Chapter 3
Chapter 3
lokutan ma sai ta yi sati tana zuwa gidan Hajjan ba tare da ta gan shi ba. Dan shi kullum yana gona ko kasuwa wurin aikinsa. A wasu lokutan ma shi da kansa yakan zo domin ya dubata. Idan kasuwa ta yi kyau har kyautar kuɗi yake mata, ko ya sai mata wasu daga cikin magungunan cutarta... “Ƙafar ma ciwo take?” Tambayar Ya Sadiq ta dawo da ita zahiri. Hakan ya sa ta kalli ƙafarta ta hagu sanna tace. “Yau da safe na tashi tana min ciwo” “Ai da ma da sanyi sai a hankali. Ita sickler ba ta son sanyi, ga shi ke kuma rabin rayuwarki a cikin sanyi take... Ki yi ta haƙuri kin ji Maimuna. KADDARA CE!. Kuma da yardar Allah za ki cinye wannan jarabawar!” Faɗin Mummy. “Kina shan folic acid ɗinki?” Ya Sadiq ya sake tambaya. Maimuna ta girgiza masa kai. “Ban sha ba. Saboda aikin da ya min yawa yau ya sa ban sha tun safe ba. Kuma yanzu da na duba inda nake ajewa sai na ga ta ƙare. Saura palludrine kawai!” Mummy na latsa wayarta ta girgiza kai tana faɗin. “Allah ya kyauta” A lokacin Maryam ta fito daga kitchen riƙe da plate. Ta aje mata a gabanta tana faɗin ga shi Maimuna. “Na gode” Maimuna ta mata godiya kamar yanda ta saba. Da yake tana jin yunwa sosai. Sai ta cinye abincin da wuri. Maryam ta bata ruwa ta sha ta gode Allah. Sannan ta godewa Mummy. Da za ta tafi Maryam tace za ta rakata. Sai Mummy tace wa Ya Sadiq ya tashi ya rakasu. Sannan ta bawa Maimuna kuɗin napep. Wanda za ta yi amfani da shi wurin zuwa asibitin. Su uku suka fita daga gidan. Sai da suka raka Maimuna har layinsu. Sannan suka yi sallama suka juya. A sace Maimuna ta shiga gidan. Ta saka sakata. Sannan ta shiga ɗakinta ta ɗaura gidan sauro. Ta shiga ta kwanta tana jin yanda sauraye ke cizonta. Saboda net ɗinta da yake a ɓule. Ga kuma sanyi da ya dameta. Ita fa tun ba yau ba ma ta riga da ta san cewa ikon Allah ne ya sa take rayuwa har yanzu. Amma ba dan ikon Allahn ba bata jin me cuta irin tata zai kasance a halin da take ciki, kuma ya ci gaba da rayuwa. *No.42, Inuwa Wada crescent, Utako, Abuja.* FARUK POV. A hankali ya tura ƙofar ɗakinsa da ya fito daga ciki ya rufe. Sannan kai tsaye ya soma taka strais zuwa ƙasa. Abu na farko da ya fara arba da shi a ƙasan shi ne. Matarsa Mariya da kuma ɗansa Hilal. “Babana” Ya faɗi yana ɗaukan ɗansa ɗan wata goma sha ɗaya da haihuwa. Kafin ya juya ya kalli matar tasa dake zaune a kan sofa. “Mary!” Ya kirata da sunan da shi kaɗai yake kiranta da shi. Mariya ta ɗaga kai ta kalle shi. Kafin ta aje wayarta da take latsawa a kan sofa ta miƙe tsaye. “Fita za ka yi?” Ta tambaya ganinsa sanye da kayansa na aiki. Wato kakin sojoji. Kasancewarsa soja. Ya shafa kan yaronsa da ɗayan hannunsa yana faɗin. “Eh zan fita” “A dawo lafiya” Kawai ta faɗi tana karɓar Hilal ɗin dake hannunsa. Sannan ta koma ta zauna tana aje yaron a gefenta. Faruk ya kalleta sanna ya girgiza kansa ya juya ya fita. Shi har yanzu ya kasa gane abin da yake damun Mariya. Yanzu kusan shekaru uku da aurensu shi da ita. Amma har yanzu babu wata shaƙuwa ta musamman irin wadda ake buƙata tsakanin miji da mata a aurensu. Bayan kuma auren soyyaya suka yi shi da ita. Kasancewar ita Mariyan ƙanwa ce a wurin abokinsa Mu'az. Kuma ta hanyar Mu'az ɗin ya fara