Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 28

Chapter 28

Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel – Maimuna’s Painful Story 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da gidan Hajiya za ta je bai kamata ta tafi ta bar shi a gidan shi kaɗai ba. Kuma halin da ya zo ya same shi a ciki ne ya ƙara baƙanta masa rai. Ya zo ya same shi cikin yunwa. Ga kuma diapers ɗin dake jikinsa ta cika da bayan gari da kuma fitsari. Da alama tun safe da aka saka masa ba'a sauya masa ba. Tsaki ya ja yana kaiwa dubansa kan agogon dake bango. Ganin goma ta haura ya sa ya sake jan wani tsakin. Sannan ya sa hannunsa a kan ɗansa yana shafawa a hankali. Lokaci guda ya ji Hilal ya zabura, sannan ya kuma canyara kuka yana ƙara zabura. Saurin kaiwa hannu ya yi ya gyara masa kwanciya a tsakiyar hannunsa. Yana karantowa ayatul kursi, tare da tofa masa. A hankali a hankali kuma sai kukan nasa ya ragu, har ya yi shiru, ya dawo yana jan zuciya, kuma duk wannan abin da ya faru idonsa a kulle yake gam. Sai ya ɓata fuska yana turowa leɓensa na ƙasa. Yanayin fuskar tasa ya bawa Faruk dariya. Dan haka ya yi murmushi. Ya shafa kansa, sannan ya sumbaci goshinsa. Ya rungume ɗansa yana faɗin. “Allah ya raya min kai babana!” Shiru ya yi ya ɗaga kai ya kalli ƙofar falo da aka buɗe. Mariya ta shigo tana kallonsa. Kuma ba tare da tace masa komai ba ta wuce shi ta nufi stairs. Kamar daga sama ta tsinkayo muryarsa, da amon da bata taɓa sanin cewa yana da shi ba. “Daga ina kike?” Sai ta tsaya cak. Sannan ta juyo. Sai ta gan shi a tsaye, Hilal ɗin da ta shigo ta same shi rungume da shi kuma ya kwantar da shi a kan sofa. “Tambayarki nake Mariya!” Ya sake magana yana tsareta da ido. Sai ta dawo cikin falon, ta tsaya a gabansa ba tare da ta masa ko tari ba. “Ina kika je ba tare da izinina ba? Kuma kika fita kika bar min ɗana a cikin gida shi kaɗai kamar maye!?” Sai ta yi murmushin da ta saba. “In da ka aike ni na je!” Lokaci guda wannan murmushin da take, da kuma yanda ta masa maganar a sigar dake nuna bata damu da ɓacin ransa ba suka fara hasalla zuciyarsa. Ya ji ya kawo wuya. Duk da shi bai cika saurin fushi da saurin kai hannu ba irin na Mu'az ba. Amma yau dai kam yana jin Mariya ta kai shi bango. “Na farko kin aikata min laifin fita daga gidana ba tare da izinina ba. Na biyu kin fita kin bar min ɗa a gida shi...” Bai kai aya ba Mariya ta katse shi. “Wai ni a kanka aka fara haihuwa? Magana ɗaya biyu sai ka sako ta ɗanka a ciki? Ai ni ma ɗana ne, ba shegensa na yo a waje ba!...” Ba ta rufe bakinta ba ta ji sauƙar mari a kuncinta na dama. Lalle yau ta ƙure Faruk har wuya, tun da yake bai taɓa ɗaga hannunsa a kan wata mace ba, ballantana matarsa ta auren sunnu, matar tasa ma Mariya, wadda yake jin sonta har cikin ransa. Amma abin da ta aikata yau ya sa ba zai iya yafe mata ba kamar sauran kura-kurenta na baya. Ita ce da laifi, amma ji yanda take ɗaga masa murya kamar ita ce mijin, shi kuma matar. “Ba ki isa ba Wallahi... Mary ba ki yi wannan tasirin a zuciyata ba da zai sa ki aikata min laifi, sannan ki zo kina ɗaga min