Chapter 11
Chapter 11
harɗe hannayensa a ƙirji, yana daga tsaye a kan Mubarak ɗin da tsoro ya sauyawa kamanni. “Ni ma ban ce ka kasheta ba. Amma me ya kaika hotel ɗin a waccan ranar, da har ka tura mata saƙo ta wata lambar da ba taka ba?” Mubarak ya haɗiye miyau. Sanna yace. “Eh, na... Na tura mata da saƙo ne saboda ina so mu tattauna wata magana ni da ita!” “Amma me ya sa ka tura nata saƙo da baƙuwar lamba, saɓanin wadda ka saba amfani da ita!” A tsorace yace. “Sati biyu kafin lokacin aka sace min wayata a Almart farm. Kasancewar ba ni ne wanda ya yi rigistern waccan layin nawa ba ya sa na jinkirta yin welcome back. A maimakon na zauna haka sai na siyi wani sabo na fara amfani da shi!” “Me ya sa ka zaɓi haɗuwa da ita a hotel. Saɓanin gidansu ko wani wurin da ban” “Da... Dama... Da dama!” Suna haɗa ido da Muktar ya ji cikinsa ya saki ƙarar tsoro. Ganin yana kame-kame ya sa Muktar ya saki hannayensa. Sannan ya ɗora su a kan table ɗin dake wurin. “Zai fi maka kyau ka sanar da ni komai. Tun kafin nasa a kaika ɗakin horo. Dan wallahi ka ji na rantse idan ka je can ba za ka fito da kammaninka na asali ba!” A take Mubarak ya soma hawaye, ya haɗiye miyau ya fi sau ƙirgen yatsunsa. Ganin babu sarki sai Allah ya sa ya buɗe baki ya faɗi gaskiya. “Ƙwarai. Na kirata hotel ne saboda ina so mu sasanta wata matsala da ta shiga tsakanina da ita. Bayan ta zo sai na nemi da ta bani kanta. Hakan ya sa muka yi wani sabon faɗan da ita. Har ta bar hotel ɗin ranta a ɓace yake. Amma daga wannan ban san komai ba yallaɓai...” Ya kai ƙarshe yana fashewa da kuka me sauti. * “Duk abubuwan da ya faɗa gaskiya ne. Saboda na sa an yi bincike a Almart farm, inda yace an sace masa wayar, kuma masu gadin wurin sun tabbatar da hakan. Dan sun ce a lokacin da aka rasa wayar su ya fara sanarwa... Shi ya sa tun farko ni ban yi zarginsa da kashe Munira ba. Tun bayan sanda muka gano cewa shi ne wanda ya aiko mata da saƙo kan ta zo ta same shi a hotel ɗin!” Muktar ya korowa Faruk dake jiransa a office tun ɗazu bayanin, bayan da ya baro ɗakin tuhuma. Faruk ya sauƙe numfashi. Yana jin ko ina na duniyarsa na ƙara cika da hargitsi. A gida Mariya da matsalolinta, a waje kuma damuwar mutuwar Munira. “So yanzu me nene mataki na gaba?” Muktar ya sauƙe numfashi, sannan ya ɗora hannayensa a kan table ɗin da ya raba tsakiyarsu da Faruk ɗin. “Duk wani CCTV camera footage na hotel ɗin an goge shi. Hakan ke nuna cewa wanda ya aikata kisan ya iya takunsa. Amma kuma duk da haka ya tafka wani kuskure da zai iya sawa mu kama shi cikin sauƙi!” Cike da zaƙuwa Faruk yace. “Wani kuskure ya aikata?” “Duk yanda mai laifi zai yi wurin binne laifinsa a ƙarƙarshin ƙasa yana kuskurewa ta wata hanyar. To haka shi ma wannan ya kuskure. Domin akwai ɗaya daga cikin masu aiki a hotel ɗin da muka tambaya, ta sanar mana da cewa ta ga sanda Munira ta fito daga ɗakin da Mubarak ya kama. Amma kuma kafin ta kai ga sauƙa ƙasa ta tsaya a ƙofar ɗaki me lamba 24. Sannan ita matar tana zargin cewa akwai abin da Munira ta ga a ɗaki me lamba 24, wanda zai iya zama sanadiyyar mutuwarta!” Girar Faruk na tattarewa