Chapter 20
Chapter 20
saka kanka a cikin damuwa, zan ci gaba da bincike a kan wannan case ɗin har sai na kama me laifin nan!...” Faruk ya yi murmushi. “Na gode sosai Muktar. Allah ya saka da alkairi” “Kada ka damu. Da yardar Allah mun kusa kaiwa ƙarshen wannan binciken. Duk wani ci gaban da aka samu i will give you a touch!” “Na gode sosai. Sai da safe” “Okay sai da safe” Muktar ya aje wayar, sannan ya shafa kansa. Ya yi shiru yana nazari, bisa ga dukkan alamu wanna case ɗin ba ƙarami ba ne kamar yanda suke tunani. Dan haka yana buƙatar faɗaɗa tunaninsa domin kaiwa ƙarshensa. Daga haka ya miƙe tsaye, sannan ya shiga barthroom dan ya watsa ruwa a jikinsa. *No.53, off Justice Clara Ogunbiyi street, Asokoro, Abuja.* MIMA POV. Ita da wata cousin sisternsu ne zaune a falo suna gulmar Mu'az. Mima ta dage tana shararowa budurwar me suna Zulaihat labarin kalar cin abinci irin na Mu'az. “... Kin ga fa waccan layyar haka bawan Allahnan ya cinye rabin ragon da ya yanka tun a ranar farko!” Zulaihat ta zare ido cikin faɗin. “Rabin rago fa Mima? Ban da sharri dai!” Mima ta taɓe baki. “Wallahi da gaske nake. Kin san ai ba zan miki ƙarya ba. Kin san Anti Maryama ce ta zo ta tayamu suya waccan layyar. To in faɗa miki Ya Mu'az zuwa ya yi compound ya aje kujera, ya hau ya zauna yana aika Na'im ya je ya ɗebo masa idan an soya. Ana soyawa yana ci, kan ki ce me har naman ya faɗa. Haka Anti Maryama ta yi ta mamakin ƙarewar naman. Da aka tambayi Gogan ina nama sai yace ai shi ya cinye kayansa. Anti Maryama har da cewa an yakuwa Mu'az mutum ne?” Zulaihat ta kwashe da dariya Mima na tayata. “Wallahi. Ai wannan mutumin da kika ganshi kura ma haka ta ga ta ƙyale a kan cin nama. Ya Mu'az? Humm!” Bata kai ga rufe bakinta ba, Mu'az ɗin ya buɗe ƙofar falo ya shigo. Saurin gimtse bakinta ta yi. Ta shiga zara ido tana faɗin ta shiga uku a ranta. Dan ta ɗauka cewa ya ji abin da tace, idan kuwa har ya ji ai yau sai ɗan buzunta a gidan nan. Amma kuma sai ta ga ko kallonta bai yi ba har ya zauna a kan sofa. Hakan ya sa ta gane cewa bai ji abin da tace ba. Ajiyar zuciya ta yi, dan ta san da ace ya ji babu abin da zai hana ya lakaɗa mata na jaki. Saboda Mu'az bai iya kauda kai a kan laifi ba. Daga zarar an masa yake mayar da martani. Amma kuma ba shi da ruƙo. Dan daga zarar ka masa laifi ya amayar da abinda ka masa zai manta, mintuna kaɗan za ka ga ya dawo yana maka magana da kansa. Kuma da ma yawancin mutum mafaɗaci haka yake. A sace ta ci gaba da kallonsa. Har ta lura da kamar akwai abin da yake damunsa. Ta riga da ta san halin yayanta. Abu ne mawuyaci ya ganta zaune a falo bai mata magana ba. Ko da ko ita bata fara masa maganar ba, ko tsokanarta ne zai yi. “Ya Mu'az ina wuni” Zulaihat ta gaida shi. Sai ya juyo ya kallesu da mamaki. Dan shi a sanda ya shigo kwata-kwata tunaninsa bai ba shi cewar akwai wani ɗan adam a falon ba. Kuma ba komai ya ja hakan ba face wani halin damuwa da zuciyarsa ta shiga yau kaɗai. Gaba ɗaya tun bayan abin da ya faru a Ummul Banat boutique ya rasa nutsuwarsa. Zuciyarsa da gangar jikinsa na faɗa masa cewar ya aikata ba dai-dai ba. Amma kuma ƙwaƙwalwarsa