Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 22

Chapter 22

Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel – Maimuna’s Painful Story 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ko girki. Tana ji tana ganin ƙananan yaran gidan zaune suna harkarsu aka sakata aikin ɗiban ruwa. Kuma ba ta isa ta musa ba, dan ya zame mata dole. Da zunɓure-zumɓuren bakinta da komai ta fita daga gidan ɗauke da bokiti. Tana tafe tana hawayen da suka zame mata farilla. Gidan dake kusa da nasu ta shiga, sannan ta roƙi matar kan dan tana so a mata lamunin ɗiban ruwa a somon gidan. Matar bata hanata ba. Dan sun ɗan saba a zamanta a unguwar. Sai da ta cika babbar randar gidan, sannan Mama Zulai tace ta je ta ɗebowa Jidda ruwan wanka. Wai akwai inda take son zuwa yau. Cike da baƙin ciki ta fita daga gidan. Amma ƙiwarta ta hanata ƙarasawa gidan da take shiga ɗiban ruwan. Sai ta tsaya a ƙofar gida. Jim kaɗan ta koma cikin gidan tace ai matar gidan tace ruwan ya ƙare. “Ke maƙiwaciya ko? Ai ko za ki ga ƙiwa ganin idonki... Jidda! Jidda!” Mama Zulai ta ƙarashe tana kiran Jidda. Jidda dake ɗakinta na ita kaɗai ta fito tana amsawa. “Zo ki ɗibi ruwa a randa ki yi wankanki... Ke kuma idan kin ɗibi ruwan nan sai dai idan na mutu!” A take idon Halima ya ciko da ƙwalla. Da ma kukan a kusa yake. Dan haka ta sake shi takaici na cika ranta. Tana ji tana gani 'ya'yan Mama Zulai suka dinga ɗiban ruwan suna ɓatawa. Kuma ba ta isa tace uffan ba. Sai Mama Sadiya ce ta sa ɗaya daga cikin yaranta ƙanana ya je ya ɗibowa Halima ruwa dan ta yi wanka. Da haka Mama Sadiya ta kashe wutar kukan nata. Tana zaune yaron ya kawo mata ruwan. Sannan ta yi wanka ta shirya domin tafiya wurin aikinta. Ko abinci bata zauna ci ba. Saboda ita yanzu ba ta jin za ta iya cin wannan busasshen ɗumamen nasu me kama da dutse. Babur ta hau, wanda ya sauƙeta a Ummul Banat boutique. Kuma shigarta cikin boutique ɗin ba wuya ta hango shi yana shigowa. Wannan farin mugun sojan da ya sauƙe mata rabin fuska jiya. Tana ganinsa ta yi saurin ɓuya a bayan wasu kaya da akajera a cikin boutique ɗin. Dan ba ta ma son wani tsautsayi ya sake haɗata da shi, bare har ta kai ga ya sake marinta. MU'AZ POV. Kamar yanda ya kwanta da tunaninta haka ya tashi da shi. Har ya gama shirinsa na fita bata fita daga tunaninsa ba, da ƙyar ya iya samun sukunin cin abinci. Kuma yana gama cin abinci ya yi hanzarin fita daga gida. Kai tsaye ya nufi Ummul Banat boutique. A sanda ya shiga wurin ya lura da cewar yanzu ma masu aikin wurin suke zuwa. Dan haka ya shiga raba idonsa a kansu, wai ko zai ga tauraruwa mai wutsiyar da ta hargitsa masa lissafi a iyaka jiya kawai. Amma bai ganta ba. Dan haka ya tsayar da ɗaya daga cikin ma'aikatan wurin, ya tambayeta. “Dan Allah ina neman wata... Wata farar yarinya haka... Fara ce... Eh fara!” Ya tsaya kame-kamen kammaninta. Dan gaba ɗaya ba yace ga yanda suffar jikinta take ba. Da ace yanayin idonta aka tambaye shi da ya zayyana komai game da shi, ba dan kar ya yi ƙarya ba, zai iya cewa ya san adadin yawan gashin idonta na ƙasa. Saboda su ne abin da ya fi kallo a fuskarta. “Halima kake nema?” Ma'aikaciyar ta tambaya. Sai ya kalleta yana tuna sanda wata ta kirata da Halima jiya. Kamar