Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 6

Chapter 6

Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel – Maimuna’s Painful Story 1,207 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Kasancewar ta san cewa su masu scikler ba'a raba su da jinya, ballantana kuma yanzu da ake cikin lokacin sanyi da cutar ta fi yawan tashi yasa tace. “Ƙafar ce ko bayanki ne yake ciwo?” “A'a. Ai yau da na tashi ban ji ciwon ƙafar ba. Auwwa ce ta ƙona ni jiya da dadare!” Ta ƙarashe tana nuna mata singalin hannunta na hagu da ya yi alamar ƙuna. Dan fatar wurin har ta tashi Cike da jin tausayinta Rahina ta kawar da kanta gefe tana kare fuska. “Subhannallahi. Wallahi Maimuna Auwwa muguwa ce” Maimuna ta sunkuyar da kanta tana gyara ledar dake kan murfin bokitinta. Sannan ta ɗaga kai ta kalli Rahina dake kallonta. “Bari na je” “Amma kar ki daɗe” Maimuna ta gyaɗa kai tana miƙewa. Kuma kai tsaye ta nufi bakin titi. Domin hawa napep, wadda za ta kaita Haɗejia general hospital. Duk da asibitin bata da nisa da unguwar Fantai. Da yake ta san sashin da Mummyn su Maryam take sai bata sha wahalar nemanta ba. Kai tsaye ta je ta sameta a inda suke zama. Kuma Mummy ita ta kaita aka ɗaye fatar ƙunan da ta tashi. Sannan aka saka mata magunguna. Kuma a pharmacy ɗin asibitin Mummy ta sai mata magungunan da aka rubuta mata, har ma da wanda ba'a rubuta ba. Wato magungunanta na cutar sickler. Kasancewar ta sanar mata cewar nata sun ƙare. Basu rabu da Mummy ba sai da ta sai mata dafaffen ƙwai. Dan ko ba'a faɗa ba ta san cewa Maimuna na buƙatar kayan ƙarin jini. To kuma sai ƘADDARA ta sa ta taso a gidan da abincin da za ta sa a cikinta ma gagararta yake. Ballantana ta samu wanda zai ƙara mata jini. Haka Maimuna ta yi ta mata godiya har suka rabu ta dawo makarantar Famfo goma. _Share fi sabillilah❤️_ _______________ _Ya kamata a fara biya tun daga yanzu fa!_ _If you want to subscribe pay ₦300 to._ 5487270431 Salma Isah Monie point *Daga alƙalamin Salma Ahmad Isah✍️.* *CANDY CE🦋.* °°°°°°°°°°°°°°°°°° *ƘADDARA CE!* *©SALMA AHMAD ISAH.* *CANDY🦋* _ArewaBooks @SalmaAhmad_ _Wattpad @Salma_Ahmad_Isah_ *03* *No.42, Inuwa Wada crescent, Utako, Abuja.* *12:55 na dare.* MARIYA POV. A dai-dai irin wannan lokacin da ya kasance duk wani abin hallita yake bacci domin samun hutu ita idonta biyu. Duk wani hankali da tunaninta ta tattara shi a kan agogon bangon dake manne a bangon ɗakinta. Burinta bai wuce ta ga ƙarfe sha biyu ta cika dai-dai ba. Ba dan komai ba sai dan ta tafi babban meeting ɗin ƙungiyarsu da za'a gabatar a yau da ƙarfe sha biyu na dare. Cike da ƙaguwa ta juya ta kalli Hilal dake kwance a kan bed ɗinta yana bacci. Ta ja tsaki tana ƙara maida idonta kan agogon. Ganin mintuna biyu ne suke rage sha biyun ta cika ya sa ta miƙe tsaye. Ta sunkuya ƙarƙashin gadonta ta janyo wani akwati dake aje a wurin. Zama ta yi a ƙasa, sannan ta buɗe akwatin, komai dake cikin akwatin ja ne. Kuma abubuwan dake cikin akwatin ba su wuce huɗu ba. Daga wata jar doguwar riga, sai 'yar ƙaramar ƙwarya da aka yiwa fentin ja. Sanna kuma a cikin ƙwaryar akwai wani jan ruwa me kauri. Daga gani daskararren jini ne. Sai reza dake ɗauke da busasshen jini a jiki, da kuma wasu zobunan ƙarfe har da sarƙoƙi. Hannu ta kai ta ɗauki rigar. Sannan ta miƙe tsaye, ta cire tufafin jikinta ta saka rigar. Har ƙasan ƙafafunta rigar ta sauƙa, kuma hannun rigar dogo ne sosai. Hannu