Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 29

Chapter 29

Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel – Maimuna’s Painful Story 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

shi sojan haya. Suka ɗebo wasu fasinjoji mutum biyu. Gambo ya juya ya kalli ogansa yana faɗin. “Oga ba na jin Auwwa za ta iya bada kuɗin nan... Ba ka san Auwwa ba ne, masifar son kuɗi gareta kamar me?” Ogan ya yi murmushi. “To ai shikenan. Sai ka yi ta zama a haka, kana hawa napep ɗin sojan haya. Ka je ka sha baƙar wahala, ka dawo a ɗauki kuɗin da bai taka kara ya karya ba a baka a matsayin sallama!” Gambo ya mayar da hankalinsa kan tuƙinsa. Yana nazarin maganar ogansa. A ƙalla yanzu an kai kusan shekaru biyu kenan da yake ta ƙoƙarin siyan napep tasa ta kansa. Amma babu hali, saboda yanda Auwwa ta kasa ta tsare a kan kuɗinta. “Me napep a Gagulmari fa za ka sauƙe mu!” Ɗaya daga cikin fasinjojin ta faɗa. Hakan ya sa ya ɗan juyo ya kalleta, sannan ya amsa. “To Hajiya” Ya faɗa yana juya kan napep ɗin. Dan harsun ɗan gota unguwar Gagulmarin. A kan titin ƙofar Arewa ya sauƙe su. Suka biyasu kuɗinsu, sannan suka juya kan napep ɗin zuwa ƙofar fada. Haka suka ci gaba da hira shi da ogansa. A kan mallakar napep ɗin da ya kamata ace ya yi, yana magana yana ɗauke kai daga kan tuƙin da yake. A haka har ya buge wata yarinya dake shirin tsallaka titin ƙofar fada ba tare da ya lura ba. Duk da ya tsorata bai sai ya kasa guduwa ba, amma kuma cikin rashin sa'a sai jama'ar dake wurin suka yi caraf suka kamasu su biyu... HALIMA POV. Hannu ta kai ta ɗauki jakarta. Ta rataya a kafaɗarta, saboda lokacin tashinsu aiki ya yi. “Kairat sai gobe” Ta yi wa ƙawarta sallama tana ɗaga mata hannu. Ita ma Kairat ɗin hannu ta ɗaga mata. Tana shirin wucewa, hirar da cashier da wata ma'aikaciya suke yi ta ɗauki hankalinta. Hakan ya sa ta tsaya tana sauraronsu. “... Wallahi dai kam haka na ji manager ya faɗa. Wai za ayi ragin ma'aikata!” Lokaci guda ta ji gabanta ya faɗi. Dan haka kawai zuciyarta ta raya mata cewar ita ma tana cikin waɗan da za'a sallama. Ita kuwa idan aka sallameta ina za ta je ta samu wani aikin?. Wannan ɗin ma da ya aka same shi?. Ballantana kuma ace ta rasa shi... Gabanta bai tsananta faɗuwa ba sai da ta ji cashier na faɗin. “Kuma a yanda Amina ke faɗa min wai waɗan da suka zo a ƙarshe-ƙarshen nan za a kora!” Ido ta zaro tana faɗin ‘Inna lillahi wa inna ialaihi raji'un’ a cikin zuciyarta. Sai ta kasa motsawa daga wurin da take. Ta ci gaba da baza ido har ta yi wani kyakkyawan gani. Saboda a sanda idonta ya lula zuwa ƙofar shigowa ta ga sanda Mr. JJ ya shigo boutique ɗin. Gabanta ne ya sake faɗuwa. Musamman da ta tuna rabuwarsu ta jiya. Hannunta na dama da ya riƙe ta kalla, tana jin kamar har yanzu hannayensa na kan wurin... Sai ta yi saurin goge ƙwallar da ta zubo mata, sannan ta nufi hanyar fita a sace, wai duk dan kada ya ganta. MU'AZ POV. Tun da ya shigo boutique ɗin yake ta dube-dube ko zai ganta. Amma har ya ɗauki sweatern da ya zo dominta bai samu ganin nata ba. Har ya fara jin ba daɗi na rashin ganinta, saboda ya fara tunanin ko dai ta tafi gida ne. Yana shirin nufar wurin cashier ya ci karo da ita tana tafiya a sukwane. Tana ganinsa ta taka