wuri guda ya furta. “Ban gane ba Muktar!” Muktar ya jinjina kansa. “A ranar da Munira suka haɗu da Mubarak aka kashe wani ba'indiye a cikin hotel ɗin, me sunan Danesh Kumar. Danesh Kumar shi ne mutumin da ya kama ɗaki me lamba 24. Idan har za ka iya zurfafa tunaninka. Za ka iya gane alaƙar zance na da kuma mutuwar Danesh!” Faruk ya yi shiru. Can kuma yace. “Idan na fahimta dai-dai, wata ƙila a sanda Munira ta baro ɗakin da Mubarak ya kama ta ga sanda aka kashe Danesh, ko kuma ta ga masu kisan, ko kuma ta ma san wanda ya yi kisan, shi ya sa ita ma aka bita aka kasheta!” “Wanna shi ne abin da bake so ka gane” “Amma abin tambayar a nan shi ne. Me ya sa makashin ko makasan ba su kasheta a nan cikin hotel ɗin ba, sai da suka bari ta fita, sannan kuma suka bita suka saceta. Sai kuma kirana da ta yi a waccan ranar, kafin su saceta!” “Idan za ka iya tunawa tun farko na sanar maka da cewa masu gadin hotel ɗin sun sanar mana da cewa Munira ta bar hotel ɗin. Kuma a ƙafa, saɓanin sanda ta shigo wurin da mota, ka ga wannan ma zai ƙara tabbatar mana da cewa lallai akwai abin da ta gani. Shi ya sa ta ruɗe har ta manta da motarta da ta je wurin da ita. Kuma wata ƙila makashin yana ganin idan har ya kasheta a hotel ɗin asirinsa zai iya tonuwa. Shi ya sa ya zaɓi ya barta ta fita daga hotel ɗin, domin ya kauda tunanin jami'an tsaro kan alaƙar kisan Danesh da na Munira. Kuma ya zaɓi sace ma duk akan wannan dalilin. Batun kiranka kuma zai iya kasancewa ta gane makashin na bibiyarta, shi ya sa ta kiraka dan neman taimako!... Amma duk da haka akwai lauje cikin naɗi! Sai dai na maka alƙawarin gano shi nan ba da jimawa ba abokina!” Faruk ya sa hannayensa duk biyu ya shafa fuskarsa zuwa ƙeyarsa. Ya furzar da iska yana jin kansa na ƙara dulmiyewa cikin kogin matsaloli. “Yanzu abin da za mu yi nagaba shi ne gano ainahin inda aka saceta. Kuma za mu iya gane hakan ta hanyar wayarta. Dan a lokacin da ta kiraka aka saceta!” Faruk ya gyaɗa kansa. Kafin ya miƙe ya bawa Muktar hannu suka gaisa, haka ya bar headquartern da nauyin zuciya, ya nufi barrack. MU'AZ POV. “Shigo!” Ya bada umarnin bayan da aka ƙwanƙwasa ƙofar office ɗinsa. Kansa ya ɗaga ya kalli me shigowar. “Sir!” Sojan da ya shigo ya faɗi yana sara masa da hannunsa na hagu. Mu'az ya aje pen ɗin dake riƙe a hannunsa yana kallonsa. “Dismiss!” Sojan ya sauƙe hannunsa. “Barka da safiya sir” “Barka. Eze me ya sa jiya baka je duty ba?” Ya tambaya yana shafa fatar bakinsa. Sargent Chiku Eze ya washe baki, sannan ya yi taku biyu zuwa jikin table ɗin Mu'az, ya aje masa containerr da ya shigo da ita. Mu'az ya kalli containerr, sannan ya kalli Eze. Da ido ya masa alama da wannan fa?. Eze ya sosa ƙeya yana faɗin. “Eh Sir. Grilled fish and potato ne matana ya girka maka!” Mu'az ya yi murmushi. Wai shi za'a bawa cin hanci da abinci. Sai ya sauƙe hannunsa a kan bakinsa, sannan ya kai hannu ya buɗe containern. Ba tare da tunanin komai ba ya fara cin abincin. Yau abinci ne fa, ai ba yaƙi ci ba. “Oh lord of mercy! Matarka ta iya girki Eze!” Ya faɗi yana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31