murya na ƙyaleki...” Mariya da mamaki ya sa ta sandare ta ci gaba da kallon fuskarsa da ta sauya mata lokaci guda. Ko dai ba Faruk ɗinta ba ne?. An yama kuwa wannan mijinta ne?... Har ya gama faɗansa ya ɗauki Hilal ya bar mata falon ba ta iya yin ko da tari ba. Cike da jin haushin da bai gama washewa a ransa ba Faruk ya kwantar da Hilal a kan gado. Ya lulluɓe shi yana jin wani abu na baƙin ciki na tokare masa maƙoshi. Gaba ɗaya ma ya rasa yanda zai yi ya huta. MAIMUNA POV. Yau da matsanancin ciwon baya ta tashi. Amma duk da haka sai da ta yi duk ayyukan da suka zame mata wajibi a gidan. Tana yi tana kuka, saboda yau ciwon da take ji ya fi na kullum. Ta yi doyar safe. Ta je ta siyar, sanan ta fara haɗa kunun dare. Tana tsaka da tatar hatsin da ta karɓo a wurin niƙa Auwwa ta kirata. “Ke Maimuna!” Da ƙyar ta iya ɗaga yalayen idonta irin na masu sickler ta kalli Auwwan. Sannan ta amsa. “Na'am” “Zo!” Da ƙyar ta iya miƙewa tsaye. Tana dafe da bayanta da yake matsanancin ciwo. Ta nufi inda Auwwa ke tsaye. Auwwa ta miƙa mata dubu uku, ta kai hannu ta karɓa. “Kasuwa za ki zo ki tafi ki siyo min doya. Na ga sauran guda ɗaya!” A take Maimuna ta ji ruwan dake zuba a idonta ya ƙara gudu. Dan haka ta ɗaga kai ta kalli Auwwa. Yanzu idan ba'a rage mata aikin dake kanta ba ai ba a ƙara mata ba. A yanayin jinyarta kwata-kwata ba'a son su shiga damuwa ko tashin hankali, dan hakan kan iya taɓa zuciyarsu kai tsaye. Amma a gidansu sam ba'a damu da hakan ba. Ɓacin rai kullum sai Auwwa ta kasa mata a fai-fai ta ɗauka. “Ko ba za ki je ba ne?” Ganin Auwwan na shirin ɗaukan madoki ya sa ta yi saurin girgiza kai. “A'a zan je” Ta rufe leɓenta ƙwalla na ƙara sauƙo mata. Ba tare da tace komai ba ta ja siraran ƙafafunta da ba su cika ƙwari da lafiya ba ta ɗauki hijabinta. Ta saka. Sannan ta fita waje tana kallon yanda rana ta baza duniya. Da ace tana da gata da a mashin za ta je kasuwar. Amma a halin da take ciki na magen maƙota ma ta fita muhimmanci ba za ta samu wannan gatan ba. Ba komai take hasasowa ba face nisan dake tsakanin gidansu da kasuwa. A abin hawa ma tafiyar ba kaɗan ba ce, ballantana kuma a ƙafa. Ga kuma yanda rana ta ƙwalle a sama, kamar ba lokacin hunturu ba, duk da sanyin ya fara ja baya. Ga ciwon baya ga na ƙafa, ga kuma na jiki da na zuci. Haka ta ci gaba da daurewa tana tafiya. Idan ta gaji sai ta samu gefen hanya ta zauna ta huta, kafin ta tashi ta ci gaba da tafiya. Da haka har ta iso titin ƙofar fada. A nan ɗin ma sai da ta zauna ta huta. Tana ta haki, ga bayanta da take jin kamar zai karye. Kuma idan aka raba tafiyarta biyu, ba ta ɗauki kashen ɗaya ba, sai dai a kirata da kwata. Hawaye ne ya zubo mata. Ta kai hannu ta share, sannan ta raba kanta da wannan hutun na jaki kaya a ka. Ta ci gaba da jan ƙafarta da ƙyar... Har ta hau kan titi a ƙoƙarinta na tsallakawa... A dai-dai lokacin kuma wani mummunan haɗari ya faru, a tsakiyar titin, a tsakiyar gari, a tsakiyar jama'a da ma duk wani me wucewa. *. *. *. Gambo ne da uban gidansa, wato me napep ɗin da yake ba

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});