birki tana ɓata fuska. Lokaci guda kuma ta juya za ta gudu. Sai dai kamar jiya, haka yau ma ya riƙo hannunta. Kuma kamar dai jiyan, yau ma sai da ta ji kamar ta yi hauka da ya riƙo mata hannu. Da ƙyar ta juyo suka haɗa ido. Sai kuma ta shiga bin kayan jikinsa da kallo. Kamar dai yanda ta saba ganinsa ne, sanye da baƙar T-shirt, da kuma wandon kakin sojoji, sai wani baƙin boot irin nasu na sojiji. Kuma yau ma kansa ba hula. Sai sweater guda biyu da yake riƙe da su. Ta sake kallon fuskarsa tana zare hannunta daga cikin nasa. “To wai mi ye?” Ta tambaya tana turo baki gaba. Mu'az ya yi murmushi kawai yana kallon wannan fuskar. “Kaya na siya a boutique ɗinku. Kuma ke nake so ki kai min mota!” Sai ta ƙara turo baki gaba. Hawaye ko tun da ya ruƙota ta fara zubar da su. “Ni lokacin tashi na ya yi” “Okay. Bari in je na faɗawa oganku...” Ya yi maganar yana shirin nufar office ɗin manager. Duk dan ya tsoratata, kuma ta tsorata ɗin, dan taku biyu kawai ya yi, ta yi saurin riƙo hannunsa ta dawo da shi baya. Ta ci gaba da ɓata fuska tana faɗin. “To ai ba sai ka je ba... Ka je ka biya, zan kai maka motar” Ta ƙarashe tana ɗauke kai gefe. Bai sake ce mata komai ba, ya yi murmushi ya je ya biya kuɗin, sannan ya dawo ya sameta tsaye a inda ya barta, ya danƙa mata shopping bag ɗin da aka saka masa sweatern a ciki. Sannan ya yi gaba ya barta a nan. Halima ta ɗaga jakar da ba wani nauyi gareta ba. Tsabar isa da gadara da take cin ransa, shi ya sa zai sa marainiyar Allah ta ɗaukar masa. Ta ƙarashe tana jan tsaki a ranta. Sannan ta bi bayansa tana kumbure-kumbere, kamar kwaɗon da ya ke shirin yin kuka. Kasancewar ta san motar tasa ya da kai tsaye ta nufi inda motar take. Ganin ƙofar driver seat a buɗe yabsa ta nufi wurin. Zaune ta gan shi a cikin motar. Amma kuma ƙafafunsa na wajen motar. A gefe ta tsaya, sannan ta miƙa masa jakar. “Ga shi” Ta faɗi kamar me shirin fashewa da kuka. Mu'az da tun da ta fito yake binta da kallo ya sa hannu ya karɓi jakar. Tana shirin juyawa yace. “Ba ki ji ba” Cike da ƙosawa Halima ta juyo, ta buga ƙafarta a ƙasa. “Dan Allah ka ƙyaleni ranka ya daɗe. An tashi aiki, kuma gida nake son zuwa” Sai kuma ta kai hannu ta share ƙwallar da ta zubo mata. Ta juya masa baya, ta turo baki gaba tana harɗe hannunta a ƙirji. Mu'az ya yi murmushi. Sannan ya fito daga motar, hannunsa riƙe da bag ɗin da Na'im ya saka masa chocolate da cookies a ciki. Ya zagaya ta gabanta, ya jingina a jikin motar yana ƙarewa fuskarta kallo. “Tambayarki zan yi” Ta masa irin wannan kallon da yake sawa ya ji kamar ya tsaga ƙirjinsa biyu, ya ciro zuciyarsa ya yar ya huta, saboda yanda bugunta yake hargitsewa. “Ina ji” Ta faɗa tana sauƙewa hannunta da ta rungume. Sannan ta goge hawayenta. “Me nene sunanki?” Sai ta dube shi. “Ai ka sani” Ya jinjina kai. “Na san sunanki Halima. Cikakken sunanki nake nufi” Sai ta ja hanci tana juya kanta gefe. “Halima Auwal Ali Kaska” Ya yi murmushi. Sannan ya ɗauki chocolate ɗaya ya miƙa mata. Ta kalli chocolate ɗin. Sannan ta kalle shi. “Ki karɓa” Ta kai hannu ta karɓa, a sanda wata tambayar take biyowa baya. “Ina ce unguwarku?” Yanzu ma sai da ta masa kallon tsanaki. Sannan ta

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});