Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 23

Chapter 23

Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel – Maimuna’s Painful Story 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

gaba, da yanda take ƙif-ƙifta idonta cike da zallar shagwaɓa, da kuma yanda hawaye yake zuba a kan fusarta. Kuma a hakan ya ga shatin yatsunsa huɗu a gefen fuskarta. ‘Lord have mercy!’ Ya faɗa a ranaa yana furzar da huci kaɗan.Kansa ya kawar gefe yana rintse ido. Sannan a hankali ya furzar da iska daga bakinsa. Ya buɗe idonsa sannan ya juyo ya kalleta. “Kin ga!...” Cak maganar da yake son fitarwa daga bakinsa ta tsaya a maƙoshinsa, saboda yanda Halima ta kalleshi da fararen idanuwanta dake zubar da ƙwalla. “Hasbunallahu wa ni'imal wakil!” Ya furta a iyaka kan leɓensa. Shi yanzu gaba ɗaya ma ya rasa me yake damunsa. Ko de yarinyar nan ta masa wani abin ne?... Sai ya girgiza kansa a fili yana haɗiye yawu. Ya yi gyaran murya, sannan ya ɗauke idonsa a kanta yana faɗin. “A... Abin da na miki jiya ban kyauta ba... Shi ya sa na dawo yau dan na baki haƙuri... Ki yi haƙuri!...” ‘Kuma dan Allah kar ki sake shigo min cikin tunanina...’ Ya ƙarashe sauran maganar a zuciyarsa. Dan ba ya jin ta isa ya faɗa mata cewar jiya tunaninta ya hana shi bacci. Halima ta ci gaba da kallonsa da fararen idanuwanta da har zuwa lokacin ba su daina zubar da ƙwalla ba. Mamakinta ɗaya, dalilin da ya sa yake bata haƙuri. Ya san cewa zai zo ya yi nadama zai mareta tun farko?. Sai ta ƙara turowa leɓenta na ƙasa gaba. Tana wani ƙif-ƙifta ido. Sannan ta shafa gefen fuskarta. “To me ya sa ma za ka mareni jiya?. Kuma ma fa ni ba da gangan na bigeka ba. Sai da na yi ƙoƙarin kauce maka, amma ka kai ka ƙi ka kauce. Har ka san na bigeka na zuba maka ruwa a jikin rigarka... Wallahi jiya har na yi bacci ina kuka. Gefen fuskata sai zugi yake min, har ji nake kamar ba a jikina yake ba!...” Mu'az ya yi shiru kawai yana kallon bakinta da take turowa gaba lokaci zuwa lokaci, da kuma yanda take maganar a shagwaɓe. Kafin ya kalli idonta da take kallon ƙasa da shi. Wato ita nan har damar yin ƙorafi ta samu, saboda kawai ya bata haƙuri?... “Kuka da ma ai ke gwanarsa ce... Tun da yanzu ma ga shi nan kina yi” Ya faɗi yana kallonta. Sai ta kalle shi ita ma. Sannan ta ɗauke kai tana ƙara tura baki gaba. “Yanzu kin haƙura?” Ya tambaya. Shi kansa tambayar na ba shi mamaki. Ita ma sai ta kuma kallonsa, sannan ta miƙe tsaye, hannunta riƙe da gorar ruwan da ya bata. “Na haƙura amma ban haƙura ba!” Ya ɗan ƙara girman idonsa cikin mamaki. Wai ta haƙura amma bata haƙura ba. “Me ya sa kika haƙura kuma at the same time ba ki haƙura ba?” Ta masa wani irin kallo da ya hautsina bugun zuciyarsa nan take. Sannan ta juya kanta tana kallon wani gefen... Sai tura baki take, kamar wadda aka wa dole kan sai ta yafe masa. “Na haƙura dai” Ta faɗa tana kallon gorar dake hannunta. Mu'az bai san sanda murmushi ya suɓuce daga kan leɓensa ba. Saboda shi haka kawai wannan abin da take yake burge shi. Yana jin ana cewa shagwaɓa, bai taɓa ganin mace me shagwaɓa ba sai yau... A hankali ya sunkuya ya sa hannunsa a cikin motarsa ta saitin inda ta fito. Ya ɗauki chocolate. Sannan ya miƙe ya miƙa mata. “Kina so?” Sai ta masa irin wannan kallon na ɗazu. Sannan ya kalli chocolat ɗin. “Ai ban sanka ba. Na sani ma ko kai ɗan