gaula, haka ya gyaɗa mata kai, sanna ya ƙara da. “Eh, ita ce. Ya aka yi kika sani?” Sai ya ga ta ɗan yi murmushi. “Cry-cry baby kenan. Ai na ga sanda ka mareta jiya!” Kamar wanda ita ma ta koɗa masa marin haka ya ji sauƙar maganarta a tsakiyar kansa. Hakan ta sa ya rintse idonsa. Kafin ya buɗe yana cilla mata tambaya. “A ina zan ganta?” “Bata daɗe da zuwa ba ai. Ka duba ta can, ba za ta wuce wurin ba” Ya dubi inda ta nuna masa. Sannan ya mata godiya ya raɓata ya wuce. A hankali yake duba kayyayakin dake wurin. Har ya wuce, sai ya tsaya cak, saboda wani hoto da idonsa ya ɗauko masa. Ya dawo da baya, ya tsaya a inda ya ganta. Sannan a hankali ya kalli fusarta da ta ɓoye a tsakiyar kayan. Suna haɗa ido Halima ta zaro nata idon. Sannan ta turo baki gaba tana shirin fashewa da kuka. Ta miƙe tsaye tana shirin fita da gudu. Kuma a lokacin ya aikata abin da bai taɓa zaton zai aikata ba. Kuma ya aikata abin da ita kanta Halima ba ta zata ba. Dan ba ta yi taku uku ba ta ji ya riƙo tsintsiyar hannunta. Cak Halima ta tsaya. Ƙirjinta na dokawa da mugun ƙarfi. Saboda wani abu da ta ji ya sauƙa a kan fatar hannunta me tsananin taushi. Bata kai ga tantance abin da yake faruwa da ita ba ta ji ya dawo da ita baya. Sannan ya shiga janta zuwa waje. Bata san me ya zare mata laka ba har ta kasa musa masa. Dan haka ya yi ta jan hannunta tana biye da shi har parking lot. Kallonsa kawai take, bakinta sake, hawaye kuwa tuni suka wanke mata fuska. A jikin motarsa ya tsayar da ita, sannan ya buɗe front seat. Ya zaunar da ita a cikin motar, amma kuma ƙafafunta duka biyu suna waje. Har zuwa lokacin kallonsa kawai take tana sakewa, ashe ma jiya bata ƙare masa kallo ba. Saboda sai a yau take ganin ainahin kammanin fuskarsa da ba su bayyana gareta ba a jiyan. Fari ne sosai, yana da tsayi, kuma yana da manyan idanu. Ga wasu dogayen gashi da suka ƙawata mabuɗar idon nasa sama da ƙasa. Ga kuma baƙin gashin girarsa da bai cika yawa ba. Kansa babu gashi sosai, sannan a fuskarsa babu gemu, sai dai ɗan siririn gashin bakinsa da babu gashi da yawa, dan sai ka yi da gaske za ka gane cewa yana da gashin bakin. Yanda yake kallonta da fararen idanuwansa ya sa ta ji kamar ba a zaune take a kan kujerar motarsa ba. Sai ta ji kamar tana zaune a kan wani abu me tsananin laushin da ya fi gajimare. Duk sai ta ji kamar za ta narke a wurin. Ba ta dawo hayyacinta ba sai da ya miƙa mata gorar ruwa, sannan yace. “Karɓi ki sha” Sai ta kalli gorar. Sannan ta kalli farin hannunsa da ya riƙe gorar. Wanda yake ɗauke da fararen faratu, gakuma wani baƙin smart watch da ya saka a tsintsiyar hannunsa da ya sa farar fatar tasa ƙara haskawa da kyau a cikin safiyar. Cikin wannan shagwaɓar da ta zame mata jiki ta ɗaga hannu ta karɓi ruwan. Sannan takai bakinta ta sha tana hawaye har zuwa lokacin. Yayin da Mu'az ya ke tsaye a kanta yana ƙare mata kallo. Shi kam ba zai ce jiya bai kalleta da kyau ba. Ya kalleta sosai, ta yanda ko da zana kammaninta za ayi idan aka tambaye shi zai iya wassafasu. Amma wannan fuskar tata da ta shagwaɓe ce ta fi ɗaukar hankalinsa fiye da komai tattare da ita. Haka kawai ya ji ta burge shi. Yanda ta turo bakinta

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});