Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 17

Chapter 17

Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel – Maimuna’s Painful Story 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kuma baƙar straight skirt. Ta yafa baƙin veil a kanta. Kuma ya lura da kamar kayan su ne wanda masu aikin wurin suke sakawa. Ƙwayar idonta dake rawa a kan fuskarsa, da kuma hawayen da ya taru a cikin idonta da yake ƙyalle saboda hasken fitilun wurin yasa ya ji kamar yana nitsewa cikin wani abu me kama da gajimare. Akwai rauni, haɗe da neman taimako a cikin idonta. Sannan ya ga fata da kuma sa rai a cikinsu. Yanayin yanda ta turo fatar bakinta ta ƙasa zai sa ka san cewa shagwaɓɓaɓɓiya ce tun tana da ƙarancin shekaru, ko kuma wadda gata ya yi wa yawa. “Mu'az!” Faruk ya kira yana taɓa kafaɗarta. “Humm!” Ya amsa kamar wanda ya dawo daga WATA DUNIYA. Ya kalli Faruk, sannan ya sake kallon budurwar dake tsaye a gabansa har zuwa lokacin. Tana dafe da kuncinta. Ga hawayen da take zubarwa, sannan bakinta da ta turo cikin shagwaɓa yana rawa kaɗan. ‘Oh lord have mercy!’ Ya faɗi a zuciyarsa. “Wai me ya faru ne?” Faruk ya tambaya. Amma sai Mu'az ya kasa magana. Ya ci gaba da kallonta. Har zuwa sanda wata murya ta kira sunan. “Halima!” Daga bayansa. Hakan ya sa ya juya, yayin da ita kuma budurwar me suna Halima ta kalli Kairat ƙawarta da ta kirata. Dan haka sai ta sauƙe hannunta daga kan fuskarta. Ta sunkuyar da kanta ƙasa, ta raɓa Mu'az ta wuce wurin Kairat. “MJ!” Faruk ya kuma kira. Mu'az ya juyo ya kalle shi. Sai kuma ya kalli rigunan da yake riƙe da su, haka kawai ya aje rigunan a kan wasu kaya. Ya nufi hayar fita. Kai a kulle Faruk ya bi bayansa. Dan shi sam bai ga tahowar yarinyar ba, ballantana ya ga sanda suka yi karo da Mu'az ɗin. “Me ya faru wai?” Kairat ta tambayi Halima da har zuwa lokacin bata daina hawaye ba. Sai ta juyo mata da ɓarin fuskarta na dama. Inda shatin hannun mutumin da ya mareta ya fito har guda huɗu. Wurin har ya yi ja. Ya kuma kumbura. “Na shiga uku? Wai wancan sojan ne ya mareki haka?” Kairat ta tambaya tana zaro ido. Tare da kama gefen fuskar ƙawarta tana ganin yanda wurin da aka mareta ya yi ja. Cike da shagwaɓar da ta zame mata jiki Halima ta gyaɗa kai tana goge ƙwalla. Sannan cikin murya me sanyi tace. “Haka kawai bawan Allahn nan ya sharara min mari, wai dan na bige shi. Kuma fa sai da na kauce masa, shi ne bai kula ba!” “To Allah ya saka miki. Ya hana masa sukuni saboda marainiyar Allah da ya cutar!” Kamar an kunna famfo haka ta ci gaba da zubar da ƙwalla. Kuma da ma ita can haka take. Abu kaɗan kan iya sakata kuka, ballantana yanzu da ta sha mari. Har zuciyarta ta jawa wannan azzalumin sojan Allah ya isa ta fi sau dubu. MARIYA POV. Kukan Hilal da ya cika ɗakinta ne yada ta ja dogon tsaki. Sannan ta juyo ta kalle shi. Yanayin zaman da ya yi kaɗai ya sa ta gane cewa bayan gari ya yi a cikin diapers ɗin dake jikinsa. Wani tsakin ta ja, sannan ta ci gaba da latsa wayarta hankali kwance. Kukan nasa da ya ci gaba da tashi ya sa ta kalle shi a hasalle, sannan ta daka masa tsawar da za ka dafa ƙur'an kan cewa ba ita ta yita ba. “Ka rufe min bakinka a wurin!” Amma bai yi shirun ba. Sai kukan nasa da ya ƙarawa volume. Wani dogon tsakin ta kuma ja. Sannan ta miƙe tsaye ta fita daga ɗakin, ta kulle ƙofar ɗakin. In