Chapter 21
Chapter 21
Daga ƙarshe ma sai ya miƙe zaune a kan gadon, sannan ya dafe kansa yana faɗin. “Ya isa Mu'az. Ya isa!” Ya faɗawa kansa yana shafa saitin zuciyarsa. Sannan ya ƙara da. “Babu abin da ya haɗa hanyarka da ta waccan yarinyar. But she's innocent!...” Wani zancen ya shigo cikin wani. Sai ya rintse idonsa yana furta. “Oh lord of mercy. Na shiga uku ni Mu'azzam!” Ya buɗe idonsa. Sannan ya sauƙa daga kan gadon. Ya shiga bayi, ya yi wani sabon wankan, wai ko zai samu yarinyar ta fita daga kansa. Ko da ya dawo ɗakin ya kwanta ba ta sauya zani ba. Daga ƙarshe sai ya miƙe ya zauna a tsakiyar gadon ya shiga yin salatin annabi. Wata ƙila Allah ya dube shi ya kawo masa ɗauki. A ranar bai yi bacci ba sai da ya sa a ransa cewar zai je ya bata haƙuri, kuma ya amin ce cewar ya aikata mata ba dai-dai ba. Zuciyarsa ma sai da ta raya masa cewa wata ƙila ma mayya ce. Shi ya sa ta hana shi baccin dare. Amma dai ko ma aljana ce zai je ya bata haƙuri, in ya so ta ci kanta ta sha baƙin ruwa. °°° °°° °°° _Humm Humm Humm_ _Garin daɗin kowa ya kama da wuta. In ji Malam Tsalha mijin me Koko.😂._ _Da alama Halima da Kairat sun yi addu'a a bakin 'yan amin._ _Sir MJ dodon abinci ya kasa sukuni saboda kuskuren da ya aikata mata_ _Wai ni ina Maimuna ne?_ _To a yi dai mu gani_ _Share fi sabillilah❤️_ *Daga alƙalamin Salma Ahmad Isah✍️.* *CANDY CE🦋.* -------------------- _Kada a manta da biyan kuɗin littafi. Free pages sun kusa ƙarewa. To subscribe pay ₦300 to._ 5487270431 Salma Isah Monie point. And send the evidence of payment via. 08130172702 #Candy #SalmaAhmadIsah °°°°°°°°°°°°°°°°°° *ƘADDARA CE!* *©SALMA AHMAD ISAH.* *CANDY🦋* _ArewaBooks @SalmaAhmad_ _Wattpad @Salma_Ahmad_Isah_ *08* *Unguwar Fanisau, Haɗejia local government, Jigawa state.* “Maryam! Maryam! Maryam ke!” Mummy dake cikin kitchen ta ƙwalawa Maryam dake zaune da Maimuna a falo kira. “Na'am Mummy” Maryam ta amsa tana nufar kitchen ɗin. Ta tsaya a ƙofar kitchen ɗin, sannan ta leƙa kanta ciki. “Mummy ga ni” “Tsabar iskanci kina ji ana kirana amma ba za ki iya kawo min wayar ba?” Maryam ta ɗan yi dariya irin ta marasa gaskiya ta na sosa kai. “Yanzu za ki je ki ɗauko min wayar ne? Ko tsayuwa za ki ci gaba da yi a nan har Mahadi ya bayyana?” Da sauri Maryam ta dawo falo, inda Maimuna ke zaune tana cin abinci. Ta ɗauki wayar Mummu dake chargy. Sannan ta kai mata wayar ta dawo ta zauna a wurin Maimuna. Ganin mahaifiyarta ce mai kiran ya sa Mummy ta bi bayan kiran. Bugu uku Hajiya ta ɗauki wayar da sallama. “Hajiya Ina wuni?” Mummy ta gaisheta cike da girmamawa. “Lafiya ƙalau Bara'atu!. Ya gida ya yaran?” “Lafiyarsu ƙalau. Alhamdullilah. Ya wurin su Faruk da matarsa, Dan Adam mun yi waya da shi ɗazu” “Faruk lafiya, amma ba lau ba Bara'atu!” Jin hakan ya sa girar Mummy tatarewa wuri guda. Sannan tace. “Me ya faru da shi?” Hajiya ta girgiza kai. “Matsalar Mariya ce ba komai ba. Duk da dai shi da kansa bai furta min hakan ba. Amma kuma ni na gane hakan tun ba yau ba!” Mummy ta girgiza kanta. “To ya za ayi Hajiya?. Tun da shi ba zai iya faɗar matsalarsa ba ballantana a ba shi shawara sai a taya shi da addu'a!” Hajiya ta sauƙe numfashi. “To... Haka ne... Allah ya dai-daita tsakani...” Daga gaka