Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 14

Chapter 14

Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel – Maimuna’s Painful Story 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

gani. Amma she looks perfect. Murmushi ya yi yana binta da kallo har ta shiga cikin motar. Har ga Allah shi kam yana son matarsa. Kuma duk abin da take masa yana dannewa saboda darajar yayanta da ta mahaifinta, da kuma son da yake mata. Da ma an ce so hana ganin laifi. “Mu je?” Ta faɗi ganin bai ja motar ba har bayan da ta shiga. Idonsa ya ɗauke daga kanta, sannan ya tayar da motar ya fita daga gidan, gidan Hajiyarsu suka fara zuwa, kafin su nufi gidan su Mariyar. A falo suka iske Hajiyarsa zaune tana cin abincin dare. A falon suka zauna, suka gaisheta cike da girmamawa. Har ta karɓi Hilal tana masa wasa. Kafin suka mata sallama suka fita a kan za su je gidan su Mariya ne. Sai da suka fita daga falo ta janye idonta a kansu. Ta girgiza kai, halin damuwar auren ɗan nata na bata mamaki. Ba sai an faɗa ba, ta san cewa Faruk ba ya jin daɗin zama da Mariya. Duk kuwa da bai taɓa faɗa mata ba, saboda ta san halin zurfin ciki irin nasa. Amma ko makaho ya shafa zai gane hakan. Sai dai kuma ita a matsayinta na uwa bai kamata ta saka musu baki a cikin al'amarin aurensu ba tare da sun sakota a ciki ba. “Wa alaikassalam!” Ta amsa sallamar ɗanta Adamu, yayan Faruk, kuma ƙanin Bara'atu 'yarta ta fari dake aure a mahaifarsu wato Haɗejia. Asalin mahaifinsu Alhaji Haruna haifaffen garin Hadejia ne. Wanda ya gaji sarautar Kaigaman Haɗejia tun daga kakkaninsa. Kuma yana da mata biyu. Hajiya Ruƙayya ita ce matarsa ta fako, wadda ta haifa masa yara uku maza, wanda a yanzu babbansu Muhammad Bello shi ne yake riƙe da sarautar ta Kaigama. Hajiya Aisha, wato mahaifiyar su Faruk ita ce matarsa ta biyu. Wadda ta haifa masa yara uku, Bara'atu ita ce ta farko, sai kuma Adamu, sannan Faruk. Kasancewar harkokin kasuwancinsa yana yinsu ne a garin Abuja ya sa ita Hajiya Aisha ya dawo da ita nan garin Abuja. Yayin da matarsa ta farko da yaranta ke gidansa na garin Haɗejia. Karatu ne ya sa Bara'atu ta koma Haɗejia. Kuma da Allah ya sa rabonta a can yake sai Allah ya haɗata da mijinta a can ɗin. Wanda suka yi aure har suka hayyayafa, kafin Allah ya masa rasuwa, amma duk da haka bata bar garin Haɗejia ba, saboda aikinta da kuma yaranta da 'yan uwanta da suke can. Adamu kuma yana da mata ɗaya. Wadda yake zaune da ita a nan garin Abuja da yaransa biyu. MARIYA POV. Durƙushe suke ita da Faruk a gaban Daddy. Wanda ke musu nasihar hannunka me sanda. A nasihar tasa bai fito yace akwai ɗaya daga cikinsu da ya zo ya kawo ƙarar ɗan uwansa ba. Kuma bai nuna cewa ya san akwai matsala a tsakaninsu ba. Ya yi amfani da hikima irin tasu ta manya. Wurin ganin ya nusar da su kurakuransu cikin ruwan sanyi. Tun da babu wanda ya san abin da ke tsakaninsu. Ko da Daddy ya kai ƙarshe sai Faruk yace inshallah za'a kiyaye. Mariya kuwa bata ce komai ba. Kuma da ma ba za ta ce ɗin ba. Da Daddy ya sallame su ma ta riga shi fita daga falon na Daddy. Ta wuce sashin Mummy, yayin da shi kuma ya tsaya a wurin Mu'az dake compound. Sun daɗe a gidan. Kafin suka yiwa kowa sallama suka tafi. Faruk ya ɗauka cewa Mariya