Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 4

Chapter 4

Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel – Maimuna’s Painful Story 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

“Tsabar shi abin magana ba ya masa kaɗan. Ya taka ya je har gidan aminiyata Hajiya Hadiza, dan ya ga 'yarta Rashida su daidaita. Tun da shi ya kasa zaɓawa kansa matar aure. Wai ya dubi Rashida ya ci mata mutunci, har da cewa wai ita ƙazama ce. Kuma ta masa kaɗan a matsayin matar aure!... Maganganu dai babu daɗin ji!” Daddy ya dubi Mu'az dake murmushi. Kafin ya kai ga cewa wani abu, Mu'az yace. “Iyaka abin da na ce kawai ta faɗa. Ba ta faɗa miki abin da ita 'yar tata ta min ba?” “Me Rashidan ta maka?” Daddy ya tambaya. “Saboda Allah Daddy. Kamar ni Mu'azzam Jibrin Gimba za ta shanya a ƙofar gida ina jiranta. Wai tana kwalliya?. Ko me za ta yi wa kwalliyar?. Wannan mummunar baƙar ƙazar fuskar tata da bata rabo da majina sanda tana yarinya ko me?... Kuma da ma can fa ni ba ta min ba. Yarinyar ba class ɗina ba ce. And ta cika rawar kai da yawa!” Cike da mamakin abin da yayanta ke faɗi a kan Rashida Mima ta ɗaga kanta sama tana hango fuskar Rashidan. Ko ita da take mace Rashida na burgeta. Saboda iya wankanta da son gayu. Amma tsabar wulaƙanci irin na Mu'az cewa yake wai ƙazama ce!. “Ya Mu'az Rashidan ce ƙaz...” Shiru ta yi saboda kallon da ya mata. Ta haɗiye maganar ta kora da miyau ɗin bakinta. Mu'az ya harareta yana faɗin. “Ƙaramar mara kunya!...” “Sannu shugaban marasa kunya!...” Faɗin Mummy a ƙufule ita ma tana wurga masa harara. “Mu'az” “Na'am Daddy!” Ya amsa a ladabce. “Rashida ce ba ta maka ba ko wata ɗabi'a ce gareta wadda baka so?” Ya yamutsa fuska yana faɗin. “Ta min ƙanƙanta da yawa. Sa'ar Mima ce fa Daddy. Kuma taba da rawar kai. Ga ta cika iyawa... Gaba ɗayanta ma bata min ba. I dislike her at all!...” “Ka kyauta. Ka kyauta da ka zubar min da mutunci a idon aminiyata” Mummy ta tari numfashinsa. “Hauwa! Kin san ni me son abin da yarana suke so ne. Tun da har baya sonta babu yanda za ayi na aura masa ita. Da ace yana sonta kuma sai inda ƙarfi na ya ƙare wurin neman aurenta!” “Shi ya sa nake sonka Daddy. You're the best!” “Ban gama da kai ba ai... Dan baka son Rashida bai kamata ka riƙa kusheta ba. Hakan babban kuskure ne. Da fatan za ka kula nan gaba!” Sai ya sunkuyar da kansa yana faɗin. “To Daddy. Za a gyara!” Wayarsa dake aje a gefen plate ɗin da yake cin abinci ce ta shiga ringing. Hakan ya sa ya ɗauka domin duba me kiran, ganin Faruk ne ya sa ya amsa. “My Gee what's up?” “Fine Wallahi. Ya ? Me ya sa ba ka zo barrack ba har yanzu?” Mu'az ya miƙe tsaye wayar kare da kunnensa ya nufi sink domin wanke hannunsa da yaci abinci da shi. Saboda shi duk rintsi duk wuya ba ya cin abinci da spoon ko fork. “Cin abinci na tsaya. Ka san aikin nawa ma ba zai iyu ba ba tare da na cika cikina ba!” “Aikin ke nan ai. To sai ka yi sauri ka zo dan mu je mu haɗu da Muktar (Ɗan sandan da yake bincike a kan case ɗin mutuwar Munira) ɗin. Tun da yace gobe zai yi tafiya” Mu'az ya goge hannunsa da toilet paper yana faɗin. “On my way” Daga haka ya sauƙe wayar ya dawo dinning area. “Mummy ni zan tafi... An jima zan aiko driver ya zo ya karɓa min abinci!” Mummy ta wurga masa