Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 16

Chapter 16

A Dalilin Da Namiji Book 3 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Daddy sun sani kuwa?” “Dambe suka yi da wani abokinshi, su Daddy sun sani, domin jiya da safe ma Daddy da kanshi ya sake kai shi asibiti aka canza masa wasu magunguna, domin wadanda yake sha sam ba su karbe shi ba.” “Dambe?” Ya tambaye ta yana qara jinjina al’amarin a can qasan zuciyarshi. “Qwarai kuwa, domin yaron da suka yi fadan da shi har yanzu yana kwance a asibiti.” Ta sake tabbatar masa da hakan don qara gamsar da shi. “Amma babu wani matakin da daddy ya dauka a kai?” “A'a! Ya so ya dauki mataki a kan shi wancan yaron da iyayen yaron, sai Yaya Abban ya hana su, a lokacin ne ma ya sanar musu da cewa shi wancan abokin fadan nashi yana can kwance a asibiti cikin mawuyacin hali.” Cikin kokwanto a kan maganar tata ya sake tambayar ta da cewa, “Su Daddy sun je asibitin sun ga shi wancan abokin fadan nasa ne?” "A’a, shi ne dai ya fada musu hakan.” “Ok.. toh na gode, bari in bar ki ki huta sai mun yi waya zuwa an jima...” Cikin salon shagwaba da marairaita ta ce “Yaya gaskiya ban gaji da jin muryarka ba...” “Yi haquri yanzu ina tsaka da aiki, za mu yi magana an jima.” Bai saurari abinda za ta sake fadi ba ya katse wayar yana jinjina al’amarin ciwon Abba a zuciyarshi. “Yaya ka yi alqawari?” Ta tambaye shi ba ta da masaniyar ya katse kiran. Fahimtar da ta yi ita kadai take magana ya sa ta yi sanyi riqe da waya a kunnenta, amma ganin Hidaya na kallon ta ya sa ta wayance ta hanyar cewa, “Ok, bye bye. I love u.” Tare da sumbatar wayar. Duk yadda Aisha ta so ta cire damuwa daga zuciyarta hakan ya qi yiwuwa, domin tun jiya da aka yi maganar auren Abdul da Yasmin Abdul ya canza mata. Tunda ya kira ta a mota suna hanyar komawa gida ita da su Daddy ba ta daga ba, sai daga baya ya kira ta yana ba ta haquri tare da kalaman kwantar da hankali bai sake kiran wayarta ba. Ta yi matuqar qoqari gurin boye damuwarta, don kada ta tashi hankalin su Mommynta, kuma ta yi nasarar hakan. Ita ce ma ta taya ta aiki kamar yadda ta saba, suka kammala hada abin kari, amma ba ta ci komai ba sai ta yi wa Mummy qaryar tana azumi. Da mamaki suke kallon ta, abinka da wacce ba ta saba qaryar ba, nan take ta fara sosa kai tana neman shiga rudani. A hanzarce ta miqe ta nufi hanyar dakinta tana fadin “Mummy zan yi wanka.” Ba ta jira amsarta ba ta shige daki ta turo qorar. Wayarta ta dauko duk da ba ta yi tunanin samun miss calls ba. Miss calls din Zainab ta gani qanwar Abdul, har guda biyar tare da baquwar lambar da ba ta san ko ta waye ba. Sai a wannan lokacin ta fahimci Abdul ya kira lambar ta sha biyu na daren jiya. Tsaki ta ja sannan ta bi kiran da Zainab ta yi mata. “Ashe ma kina gida?” Abinda ta fara furtawa kenan bayan ta daga wayar daga can 6angaren. “Ashe ma kin mai da ni shanshani mai qafar yawo kenan?” Aisha ta mayar da tambayar tana dan dariya mai sauti. "A’a, ba haka ba ne, kawai dai tambayar ki na yi.” “Ina zan je da sanyin safiyar nan? Ina nan a gida, ya aka yi?” “Ga mu nan a hanyar zuwa gidanku ni da