ta ji nasihar Daddy, ta kuma ɗauketa kamar yanda Daddyn ke fata, amma sai ya ga saɓanin haka. Dan suna komawa gida ta wuce ɗakinta ɗauke da Hilal a hanunta, wanda ya yi bacci. A mamakance ya bita da kallo har ta shige ɗakin. Ji ya yi yau ba zai iya turewa ba kamar yanda ya saba, dan haka ya bita ɗakin dan ya mata magana. A bakin gado ya sameta tana kwantar da Hilal. “Mariya” Ya kira sunanta. Ta juyo ta kalleshi. “Na ɗauka cewar ko da laifi na miki, za ki yafe min saboda nasihar da Daddy ya mana ɗazu. Na ɗauka cewar ko da kina jin haushina ne za ki sauƙo saboda maganar Daddy... Amma kuma kin tabbatar min da ba haka ba ne, tun da har kika dawo ɗakinki a maimakon nawa.” Mariya ta yi shiru tana kallonsa. Wai da shi haka yake zaton tana da sauƙin kai?. Ai ko ya yaudari kansa da zuciyarsa. A ta waje ne jama'a ke mata kallon me sauƙin kai, amma a ta ciki sam Mariya bata da taushin zuciya. “Faruk! A gaskiya ba na jin zan sake haɗa ɗaki da kai. Ballantana har na haɗa shimfiɗa da kai... Wannan a baya ne, ban da yanzu!” Ta yi maganar tana juya masa baya, tare da nufar barthroom. Amma sai ya riƙo hannunta ya dawo da ita baya. Ta kalli hannunta da ya riƙe, sannan ya kalli fuskarsa. “Faruk! Are you trying to hurt me?” Ta tambaya a mamakance. Faruk ya kalli hannunta da ya matse. Da sauri ya saki hannun nata, sannan yace. “Mariya, look, I don't want to hurt you or cause you any harm. I just want to know if you've stopped loving me. Just be honest with me!... A farkon aurenmu ba haka muke zaune ba. There is love and care. Me ya sa komai ya sauya yanzu? Could you explain to me why?” Ko gezau ba ta yi ba ballantana ta ba shi amsa. Jin haka ya sa Faruk ya ɗora yatsun hannunsa biyu a kan karan hancinsa ya rintse ido. Sannan ya buɗe idonsa. “Mariya!. Idan sona kika daina ya kamata ki faɗa min. Ni kuma a shirye nake domin sawwaƙe miki, da ace mun ci gaba da yin irin wannan zaman da za mu riƙa cutar da junanmu!...” Jin yana batun rabuwa ya sa Mariya ta saka ƙwayar idonta cikin nasa. Sannan a hankali bakinta ya motsa cikin faɗin wata kalma. A take ƙwayar idonta ta sauya kala zuwa ja. Wani irin jiri Faruk ya ji ya kwashe shi. Hakan ya sa ya yi saurin dafe kansa yana yin baya. Idonsa ya rintse gam, sannan ya buɗe yana jin wani irin juyawa da kansa yake. Juyowa ya yi ya kalli Mariya dake tsaye. A take ya ji tunaninsa ya birki ce. Sai ya kasa tuna sanda ya shigo ɗakinta. Ya kasa tuna maganar da yake, kamar kuma wani abu yake nema a wurin wani. “Mary!” Ya kira yana kallonta. “Papi lafiyarka ƙalau?” Sai ya sauƙe hannunsa daga kansa yana kallon ɗakin kamar baƙonsa. Gaba ɗaya ya kasa tuna abin da ya faru a ɗakin. “Me nake yi a nan?” Wani irin makirin murmushi ta yi na gefen baki. Sana ta nufe shi, ta tsaya a gabansa ta yanda har suna musayar numfashi. “Baka da lafiya Papi. Mu je na kaika ɗakinka” Ta faɗi tana kama hannunsa na dama. Sannan ta shiga jansa zuwa waje. Kuma bai musa mata ba. Ya bi bayanta yana son tuna abin da ya kai shi ɗakinta. Amma ya kasa tunawa. Har ɗakinsa ta kai shi. Sannan ta zaunar da shi a bakin gado. Ta ɗauki ruwa ta bashi ya sha, har zuwa lokacin bai fita daga cikin ruɗanin da ya shiga ba. “Ba

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});