Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 9

Chapter 9

Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel – Maimuna’s Painful Story 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Daddy. Amma na lura da kamar akwai matsala tsakaninsu. Na gane hakan ne ta hanyar halin damuwa da yawan tunani da Kaigama yake shiga. Kuma duk yanda na kai da bugun cikinsa dan ya faɗa min ya ƙi faɗa. Saboda mugun zurfin ciki irin nasa. Amma ni na tabbatar akwai matsala a tsakaninsa da Mariya!” Daddy ya yi shiru yana sosa haɓarsa dake ɗauke da ɗan gajeren gemunsa irin na masu rayuwa cikin hutun nan. Can kuma ya dubi Mu'az yace. “In dai kuwa haka ne ya kamata a ji abin da yake faruwa” “Haka ne Daddy. Sai ka kiransu su duka, dan su zo ka ji abin da ke faruwa a tsakaninsu, wata ƙila idan kai ka tambaya za su faɗa maka. Kuma ka ga sai a sasanta su!” Daddy ya yi murmushi yana kallonsa. “Shi yasa nake jin alfaharin cewa bayan na mutu kai ne za ka gajeni. Saboda a bayan bauɗɗaɗɗun ɗabi'unka akwai halaye masu kyau. Haƙiƙa ka yi tunani me kyau. Allah ya maka albarka, ya kuma baka ladan zama sannadiyyar gyara sunnar fiyayyen hallita. Tun da kai ka ƙi raya sunnar!” Mu'az ya yi murmushi yana shafa gajerar sumar kansa me ƙarfi kamar ta sauran Africans. Amma da yake tana jin gyara kuma ba ya tarata sosai sai ta yi kyau abinta. “Daddy! Zan yi aure fa. Kawai dai ni harkar 'yan matan ce bata gabana. Bana son raini Daddy, 'yan matan yanzu kuma sun iya raini!” (MJ ne ya faɗa. Nii dai ba ruwana!) Daddy ya dara. “Allah ya baka mace ta gari, sannan ya baka wadda za ta yi haƙuri da kai, ya kuma baka wadda ba za ka zalunceta ba. Sannan ya baku zuri'a ta gari!” Mu'az ya miƙe tsaye yana murmushi. “Oh lord of mercy!. Irin wannan addu'a haka Daddy?” “To ai baka ce amin ba” “Amin Daddy” Ya amsa yana fita daga falon. Kai tsaye ya nufi sashensa dake can wani gefe da ban na gidan. Falo ɗaya ne da ɗaki sai bathroom. Tun daga falo ya cire rigar jikinsa. Dan shi da riga kamar maƙiya haka suke. Idan ka ga ya saka riga fita zai yi. Amma muddin zai zauna a sashensa to fa ba zai sakata ba, a cewarsa wai takura shi take. Yana shiga ɗaki ya aje rigar a kan bed. Sannan ya kunna kiɗa ya yi zamansa a ɗakin. Saboda yawan jin kiɗa ɓabi'ar sojoji ce. Bai haura mintina biyar da shigowa ɗakin ba aka kira wayarsa. Hakan ya sa ya rage sautin kiɗan. Ya ɗaga wayar yana wani haɗe rai, kamar wanda aka cewa ya sha magani ba ruwa. Kuma hakan ya samo asali ne daga ganin sunan me kiran. Yasmin. Wata yarinya ɗaya tilo da ta nace a duniya kan shi take so. Kuma cikin wani ikon Allah sai aka yi rashin sa'a shi babu sonta a tsarin rayuwarsa. Dan yace shi bata masa ba, saboda ta cika naci da yawa. “Yanzu abin da kake min ka kyauta Mu'az?” Muryarta me sanyi ta fito daga cikin wayar. Ya lumshe idonsa yana murza goshinsa. “Me na yi kuma?. Ko da yake, ai ba'a rasa nono a ruga. Da ma ni kullum me laifi ne!” Daga ɗayan ɓangaren, Yasmin ta girgiza kanta. “Ko kaɗan Mu'az ba haka ba ne. Ni dai kawai abu ɗaya nake so daga gareka. Kuma shi ne na kasa samunsa har yanzu. Kulawa ita ce abin da nake buƙata Mu'az. Ya kamata ka riƙa nuna cewa ina da muhimmanci a cikin rayuwarka!” “Me ya sa zan miki ƙarya?” Cikin rashin fahimta Yasmin tace. “Ƙarya kuma? What do you mean?” “Yes, ƙarya. Did you want me to be saying that i