yaso ya je can ya yi ta yi shi kaɗai. Tana taka stairs tattoo ɗin dake bayan wuyanta ya soma haske. Hakan ya sa ta ƙame a wuri ɗaya. Domin ta san kira ne daga shugaban bayin shiaɗan. Bata raba ɗayan biyu ba suffar Wahash ta bayyana a tsakiyar falo. Hakan yasa ta sauƙa ƙasa da gudu. Sannan ta yi saurin zubewa a ƙasa, ta yi wa shugaban bayin shaiɗan sujjada. “Giram gareka Wash. Duk wani shugaba da ba kai da shaiɗan ba ba a kan gaskiya yake ba!” (A'uzubillah!) Wahash ya sa hannu ya ɗago da ita, ya miƙar da ita a kan ƙafafunta. Amma kanta a ƙasa cike da girmamawa irin tasu ta 'yan wahala a duniya. “Rezor!” Wahash ya kira. Hakan ya sa ta ɗaga idonta ta kalli fuskarsa. “Mijinki da ɗan uwanki, da kuma wani jami'in ɗan sanda na shirin haƙa ramin binne kansu!” Cike da rashin fahimta tace. “Ban gane ba shugaban bayin shaiɗan!” Wahash ya juya bayansa. Sannan ya yi taku biyu gaba. Ya ɗan juyo kaɗan ya kalleta. “Duk da na sa a goge duk wata shida da za ta nuna cewar ke kika kashe Munira da kuma Danesh sai da suka yi ƙoƙarin zaƙulo wani abin. Yanzu haka shi ɗan sandan da suka ɗora a kan aikin yana ta binciken gano wanda ya kashe Danesh da Munira, domin kuwa duk sun gane cewa makasan nasu mutum ɗaya ne ko biyu. Ko ma sama da haka, kuma da alama suna daf da cimma gano ki. Ganoki kuma yana nufin gane ƙungiyar jajayen bayin shaiɗan!...” Mariya ta girgiza kanta da sauri, sannan ta tsaya avbayan Wahash tana faɗin. “Yanzu wani mataki aka ɗauka a kansu... Da ace asirin ƙungiya ya tonu tadalilina gwanda a kawar da mijina da kuma ɗan uwana. Idan har asirin ƙungiya ya tonu ina zan saka kaina Wahash?!” Wahash ya girgiza kansa, sannan ya juyo suka fuskanci juna. “Mijinki da ɗan uwanki ba su ya kamata mu kashe a yanzu ba. Shi wannan ɗan sandan me sunan Muktar shi ne babban haɗarinmu a yanzu. Dan haka shi ne wanda za mu fara kawarwa a duniya” Ba tare da ta nemi sanin waye ɗan sandan ba tace. ”Ina fatan yin hakan ya kawo ƙarshen wannan tsinannen binciken da aka fara. Da dukkan goyon bayana na amince da hakan Wahash!” Wahash ya gyaɗa kansa. Sannan ya lumshe idonsa, cikin ƙasa da sakanni ya ɓace a falon. Mariya ta ja dogon tsaki tana jin haushin Mu'az da Faruk a lokaci guda. Ta lura da kamar suna so su daƙile mata son kasancewarta ta hannun daman Wahash. Amma ba komai, idan har suka ci gaba da ƙoƙarin tono ramin za ta sa a binne su ciki. _Share fi sabillilah❤️_ *Daga alƙalamin Salma Ahmad Isah✍️.* *CANDY CE🦋.* -------------------- _Kada a manta da biyan kuɗin littafi. Dan free pages sun kusa ƙarewa. To subscribe pay ₦300 to._ 5487270431 Salma Isah Monie point. And send the evidence of payment via. 08130172702 #Candy °°°°°°°°°°°°°°°°°° *ƘADDARA CE!* *©SALMA AHMAD ISAH.* *CANDY🦋* _ArewaBooks @SalmaAhmad_ _Wattpad @Salma_Ahmad_Isah_ *07* *Unguwar Dutsen Alhaji, Bwari, Abuja.* *Da misalin 08:20 na dare.* HALIMA POV. Mai mashin ɗin da ya ɗaukota tun daga Ummul Banat boutique, wato wurin da take aiki ya tsaya a ƙofar gidan kawunta. Ƙanin mahaifinta, wanda take kira da Kawu Sani. Sauƙa ta yi daga kan mashin ɗin. Sannan ta ɗauko kuɗin mai mashin ɗin ta ba shi. Ta juyo ta kalli ƙaramin gidan da ya fi ko wani gida nuna halin rashi a layin. Bakinta ɗauke da sallama ta shiga gidan. A tsakiyar gidan ta taka birki. Ta

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});