ganinta. Har ta kai ga ya fara sonta. Kuma ba tare da ɓoye-ɓoye ba ya furta mata cewar yana sonta. Kuma ita ma ta nuna amincewarta kan hakan. Shi ya sa ba a daɗe ba aka yi aurensu. A farkon aurensu ba zai ce babu soyyaya ba. Amma tun bayan da ta samun cikin Hilal komai ya sauya. Duk da da ma can ita ba mace ce me yawan magana ba. Gaisuwar da sojoji biyun da suke gadin gidansa ke masa ce ta dawo da shi zahiri. Ya dube su yana amsawa. Kafin suka buɗe masa gate ya fita da motarsa daga gidan. Sai da yafara biyawa ta gidan mahaifiyarsa Hajiya dake kusa da nasa gidan. Ya gaisheta kafin ya wuce wurin aiki. Kasancewar akwai wani aiki na binciken mutuwar abokiyar aikinsu dake gabansu ya sa yana zuwa barrack bai nemi kowa ba sai Mu'az. Aboki, kuma abokin aikinsa. _Share fi sabillilah❤️_ ______________ Za ku iya karanta wannan littafin a ArewaBooks, da ma wasu litattafaina na baya @SalmaAhmad. Sai kuma Wattpad @Salma_Ahmad_Isah. Saboda page ɗin can za su fi na nan tsayi. And don't forget to follow, like, share and comment. *Daga alƙalamin Salma Ahmad Isah✍️.* *CANDY CE🦋.* °°°°°°°°°°°°°°°°°° *ƘADDARA CE!* *©SALMA AHMAD ISAH.* *CANDY🦋* _ArewaBooks @SalmaAhmad_ _Wattpad @Salma_Ahmad_Isah_ *Paid book* *02* *No.53, off Justice Clara Ogunbiyi street, Asokoro, Abuja.* MU'AZ POV. Mutum biyar ne zaune a kan dinning table suna yin breakfast. Shi kaɗai ne a cikinsu yake cin abinci da hannunsa. Yayin da kowa yake ci da spoon. Mahaifiyarsu Hajiya Hauwa, wadda suke kira da Mummy ce ta dube shi. Yanda ya dage yake cin abincinsa bil haƙƙi da gaskiya. Dan idan kana so ku saɓa da Mu'az a ƙi ba shi abinci lokacin da yake jin yunwa. Idan kuma kana so ka burgeshi ka masa kyautar abinci ka ga ƙauna. Shi da abinci 5 and 6 ne. Shi ya sa kaf yaran gidan su biyar. Wanda suka ƙunshi babbar yayarsu 'yar matar Daddynsu ta farko wadda Allah ya yi wa rasuwa. Me suna Farida. Sai shi da ya kasance ɗan Mummy na farko, sai Mariya da take bi masa. Sanna Safiyya da ta ci sunan mahaifiyar Daddy, suna mata inkiya da Mima. Sai auta Na'im. Duk cikinsu ya fi kowa ƙiba. Duk da shi ma ba wai ƙibar ya cika ba. Amma ya fi su jiki. Sai Mima da ita ma take da 'yar ƙiba. Kuma a duk cikin yaran Daddy su biyar, ya fi kowa farin fata. Dan shi farin Mummy ya biyo su kuma duk baƙin fatar Daddy suke biyowa. Hakan ya sa ya fita da ban a cikinsu. Idan ka ganshi ba lalle kace ɗan gidan ba ne. Saboda yana da fari sosai, saɓanin sauran 'yan uwansa da suka kasance baƙaƙe. “Mu'az!” Mummy ta kira. Hakan ya sa ya ɗago da fararen idanuwansa ya ɗora a kanta yana amsawa. “Na'am Mummy” Cikin tsare shi da ido Mummy tace. “Me ka je ka aikata a gidan Hajiya Hadiza?... Jiya da daddare bayan ka dawo daga gidan ta kirani tana ta masifa!” Maganar Mummy ta janyo hankalin kowa kansu. Shi kuma sai ya yi murmushi yana maida hankalinsa kan cin abincinsa. Dan ya tuno da tsiyar da yaje ya yi a wurin yarinyar aminiyar Mummy da tace masa ya je dan su daidaita juna. “Ka san baka da gaskiya ke nan?” Faɗin Mummy. Alhaji Jibrin Gimba Gashuwa ya kalli matarsa yana faɗin. “Me ya yi kuma?” Cike da jin haushin abin da ya aikatawa 'yar aminiyarta Mummy tace.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31