love you?. Bayan kuma a zahiri ba haka ba ne” Ƙwalla ta zubo daga idon Yasmin. “Mu'az!” Ta kira cikin sanyin murya. “Na'am” Ya amsa. “Ina so na tambayeka abu ɗaya” “Faɗi, ina ji” “Mu'az kana sona, ko a'a?” Kai tsaye yace. “Bana sonki Yasmin. Ban taɓa sonki ba, kuma bana tunanin fara sonki ko da a nan gaba” Cike da baƙin ciki Yasmin ta kashe wayarta. Yana jin ta sauƙa a layi ya cilla wayar kan gado. Sannan ya ƙure Volume ɗin waƙar da yake ji hankalinsa kwance kamar tsumma a randa. Kamar ba shi ne ya gama tarwatsa zuciyar wata yanzu ba. _Share fi sabillilah❤️_ ------------------------ _I have told you that KADDARA CE! Isn't free!_ _If you want to subscribe pay ₦300 to._ 5487270431 Salma Isah Monie point And send the evidence of payment via 08130172792. *Daga alƙalamin Salma Ahmad Isah✍️.* *CANDY CE🦋.* °°°°°°°°°°°°°°°°°° *ƘADDARA CE!* *©SALMA AHMAD ISAH.* *CANDY🦋* _ArewaBooks @SalmaAhmad_ _Wattpad @Salma_Ahmad_Isah_ *04* *Unguwar Fantai, Haɗejia local government, Jigawa state.* MAIMUNA POV. Su uku ne jere a bakin titi. Kuma ko wacce a cikinsu kayan siyarwarta ne a gabanta. Ɗaya tana suyar awara, ɗaya tana soya wainar fulawa, sai kuma ita da bokitin kununta ke aje a gabanta. Tun daga nesa ta hangi kawunta, ƙanin mahaifinta wato Kawu Barau. Duk da duhun magariba da ya fara sauƙa bai sa ta kasa gane shi ba. Baki ta washe ta miƙe tsaye tun kafin ya iso inda suke. Kuma shi ma har ya iso inda suke murmushi yake. “Kawu ina wuni!” “Lafiya ƙalau me sunan Hajja” Kawu Barau ya amsa yana kallon tilon 'yar ɗan uwansa. A lokacin ya lura da hannunta na dama dake ɗauke da tabon ƙuna. Lokaci guda fara'ar kan fuskarsa ta yi balaguro. “Me sunan Hajja ya aka yi kika ƙone?” Maimuna ta kalli hannunta, sannan ta kalli kawu tana faɗin. “Auwwa ce ta ƙonani rannan. Amma ai ya fara warkewa, saboda Mummynsu Maryam ta kaini asibiti, kuma har magunguna ta sai min” Cike da tausayawa Kawu ya girgiza kansa yana faɗin. “Wa cece kuma Mummyn su Maryam?” “Wannan ƙawar tawa, jikar tsohon Kaigama” “To to. Na gane, 'yar gidan Bara'atu ko?. 'Yar Alhaji Haruna Kaigama me rasuwa, ƙanwar Alhaji Bello Kaigama na yanzu!” Maimuna ta gyaɗa masa kai. “Amma ko ta kyauta. Allah ya biyata da gidan aljanna... Amma baki faɗawa Hajja ba?” Ta yi saurin gyaɗa masa kai. Dan bata faɗawa kakar tata ba. Saboda a tsakanin kwanakin ba ta je gidanta ba. Kuma ko ta je ma ballale ta faɗa ba idan har ba tambaya Hajjan ta yi ba. “To Allah ya kyauta. Ya saka miki da abin da Auwwa take miki. Ki ci gaba da haƙuri kin ji ko me sunan Hajja?. Allah na sane da ke, kuma zai kawo miki ƙarshen wannan wahalar taki. Ki ci gaba da addu'a. Kan Allah ya baki ikon cinye wannan jarabawar da yake miki” Faɗin Kawu Barau yana lissafo 'yan kuɗaɗen da suka sa aljihunsa yin nauyi a safiyar yau. Cike da damuwa Maimuna ta gyaɗa masa kai. “To Kawu. Inshallah zan yi” “Karɓi wannan ba yawa. Na san magungunanki sun ƙare, dan wallahi suna raina, shi ya sa na kasa sukuni har sai da na samo kuɗin siyansu, dan na san a yanzu lokacin sanyi kin fi buƙatarsu” Maimuna ta yi murmushi tana girgiza masa kai. “Ai duka Mummy ta siya min har da folic acid da palludrine” Cike da mamaki Kawu ya kalli kuɗin hannunsa, sannan ya ƙara miƙa mata. “Duk da haka dai ki karɓa, ba zaki rasa amfanin da za su

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});