Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 16

Chapter 16

Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel – Maimuna’s Painful Story 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kuma sai yace. “Wani kalar kaya ne a jikinta?” “Baba tana sanye da abaya ruwan goro!” Ali ya amsa masa. Baba ya kuma yin shiru, can kuma sai ya gyaɗa kai. “Ƙwarai kuwa da gaske, na gano, lokacin da ta zo ta wuce ina zaune a nan. Har nake cewa wata ƙila wani mugun abin ne ya biyota...” Muktar ya yi murmushi. “Yauwwa Baba. To ko za ka iya tunawa da inda ta yi bayan ta wuce ta nan ɗin?” “Ƙwarai zan iya tunawa. Dan har ta ƙulewa ganina idona na kanta. Saboda na ga kamar akwai wata baƙar mota dake bibiyarta.” Tsabar jin daɗi yasa Muktar zama kusa da baba. Sannan yace. “Haka nake son ji Baba. To nuna min ta inda ta bi” Baba ya juya bayansa, sannan ya nuna musu layin dake bayansa. “Ta nan haka ta bi. Kuma har ta ɓace min baƙar motar nan na binta” Muktar ya gyaɗa kansa. Sannan ya miƙe tsaye. Ya miƙawa baba Hannu suka kuma gaisawa. Ya masa godiya. Suka juya zuwa wurin motocinsu. Yana shirin shiga motar ya tsinkayo muryar Ali cikin faɗin. “Sir ya kamata mu shiga layin mu bincika ko akwai wanda ya ga sanda aka ɗauketa” Ba tare da ya juyo ba ya yi murmushi. Sannan yace. “Ka ɗan juya bayanka ta ɓarin hagu. Akwai wani matashi a kan mashin da yake amsa wayar ƙarya tun sanda motarmu ta tsaya a nan. Ɗa leƙen asiri ne. Idan muka ce za mu shiga layin a yanzu akwai matsala. Ni da kai ne kawai, kuma mu duka ba mu da bindiga. So sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi. Yanzu mu koma headquarter. Next time za mu haɗe da shi!” Yana gama faɗin hakan ya buɗe motarsa ya shiga ciki. Ali ya juya ya kalli matashin dake waya yana satar kallonsu. Kuma ba tare da yace komai ba shi ma ya zagaya ta ɗayan ɓangaren ya shiga motar ya ja suka bar wurin. *No.42, Inuwa Wada crescent, Utako, Abuja.* *08:32 na safe.* FARUK POV. Kasancewar yau an tashi da yayyafi ya sa daddaɗar iskar dake haɗe da sanyin ruwan saman a aka yi yake kaɗa curtains ɗin dake ɗakin. Iskar da ta ɗan ƙara ƙarfi ce tasa windown ɗakin ya buɗe. Sannan iskar ta kaɗa labulen da yake a saitin inda gadon ɗakin yake. Sanyin iskar ya busa a kan fatar jikinsa. Hakan ya sa ya motsa ƙafafunsa dake cikin takalmi. Kafin ya rintse idonsa dake rufe, saboda wani ciwo da kansa ya fara lokaci guda. Hannunsa na dama ya ɗaga ya ɗora a kansa. Sannan ya ja iska ta bakinsa cike da jin zafin ciwon kan. A hankali ya buɗe idonsa. Sannan ya rufe, ya kuma buɗewa, ganin gari ya yi haske ya sa ya yi saurin miƙewa zaune. Ya dafe kansa dake masa ɗan karen ciwo. Da ƙyar ya miƙe tsaye ya shiga banɗaki. Bayan wani lokaci ya fito. Ya yi sallahr asuba da ta wuce shi. Bayan ya idar bai miƙe daga kan dardumar ba sai da ya yi ta jero istigfar. Saboda rashin yin sallahr a kan kari. Haka ya zauna a kan dardumar yana nazarin da bai san na miye ba. Har yanzu yana jin kamar akwai abin da ya manta, kamar akwai wani abu da aka goge daga cikin tunaninsa. Amma kuma ya kasa tuna miye. Jin an buɗe ƙofar ɗakin ya sa ya ɗaga kansa ya kalli Mariya da ta shigo. Ganinsa cikin wannan yanayin da ya kwana da shi a jiya ya sa ta yi miskilin