suka ɗan taba hira, kafin suka yi sallama. Ko da Mummy ta gama abin da take a kitchen ɗin sai ta fito. Inda ta samu Maimuna da Maryam zaune a falo. “Maimuna ya kamata ki tafi gida. Na ga lokaci ya ƙure. Kar Auwwa ta dakeki!” Maimuna ta miƙe tsaye tana faɗin. “To Mummy, bari na tafi!” “Ga shi kuma yau Sadiq ba ya gari. Ballantana su raka ki shi da Maryam” Maimuna ta girgiza kai tana faɗin. “Ai ba komai Mummy. Zan iya tafiya Ni kaɗai” Mummy ta jinjina kai. “To mu kwana lafiya” “Allah ya tashemu da alkairi” “Amin” Maimuna ta yi wa Maryam sallama, sannan ta fita. Tana tafiya a hanya tana tuna dalilin fitarta cikin wanna daren, kuma ba komai ya ja hakan ba face abinci da Auwwa ta hanata kamar yanda ta saba a wasu lokutan. Dan wani lokacin idan 'yan imanin na kusa ba ta hanata. “Assalamu alaikum” Ta yi sallama daga soron gidan. Sannan ta shiga. Gabanta ne ya soma faɗuwa tun da ta yi arba da Auwwa tsaye a tsakar gidan. Ta ƙame a gu ɗaya. Hannunta kan ƙugu tana jijjiga kamar me shirin hawa bori. Tun da ta ga haka ta san cewa yau kam ta banu. “Daga gidan ub*n wa kike?” Auwwa ta tambaya. Maimuna ta haɗiye yawu jikinta na rawa. Sannan tace. “Gi... Gi... Gidan su... Maryam na je!” “Saboda ke gaki kwaɗayayyiya ko?... Su kuma ga su dangin waliyyai, masu zuciyar tausayi?... Shi ne kika ɗauki ƙafa kika tafi gidan...” Ta dakata tana cafkowa hannunta. A take Maimuna ta fashe da kuka. Sannan ta soma roƙon Auwwa. “Dan Allah Auwwa ki yi haƙuri! Dan Allah! Dan Allah!..” Auwwa ta ɗaga ɗayan hannunta da bata riƙeta da shi ba, ta doke mata baki har sai da jini ya fara fita daga bakin nata. Maimuna ta fashe da wani sabon kuka, a sanda ta ga Auwwa ta nufi gindin murhu da ita. A gaban murhun ta durƙusar da ita, sannan ta sa wani cokali a cikin murgun, ta ɗaiko garwashi, ta ɗora a kan hannun Maimuna. Haka Maimun ta yi ta ƙwalla ƙarar azaba tana kuka tana roƙon Auwwa. Amma ko a jikinta. Ga shi su ba maƙota garesu ba bare a ji a kawo mata agaji. “Shegiya matsiyaciya. Allah ya sa gobe ma idan na hukunta ki da abinci ki sake zuwa can ki ci!” Maimuna ta ƙarawa kukanta sauti. Sannan ta durƙushe a wurin tana kuka me ban tausayi. Haka Auwwa ta miƙe tsaye ta tsallaketa ta wuce ɗakinta. Maimuna ta ci kukanta ta godewa Allah. Da ƙyar ta iya tashi ta shiga ɗakinta da babu bulb. Da akwai, amma kwana nan Auwwa ta cire shi, wai za'a bawa Gambo. Saboda ɗakin da yake kwana nasu ya mutu. Haka ta zauna a cikin sauron da take iya jin kukansu a kunnenta. Da ƙyar ta janyo ledar magungunan da Mummy ta sai mata. Ta sha tana hawaye har zuwa lokacin. Saboda wannan ƙunan da Auwwa ta mata a yau ya fi na ko yaushe. Da ƙyar ta lallaɓa ta shiga net ɗin. Tana jin yanda ƙashin bayanta yake amsawa. Saboda a kullum rana idan ta zo kwanciya sai bayanta ya amsa. Shi ya sa bata kwanciya kai tsaye, sai a daddafe. Zaninta ta ja ta lulluɓe jikinta. Duk da yanzu sanyin ya fara ja baya, ba kamar na kwanakin baya ba. Amma da ma ita ko da sanyi ko babu sicklernta tashi take a ko wani lokaci. Har ɓarawo ya saceta ba ta daina zubar da hawaye ba. HALIMA POV. Kamar kullum, yau ma haka suka tashi a gidan babu ruwa ko na yin sallah ballantana na yin wanka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31