harara tana faɗin. “Saboda ga Mummy baiwarka ka aje za ta maka girki ko?” Mu'az ya ƙunshe daiyarsa. “Oh lord of mercy!” Ya faɗa, sannan ya kalli Mima. “‘Yar lukuta ki min girki zan aiko a karɓa min. Yau Mummy ta yi fushi da ni!” Ba dan Mima ta so ba haka ta gyaɗa masa kai. Dan ita yau ta riga da ta tsara fita tare da ƙawayenta. Kuma bata isa ta masa musu kan ba za ta yi ba. Ita a wa?. Yanzu sai ya hauta da bala'i. In ba sa'a ba ma ta kaisu ga duka. “Oga tulele ka gama mu je na sauƙeka?” Ya faɗi yana kallon Na'im. Na'im ya ɗauki bagpack ɗinsa yana faɗin. “Eh na kammala mu je” Suka yi wa Daddy sallama suka fita tare. Mummy ta yi ƙwafa. “Wai yanzu haka za'a zuba masa ido ya zauna babu aure?. Ga shi Mariya da take ƙanwarsa har da yaro ɗaya. Amma shi tsayuwa da 'yan matan ma ya ƙi. Ballantana har a fara batun yin aurensa!” Daddy ya yi murmushi yana sipping tea ɗinsa. Ya aje mug ɗin yana faɗin. “Hauwa ke nan!. Shi fa aure da mutuwa duk lokaci ne da su. Idan Allah ya nufa sai ki ga an yi nan kusa. Wata ƙila kuma shi nasa rabon a nesa yake” “Hum-um. Ai bana jin Ya Mu'az zai yi aure kwana kusa Daddy. 'Yan mata nawa Mummy ta masa?. Amma duk cikinsu cewa yake babu wadda ta masa. Har da wadda yace warin baki take. Ai babu me iyawa wannan mutumin sai Allah. Ga zafin zuciya kamar garwa shi. Ga hancini!. Ga faɗar baƙar magana kamar jikan kutare!...” “Duk zai daina with time. Har yanzu Allah bai haɗa shi da wadda za ta dace da shi ba ne...” Daddy ya katseta. Mima ta taɓe bakinta tana ganin rashin iyuwar hakan. Dan a ganinta, babu budurwar da za ta iya zama da yayanta da halayensa. Su ma da suke 'yan uwansa wasu lokutan kasa ɗaukan halin nasa suke ballantana wani da ban. *Nigerian Army resources center, Mambilla Barrack, Asokoro, Abuja.* “Hello! Sirikina ina kwana” Faɗin Mu'az a lokacin da ya shiga office ɗin Faruk dake jiransa. Dan bayan ya je ya aje Na'im a school kai tsaye ya wuto nan barrack ɗin. Saboda daga gidansu zuwa Barrack ɗin ba nisa. Faruk dake tsaye a jikin shelf yana duba wani file ya jiyo ta kalli Mu'az ɗin dake shigowa office ɗin. Kamar kullum, sanye yake da wandon kakin sojoji, da kuma rigar da suke sakawa a ƙasan rigar uniform ɗin nasu me kama da T-shirt. Amma shi kam da ma abu ne me wuya ka gan shi sanye da complete uniform. A cewarsa waccan ta saman takura shi take. Saboda shi da riga kamar maƙiya suke. Idan ka gan shi da complete uniform to meeting zai shiga, ko kuma akwai wani wurin da zai je ba barrack ba. “Sannu da zuwa sir” Faɗin Faruk yana sarawa Mu'az ɗin. Kasancewar shi ne sama da shi. Mu'az ya cire glasses ɗin idonsa yana faɗin. “Karka sa na ji kunya mana sirikina. Ni ban san wannan abin. Ka share kawai” Faruk ya sauƙe hannunsa yana murmushi. Dan wannan ɗin magana ce wadda ya haddaceta a cikin kansa. “Ina ɗana?” Mu'az ya tambaya. “Lafiyarsa ƙalau.” “An jima muna da meeting da general Haladu Mansur. Gwanda mu je mu ga Muktar kafin lokacin ya yi” Ya faɗi yana maida glasses ɗinsa. “Okay” Daga haka suka fita zuwa FCID domin jin yanda binciken mutuwar abokiyar aikinsu ya kwana. *FCID (Force Criminal Investigation Department), Moshood Abiola Road, Garki, Abuja.* “A halin yanzu mun yi nasarar

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});