murmushi. “Sai yanzu ka farka?” Ya kalleta. Amma bai ce mata komai ba. Dan ji ya yi bakinsa ya yi nauyi, ga kansa da yake sarawa. “Ya Mu'az ya zo yana waje. Yace ya jika shiru ba ka je barrack ba, kuma ya kira wayarka baka ɗaga ba, shi yasa ya zo!” Da ƙyar ya iya miƙewa tsaye. Sannan ya sa hannu ya cire rigar jikinsa yana faɗin. “Ki ce masa ina zuwa!” Mariya ta juya kai, sannan ta fita daga ɗakin. Ta dawo ƙasa. Idan ta bar Mu'az da Hilal zaune suna wasa. Ganin ta fito ita kaɗai ya sa Mu'az ya ɗaga kai ya kalleta. “Yana ina?” Ta zauna a kan kujera tana faɗin. “Wanka zai yi. Amma yace yana zuwa” Mu'az ya gyaɗa kai, sannan yace. “Me ya same shi wai?” “Kwana ya yi da ciwon kai, shi yasa ya makara” Ya kuma gyaɗa kansa yana ɗaga Hilal. Suka ci gaba da wasa da Hilal ɗin, har zuwa sanda Faruk ya sauƙo sanye da kayan aikinsa, wato kakin sojoji. Kana ganinsa ka ga wanda ba ya cikin nutsuwa, ko kuma mara lafiya. “Kaigama!” Mu'az ya kira yana miƙewa tsaye, yana riƙe da Hilal. Faruk ya ɗan yi murmushi yana lumshe idonsa da kalarsa ta sauya. Sannan ya buɗe shi a kan Hilal. “Idan kan naka bai daina ciwo ba za ka iya komawa ka huta” Faruk ya girgiza kansa. “A'a. Zan iya zuwa barrack. Mu je kawai” “Kuma fita za ka yi ba tare da ka ci abinci ba?” Mariya dake gefe ta faɗi. Hakan ya sa suka dubeta a tare. “Yanzu na makara. Ki aje min abincin dare kawai” Faɗin Faruk. “A'a ka zauna ka ci abincika kawai” Cewar Mu'az. “Bana jin cin abincin ne. Mu je kawai, zan ci abincin a barrack” Mu'az ya jijina kansa, sannan ya miƙawa Mariya Hilal. Suka mata sallama suka fita a motar Mu'az. Suna tafiya a hanya Ƙaddara tasa Mu'az tsayawa a wani boutique me sunan ‘UMMUL BANAT BOUTIQUE’. A sanda motar ta yi parking a harabar boutique ɗin Faruk ya ɗaga kansa ya karanta sunan boutique ɗin. Sannan ya kalli Mu'az yana faɗin. “MJ me za mu yi a nan?” Mu'az na cire seat belt ya amsa da. “Na'im ne yace na sai masa sweater” “Okay mu je” Ya faɗa yana buɗe ƙofar motar. A tare suka nufi ƙofar shiga boutique ɗin. Boutique ɗin da ƙaddarar Mu'az ke zaune a ciki. Boutique ɗin da zuwansa cikinsa zai sauya rayuwarsa gaba ɗaya. Kamar yanda Na'im ya wassafa masa yanayin sweatern da yake so ita ya ɗauko masa har guda biyu. Rigunan na riƙe a hannunsa suka nufi wurin cashier. Ya juya kansa yana yi wa Faruk magana. Ya ji ya ci karo da mutum. Kuma a lokaci guda abinda ke hannun mutumin da sukayi karon, wanda yake da tabbacin ya fishi tsayi ya zube a jikin rigarsa. A lokaci guda zuciyarsa ta tafarfasa har ta fara shirin ƙonewa. Hakan ya sa ba tare da ya duba da wa ya ci karo baya ɗaga hannunsa da bai riƙe rigar da shi ba, ya sharara wa budurwar dake tsaye a gabansa mari. Wata iriyar ƙamewa ta yi. Ta saki kofin ruwan dake hannunta, wanda ruwan cikin ya zube a jikin rigarsa. Sannan ta ɗora hannunta na dama a kan kuncinta. A take hawaye suka soma zubowa daga raunannun idanuwanta. Da ƙyar ta iya ɗaga idonta ta saka su cikin nasa. Kuma shi ma sai a lokacin ya samu damar kallonta. Wata farar matashiya ce, da a shekaru ba za ta ɗara Mima ba. Hawayen da suka wanke mata fuska ya sa ya ga fuskar tata har wani ƙyalli take. Sanye take da farar Oxford shirt. Da

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});