yankan kai ne?” Murmushi ya sake yi yana ɗaga kansa sama kaɗan. Sannan ya sauƙe yana faɗin. “Ba ki ga ni soja ba ne?” Ta kalli wandon kakin sojojin dake jikinsa. Dan daga shi sai wata baƙar T-shirt da ya sa. Ta kalli fuskarsa, wadda yanayinta kaɗai, da kuma askin kansa zai sa ta gane cewa shi sojan ne, amma sai ta girgiza kai. “Ai akwai sojojin gona” “Ni ba ɗaya daga cikinsu ba ne” “Me cece shaidarka?” Ta tambaya tana kafe shi da ido. Ya kuma yin murmushi yana girgiza kansa, sanna ya sa hannunsa ya kamo nata da bata riƙe gorar ruwan da shi ba. Ya saka mata chocolat ɗin a ciki, kuma ba tare da ya saki hannun nata ba ya kalleta yana faɗin. “Ki daina jayyaya Leemat. Ba na son gardama na san kin yarda da ni, tun da har kika yarda kika sha ruwan da na baki. Dan haka ki karɓi wannan ma. Kyauta ce daga MJ zuwa Leemat! Sunana Mu'az... Wata ƙila hakan zai amfaneki wata rana” Tun da ya riƙo hannunta Halima ke kellon fuskarsa. Saboda ita ta kasa gane wannan wani kalar mutum ne. Haka kawai sai ya yi ta riƙe mata hannu ba da son ranta ba?. Saboda ƙarfin hali biyan ba shi da ɗan kishiya?. Kuma ita amfanin ne sunansa zai mata. Ai tun jiya take fatan kada Allah ya sa ta sake haɗuwa da shi, yanzun ma tsautsayi ne. Kuma tana fatan kada Allah ya sake nuna mata shi har ta koma gare shi. Hannunta dake kan nasa ta janye tana goge ƙwallar idonta. Sannan ba tare da tace masa komai ba ta juya ta nufi hanyar shiga cikin boutique ɗin. Sai da ta shige ciki sannan Mu'az ya yi dariya. Haka kawai halinta na saurin kuka da langwami da kuma shagwaɓa suka saka shi cikin nishaɗi. Motarsa ya shiga ya tayar ya bar boutique ɗin. Kuma har ya isa barrack bai daina dariyar abin da Halima ta yi masa ba. Cike da farin ciki Halima ta buɗe ledar chocolate ɗin da MJ ya bata. Saboda tun tana ƙarama Allah ya ɗora mata ƙaunar chocolate. Kuma iyayenta na sai mata chocolate ɗin sosai. Yanzu kuma da ruwa ya ƙarewa ɗan kada ta manta rabonta da shan chocolate ɗin. Bite na fako da ta yi sai da ya sa ta ji ta kamar a wata duniya. Saboda ta yi matuƙar kewar chocolate fiye da yanda za'a iya kwatantawa. Lokaci guda ta yi murmushi. Saboda ta tuna da yanda mahaifinta yake yawan kawo mata chocolate. “Allah ya ji ƙanka Daddy” Ta faɗa a fili. Tana tuna duk wani kyakkyawan abu da ya gabata a rayuwata. “Ke Halima! Zaman me kike a nan da ba za ki zo ki kama aiki ba?” Ta juyo muryar Boss ɗinsu a bayanta. Da sauri ta sauƙa daga kan kujerar da take. Tana zare ido kamar wadda ta yi wa sarki ƙarya. “Ki zo ki fara aikinki. Ga wasu can sun zo siyan kaya suna neman wanda zai taya su zaɓa!” Ta gyaɗa kai da sauri tana nufar hanyar wurin da Boss ɗin ya nuna mata. _________________ _Daɗina da gobe saurin zuwa😂_ _Salmanians!_ _Da alama Sir MJ dodon abinci ya haɗu da gamonsa_ _Share fi sabillilah❤️_ *Daga alƙalamin Salma Ahmad Isah✍️.* *CANDY CE🦋.* -------------------- _Kada a manta da biyan kuɗin littafi. Coz free pages sun kusa ƙarewa. To subscribe pay ₦300 to._ 5487270431 Salma Isah Monie point. And send the evidence of payment via. 08130172702 #Candy #SalmaAhmadIsah °°°°°°°°°°°°°°°°°° *ƘADDARA CE!* *©SALMA AHMAD ISAH.* *CANDY🦋* _ArewaBooks @SalmaAhmad_ _Wattpad @Salma_Ahmad_Isah_ *09* MUKTAR POV. Kamar yanda suka yi alƙawarin komawa bincike layin BB hotel

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});