Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 30

Chapter 30

Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel – Maimuna’s Painful Story 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

amsa. “Da a Life Camp muke ni da iyayena. Bayan Allah ya musu rasuwa kuma sai na dawo wurin kawuna a Bwari!” Ya kuma jinjina kansa. Sannan ya bata wata chocolate ɗin. Ita ma ta karɓa tana kallonsa kawai. “A halin yanzu kina karatu?” Mu'az ya sake tambaya. Saboda yana so ya san wani abu da ya shafi rayuwarta, ƙila shi ne zai nuna masa hanyar da zai bi domin gano abin da idanuwanta ke faɗa masa a duk sanda nasa idon zai haɗu da nata. “Shekaru biyu da suka wuce na kammala FCT College of Nursing Sciences, Gwagwalada. Kuma a shekarar ne Allah ya yi wa iyayena rasuwa” Ya kuma bata wata chocolate ɗin. “Me ya sa malamar asibiti take aiki a boutique?” Yanzu kuma sai ta kasa amsa masa. Ta yi shiru tana kallonsa. “Na gaji da amsa tambayoyin da ban san dalilinsu ba. Sai an jima” Ta ƙarashe tana shirin raɓa shi ta wuce. Amma sai ya riƙo damtsen hannunta a wannan karon, ya dawo da ita. Mamaki zane a kan fuskar Halima take kallonsa. Wai shi me yake damunsa ne?. Haka kawai sai ya yi ta riƙeta?. Shi bai san me take ji ba a duk sanda zai riƙeta?. “Gida zan tafi” Ta faɗa tana turo baki. “Mu je na kaiki” Yanzu ma kallonsa ta sake yi. “Ni ban sanka ba fa Malam JJ Ɗan Iya!” Sunan da ta kira shi da shi ya sa ya yi dariya kaɗan. “Ni kuma na sanki. Ki shiga mu je na kaiki” Ta noƙe kafaɗa alamun ba za ta shiga ba. Lokaci guda Mu'az ya haɗe fuska. “Get in, Idan ba haka ba zan mareki!. I'm running out of patience!. ” Lokaci guda cikinta ya murɗa. Saboda ta tuna yanda ya mareta last time. Dan haka ta yi saurin ja da baya za ta sa kuka. “Leemat ba na son gardama. With due respect. Get into the car” Ta turo baki. Sannan ta buga ƙafa a ƙasa. Ta juya ta zagaya ɗayan ɓangaren, ta shiga gidan gaba tana hawaye. Shi ma motar ya shiga. Sannan ya miƙa mata jakar chocolate ɗin hannunsa. Ta ɗauka tana ta ɓata rai. Wanda suke hannunta ma a ciki ta sa. Ta kame kanta gefe, ta ƙi yin magana sai hawayen da take. Shi ma bai takura da sai ta yi maganar ba. Har sai da suka iso Bawri. Sannan ya tambayeta layin gidansu a Dutsen Alhaji. Sai a sannan ne ta yi magana. Kuma suna isa ƙofar gidan ta shiga ƙoƙarin buɗewa ta fita. “Baby girl!” Cak ta tsaya daga shirin fitar da take. Saboda wani abu da ya faɗo a cikin kanta. A gaba ɗayan rayuwarta mahaifiyarta ce kaɗai ke kiranta da sunan. Hakan ya sa ta juyo ta kalle shi. “Kukan na mi ye?” Ta kai hannu ta goge ƙwalla tana ci gaba da tura baki. “Ba kai ne ka min tsawa ba” Kansa ya girgiza. “Gardama kika yi. And i hate stubbornness. Amma ki yi haƙuri” Ta ci gaba da tura baki tana kumbura shi. “Ki haƙura da wuri, saboda kar ki sake shigo min ciki tunani ki fitineni” Ta kuma kallonsa. “To na haƙura. Kuma na gode” Tana kaiwa nan ta fice daga motar. Zuciyarta cike taf da farin cikin wannan kyauta da ya mata ta chocolate da cookies. Saboda abu ne da ta daɗe ba ta sa a ido ba, ballantana har ta kai ga sha. A ɗaya ɓangaren kuma tana cike da fargabar batun rage ma'aikata da za ayi a boutique ɗinsu. Shi ma wannan batu ya hana zuciyarta sukuni. Har ta shige