ta kasa yarda da hakan. Gaba ɗaya shi ji yake cewar bai aikata ba dai-dai ba, tun farko wa yace ta buge shi, har ta zuba masa ruwa a jikinsa?. Sai dai kuma wani sashi na zuciyarsa na faɗa masa cewar ya aikata kuskuren marinta. Bai kamata ace tashin farko ya mareta ba, ya kamata ace sai da ya tambayi ba'asi tukkuna. Amma ya zai yi?. Zuciyarsa ce a kusa, abu kaɗan ke sawa ya harzuƙa, kuma shi daga ya fusata yake mayar da martani. Ture wannan tunanin dake damun kansa ya yi, sana ya amsa gaisuwar Zulaihat. “Lafiya Zulaihat... Ya gida?” “Gida lafiya” Ta amsa tana satar kallon idon Mima da har yanzu a tsorace take. Kuma ba ta ƙara razana ba sai da Mu'az ɗin ya kalleta. “Mima ina Mummy?” Ta haɗiyi yawu, sannan ta amsa masa da sauri. “Tana ɗakinta” “Me aka dafa yau?” Ya kuma tambaya. “Tuwo aka yi. Amma Mummy tasa na dafa maka jollof ɗin couscous” “Kin saka nama ko kifi?” Ta ɗan kalli Zulaihat, dariya na son kufce mata. Sannan ta kalle shi tana amsawa. “Eh. Na saka maka catfish” “Zuba min Please” “To” Ta faɗa tana miƙewa, sannan ta nufi kitchen. A lokacin Na'im ya sauƙo daga sama. Kuma yana sauƙowa ya yi kan Mu'az. “Ya Mu'az ka siyo min sweatern?” Na'im ya tambaya yana zaunawa kusa da shi. Maganar sweater ta tuno masa da yanda aka yi ya aje sweatern. Lokaci guda hoton ya taho haɗe da na fuskarta, da kuma na idanuwanta da ya fi kalla a fuskar tata. Maimakon yace wani abu sai ya dafe kansa yana faɗin. “Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!” Na'im ya taɓa shi. “Baka da lafiya ne Ya Mu'az?” Sai ya girgiza kansa yana ɗagowa da shi. Sannan ya ƙaƙalo murmushi. “Lafiyata ƙalau. Na manta da siyan sweatern ne. Amma gobe inshallah zan siyo maka!” Yana faɗin hakan ya miƙe tsaye, ya nufi hanyar fita daga falon. Mima da ta fito daga kitchen, hannunta riƙe da plate ɗin abincinsa tace. “Ya Mu'az ga abincin!” Sai ya juyo ya kalleta. Ba tare da ya ce komai ba ya nufeta, sannan ya karɓi plate ɗin. Ya juya ya fita daga part ɗin Mummy ba tare da yacewa kowa komai ba. Har ya fice su Mima ba su daina mamakin abin da ya hana shi sukuni ba. A falon part ɗinsa ya zauna, ya saka abincin da ya karɓa a wurin Mima a gaba yana kallo. Ya kasa ci, kuma ya rasa yanda zai yi da shi. Can kuma sai ya ja wani dogon tsaki. Haba mana. Ya za ayi wata yarinya ta shigo tunaninsa ta takurawa rayuwarsa, ta hana shi sukuni haka kawai dan ya mareta?. Mutum nawa ya mara a kan sun masa laifi?. Sai ita da aka ƙerata da gwal?. Za ta takurawa tunaninsa?. Idan har ta sake shigo masa tunani sai ya je har Ummul Banat boutique ɗin ya hukuntata. Da wannan maganar da zuciyarsa ta raɗa masa ya samu sukunin cin abinci. Har ya taso ya koma ɗaki. Ya cire rigar jikinsa ya kwanta a kan gado. Ya kashe wuta da niyyar yin bacci. Amma sai baccin yace ai ba su yi yarjejeniya da shi kan zai ɗauke shi a wannan lokacin ba. Tunaninta kuma ya ƙara dawo masa. Idanuwanta da suke ƙyallin ƙwallar da take zubarwa sun fi komai takura masa. Hannu ya kai ya ɗauki pillow ya danne kansa da shi, wai ko za ta fice masa a cikin tunani. Amma Wallahi ba ta fita ba.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31