ta kai ta cire ribbon ɗin da ta ɗaure gashin kanta da ba kitso. Ta barbaza shi a bayanta. Ta ɗauki zobina masu ɗauke da kan wata dabba mara fasali ta saka a yatsunta duka goma. Sannan ta saka sarƙoƙin dake cikin kayan. Ta ɗauki kwaryar dake ɗauke da daskararren jini ta riƙe a hannunta. Sannan ta juyawa gabar baya tana jiran cikar ƙarfe 12. A dai-dai lokacin da hannun agogon ɗakin ya kaɗa a kan ƙarfe sha biyu dai-da. Mariya ta rintse idonta da ƙarfi. Sannan pendant ɗin ɗaya daga cikin sarƙoƙin dake wuyanta ya kawo jan haske. A hankali cikin salihar muryarta ta furta. “Mhish!” A lokacin da fatar leɓenta ta sama ta haɗu da 'yar uwarta ta ƙasa wurin kaiwa karshen kalmar taɓace bat a cikin ɗakin. *RED SHAITAAN'S SAVERNTS PALACE.* Babban ɗakin taro ne. Wanda ya ƙunshi jerin kujeru sama da ɗari. Kuma duka kujerun suna kallon juna ne daga ko wani bango na ɗakin. Kamar dai jerin kujerun majallisar sarakunan gargajiya. Ko wace kujera a wurin ja ce, kuma kowacce tana ɗauke da sunan me ita. Daga can kan stage ɗin dake a tsakiyar ɗakin taron daga can ƙarshe kuma kujeru ne guda uku. Wadda ke tsakiya tafi kowacce kujera girma. Yayin da biyun da suke a gefe da gefenta kuma irinsu ɗaya. Amma kuma su ma sun fi sauran kujerun dake ɗakin girma. Daga tsakiyar ɗakin kuma wani katon rami ne dake ɗauke da itatuwan dake ci da wuta. Ga kuma wasu kayan tsaface tsaface da baka ce ga sunayensu ba. A hankali suffar Mariya sanye cikin jan kaya ta bayyana a tsakiyar ɗakin taron. Kuma sai da ta ji ƙafafunta sun sauƙa ƙasa, sannan ta buɗe idonta a hankali. Ƙafarta ta cira ta fara tafiya a hankali. Har ta isa kujerar dake ɗauke da sunanta a cikin ƙungiyar. Wato RAZOR!. Sai da ta zauna sannan ta aje ƙwaryar dake hannunta a kan wani teburi. A hankali a hankali mutane suka ci gaba da bayyana a cikin ɗakin. Kafin kace me har sun cika ɗakin. Duk yawan waɗannan kujerun sai da suka cika su taf. Mutane ne da ban-da ban, daga sassan duniya, wasu baƙaƙen fata ne, wasu kuma fararen fata ne. Kuma ko wa a cikinsu na sanye da jan kaya. Yayin da wasu daga cikin bayin shaiɗan na wurin ke aikin haɗa wutar dake ci a ɗakin taron. Bayan shuɗewar wani lokaci wata ƙofa dake kusa da babbar kujerar dake ɗakin taron ta buɗe. Sannan wani tsoho da ya tara farin gemu ya shigo sanye cikin jan kaya. Bayyanarsa a cikin ɗakin taron ya sa sauran bayin shaiɗan ɗin suka miƙe domin nuna girmamawarsu ga Shugaba!. Tsohon ya tsaya a jikin kujerarsa da tafi ta kowa kyau da girma a ɗakin taron, wadda ke nuna cewa ya fi kowa matsayi a wurin. Ya ɗaga hannayensa duka biyu sama, sannan ya haɗesu wuri guda alamun bauta da jinjina. “Jinjina zuwa ga bayin shaiɗan!” Duka ɗakin ya ɗauka da muryoyin mutanen cikinsa, masu banbancin jinsi, al'ada da yare. “Jinjina zuwa ga shugaban bayin shaiɗan!” Tsohon ya yi murmushi, sannan ya musu alama da su zauna. Kowa ya zauna, sannan shina ya zauna. Sai da ya juya ya kalli ɗaya daga cikin kujerun da suka saka tasa a tsakiya. Wadda wani ba'indiye ke zaune a kai, alamun dai shi ne na hannun hagunsa. Kafin ya juya ya kalli ɓangaren kujerar dake damansa, wadda babu kowa a kai. Sannan ya juya ya kalli sauran bayin shaiɗan ɗin da suka yi shiru suna jiran jin abin da ya sa aka tara su a wurin. “Kamar yanda muka saba gudanar da taron tattaunawa a ko wani mako. Yau ma haka ne. Sai dai ina so na

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});