin barcin da yake yi da taimakon ababen gusar da hankalin da ya sha ne. Kanshi ne ya kara daurewa, domin sai a yanzu ya gama fahimtar ciwukan duk kusan sanadin samuwarsu daya ne. kallo daya za a yi ma duk wani ciwo da yake jikin Abba a fahimci yakushi ne. “Da waye Abba ya yi dambe aka yakushe mishi sassan jiki haka?” Abdul ya tambayi kanshi da kanshi duk da yana da tabbacin amsar bazaiyi wuyar samu a gareshi ba. Tsawon mintuna goma sha biyar yana tsaye a kan Abba yana qare masa kallo, daga bisani kuma sayya kashe wutar dakin ya barshi a duhu a yanda ya tarar da shi da farko, kai tsaye ya fice daga falon ya nufi gurin maigadi, a zuciyarshi yake addu’ar Allah ya sa ya samu qarin bayani daga gurinshi. Yana kishingide a kan benci a dakin da yake kwana amma ba barci yake yi ba. Motsin da ya jiyo ana taba qofar dakinshi ya sa ya fito da sauri da adda a hannunshi, yana muzurai. Ganin Abdul a tsaye kyam ya sa jikinshi ya yi sanyi, sai daga bisani ya yi qarfin halin fadin “Ranka ya dad'e lafiya kuwa? Ko wani abu kake nema?” Bai ce da shi komai ba illa ra6ewa da ya yi gefe maigadin ya shiga dakin ya zauna a kan bencin. Biyo bayanshi ya yi sannan ya zauna a can nesa da shi, yana jiran abinda Abdul zai ce da shi. “Malam ina fatan ban takura maka ba? Sam ba na jin barci shi ya sa na yanke shawarar zuwa gurinka don in taya ka hira.” “Habawa ko da na ji! Ni fa na yi mamakin ganin ka a wannan lokacin bayan har na fitar da tsammanin ka yi nisa cikin barci.” Maigadin ya fadi haka yana qara washe haqora tare da sakin jikinshi gaba daya. “Ka san gobe ranar aiki ne, ko a gida ban cika sakin jiki in yi barci mai nisa a daren Lahadi ba, amma fa ina kai wa sha biyu na safe ban tashi ba ranar Asabar da Lahadi, so barcin da na yi a safiyar Lahadin yau shi ya sa a daren barcin ya qi kawo min farmaki.” “Allah Sarki Ranka ya dad'e, ai kuna matuqar qoqari. Irin wannan aikin naku na ‘yansanda ba kowa ne zai iya shi ba, shi ya sa ladanku sai gurin Ubangiji.” Sai da Abdul ya yi dariya sannan ya ce, “Aikin namu ai duk kusan tafe yake da naku Malam Inusa. Bambancinmu da ku kadan ne, ka ga mu muna gadin rayuwar al’umma ne, yayin da ku kuma kuke gadin wasu daga cikin al’ummar. Ka duba, misali yadda duk mutane gidan nan a yanzu haka suna kwance suna barci, amma kai a lokacin barci kai kuma idanunka biyu kana gadinsu. Ka ga dole a jinjina muku, Ladanku ku ma sai gurin Allah. Don haka nake ganin ko miliyan nawa aka biya ku da shi ba a biya ku abinda ya dace da ku ba.” Dariya maigadin ya qyalqyale da ita cikin matuqar jin dadin an yabi qoqarinshi, kuma ya san kadan daga cikin aikin Abdul ne ya sa a yi masa qarin albashi. Don haka ya sake kwantar da kai yana nunar wa Abdul irin qoqarin da yake yi a kan aikinshi na gida. “Maganarka gaskiya ne Ranka ya dade, yanzu ka duba dai yadda Alhaji Abba ya dawo gidan nan a galabaice, idan ba da irinmu haziqan masu gadin ba ai sai ya shiga cikin wani hali ba tare da sanin iyalan gidan nan

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});