gidan Mu'az na kallonta yana murmushi. “Rigima Baby girl” Ya faɗa yana shafa gajerar sumar kansa. Yana shirin tayar da motar kiran Faruk ya shigo wayarsa. Hakan ya sa ya fasa ya ɗaga wayar. “Kaigama what's up?” Daga ɗayan bangaren Faruk yace. “Yanzu Muktar ya kirani. Ya sanar min da cewa yana son ganinmu ni da kai da gaggawa!” Mu'az ya ɗan sosa kan hancinsa yana duba agogo. “Okay a ina zan sameka?” “Ina gida. Ka zo ka ɗaukeni sai mu wuce headquartern” “Okay” Daga haka ya sauƙe wayar. Sannan ya tayar da motar ya nufi gidan Faruk. MUKTAR POV. Zaune yake cikin office ɗinsa. Yayin da Faruk da Mu'az ke zaune a kan kujerun dake gaban teburinsa. Tun da suka zo headuatern, suka ritsa shi da tambayoyi na me ya same shi. Saboda ganin raunukan da suke a jikinsa. Hannunsa na hagu da yake da tabbacin ya karye ya kuwa karye ɗin. Dan yanzu haka sai da aka yi wa hannun ɗori a asibiti. Ban da sauran wuraren da suka raunatu a jikinsa. Saboda jiya har ƙarfe sha biyu suna asibiti shi da Walid da Ali. Kuma duk da yanda likitocin suka so ya zauna a asibitin ƙi ya yi. Saboda ba ya jin zai bar abin da ya faru ya tafi a banza. Dole ne ya ɗauki matakin gaggawa, a yanzu sun kuskure wurin halaka shi, wata ƙila nan gaba Allah zai iya basu nasara. Ba mutuwarsa ce abar tsoro a wurinsa ba. Ya san cewa ko wani mai rai ƙarshen rayuwarsa a duniya mutuwar ce. Kamar dai yanda mahaifinsa ya rasu ya bar su shi da ƙaninsa da kuma mahaifiyarsu. Abin da zai fi ƙona masa rai shi ne da zai mutu ya bar Mariya da abokin aikata kisanta a raye, suna cutar Faruk da kuma sauran al'umma... “Mukhy!” Mu'az ya kirashi da ɗan ƙarfi, ganin kamar tunaninsa ya yi nisa da gangar jikinsa. Hakan ya sa ya dube shi da sauri yana amsawa. “Na'am!” “Ina ka tafi?” Mu'az ya tambaya yana watsa hannu a iska. Muktar ya girgiza kansa yana ɗora hannunsa a kan table ɗin dake gabansu. Ya furzar da huci kaɗan. Sannan ya dubi Faruk, ya dawo ya dubi Mu'az. “Kaigama!” Faruk ya gyara zama yana faɗin. “Na'am Mukhy!” Muktar ya kalli Mu'az. “MJ!” “Umm!” Shi ma ya amsa. Muktar ya jinjina kansa. Yana son sanin ta inda zai fara musu bayani a kan wata makusanciyarsu ita ce me laifin da suka daɗe suna nema ruwa a jallo. “Kaigama! MJ!. Ba na so na zama mutum na farko da zaisanar da ku wannan mummunan labarin!... Dan haka zai fi kyau ku kalla da idonku, kafin bayanina ya biyo baya!...” Su dai kallonsa kawai suke da rashin fahimta. Kuma duk sun ƙagu ya faɗa musu dalilinsa na yin kiransu. Ba su ce komai ba har ya juyo musu screen ɗin laptop ɗin dake kan teburin. Sannan ya naɗe hannunsa yana kallon fuskokinsu. A lokacin da videon ya kai ƙarshe. Ba a ce a tsakanin Faruk da Mu'az wa ya fi wani shiga shock ba. Kallon juna kawai suka yi baki a sake. Kafin Mu'az ya yi ƙarfin halin kai hannunsa ya sake kunnawa. Tunaninsa, zuciyarsa, da duk wani abu me faɗa a ji a jikinsa na faɗin wannan ba ƙanwarsa ba ce. Wannan ba Mariya ba ce. Wannan ba ƙanwarsa da ta fi kowa acikin ƙannensa soyiwa a ransa ba ce. Sam ba ita ba ce!... Ya ma za ayi ta kasance Mariya Jibrin Gimba?. Shi dai Faruk ba irin wannan tunanin yake ba. A kallo ɗaya da ya yi wa videon ya gane matarsa. Saboda ya santa, ya

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});