su Maryam, ki shirya kafin mu qaraso domin fita za mu yi" “Sannu Mummyna, sai kun iso.” Dariya mai qarfi ta kwashe da ita, daga bisani ta ce, “Da dai sannu Aunty Zainab ki ka ce sai in amsa, amma ban isa haihuwar kamarki ba” “Lallai ma yarinyar nan! Zan kama ki ne.” Aisha ta fada tare da jan qwafa mai qarfi. Tana magana da Zainab ta ga kiran Abdul ya shigo, don haka da gangan ta yi ta jan hirar tasu har sai da ta sanar da ita sun shigo layinsu, sannan ta haqura ta katse wayar, bayan ta yi mata fatan isowa lafiya. Kafin ta gama maida numfashi kiran nasa ya sake shigowa, sai da ta bari yana gab da tsinkewa sannan ta daga ta yi shiru ba ta ce komai ba. Shi ne ya gaji da shirun nata ya ce, “Assalamu alaikum ya Habibati...” Kamar ba za ta amsa ba amma sanin ladan da ke tattare da amsa sallama ya sa ta amsa da “Alaikas salam.” Sannan ta ja bakinta ta tsuke. “Afuwa dai matata, na san dai na yi laifi” Ya fada cikin marairaicewa. “Au, da gaske? Laifin me ka yi in taya ka ba da haquri?” Ta fada cikin gatse, domin ya qona mata zuciya tsakanin jiya da yau. "Allah ya huci zuciyarki, amma ai ko za a yi min hukunci ya kamata a ji uzurina tukuna.” “Ai na riga da na san uzurinka Abdul, don haka ba na buqatar ka ba ni haquri, domin ba ka yi min laifi ba.” “Mene ne uzurin nawa? Kada fa ki yi zaton abinda ba haka ba ne?” “Gurin matarka ka je domin ku yi tsare-tsaren abinda za ku gudanar da bikinku. Ko ba haka ba ne?” Shiru ya yi yana mamakin yadda ta fadi inda ya je da kuma wani daga cikin abinda suka tattauna tsakaninshi da Yasmin. “Ni dai kaina bisa wuyana matata, don Allah a kar6i tubana. Wallahi ba qaramin dauriya na yi ba da rashin jin muryarki a daren jiya.” A daidai wannan lokacin su Zainab suka turo qofar dakin tare da sallama, su hudu ne duk da Zainab. Ganinsu bai sa ta daina amsa wayar tashi ba, amma nan take ta yi saurin sauya salon maganarta yadda ba za su fahimci da wa take magana ba. “Au, haba! Da gaske?” “Haba matata, don Allah fa na ce.” “Wannan sunan kamar dai ba da ni ya dace ba. “Na ji kamar hayaniyar mutane sun shiga dakinki, mun yi baqi ne?” “Eh na yi baqi ne.” Ta amsa kai tsaye. “Su waye baqin naki matata, da har kike fadin ke kadai ki kai yi baqi?” “Ba ka sansu ba. ‘Yan’uwana ne.” “Yau dai kina gara ni da yawa matata, ko dan kalaman bakinki masu zaqi kin qi furta min. Ko kina so in yi miki kuka ne?” Sai da ta yi murmushin jin abinda ya fada, sannan ta amsa masa da cewa “Ni kuma sai in yi maka dariya...” Zainab ce ta matso da bakinta kusa da wayar ta ce "Malam don Allah ka bar mana ‘yar’uwa haka, tun dazu ka dame ta ko gaisawa da ita ka qi bari mu yi.” Tana gama fadin haka ta sanya hannu ta katse wayar tana dariya. Ita ma Aisha dariya take yi tana kallon ta ta ce, “Kin san da wa nake magana da har za ki fada masa haka?” “Ko ma dai waye ai kin gama ya gama, haba... tun dazu kina amsa waya kin kyale mu?” Ta fada tana dariya hade da watso mata harara cikin wasa. “Oh, su Smally kenan! Irin wannan kashe murya da yanga ai sai ki sa ya manta a inda ya ke.” "Maryam ce ta fadi

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});