Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 1

Chapter 1

Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel – Maimuna’s Painful Story 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

*ƘADDARA CE!* _(Destiny unfolds with a heavy heart)_ *©SALMA AHMAD ISAH.* *CANDY🦋* ••• Assalamu alaikum jama'a. Barkan mu da wannan lokaci. Sannun mu da sake saduwa da ku a sabon littafina me taken ƘADDARA CE!. To, kamar littafin HASKE, shi ma wannan paid book ne. A kan ₦300 kacal. Amma kafin nan ina ɗauke da free pages har guda 10. To sai ku gyara zama, domin karɓar wannan da zafinsa. Kamar dai yanda kuka saba karɓar duk wani rubutu nawa. *⚠️ Ban yarda da wani/wata. Ya sarrafa min littafi ta ko wace hanya ba tare da izinina ba. Saboda yin hakan, babban kuskure ne. Da fatan za mu kiyaye, a bi doka a zauna lafiya.* Na sadaukar da wannan littafin zuwa ga duk wata 'ya mace dake fama da cutar sickler... •Gaisuwa zuwa ga Khadeeja Candy, Hadiza D Auta, Sadi Sakhna, Nainerh KD, Fatima Ahmad Isah da kuma Amina Ahmad Isah. Allah ya kare min ku a duk inda kuke.• *SHIMFIƊA...* KADDARA! Shin me cece ita?. KADDARA na ɗaya daga cikin hukuncin Allah da ya kan zartar a kan bayinsa tun yayin hallita. KADDARA tamkar zagayen zobe take, wanda ɗan adam ke rayuwa a tsakiyarsa. Duk wani abu da ya samu bawa tun daga ranar haihuwarsa zuwa ga ranar da zai koma ga mahallicinsa sunansa KADDARA. KADDARAr ko wani bawa na rubuce ne tun kafin ya iso zuwa duniya. Kowa da ka ga yana rayuwa a doron duniya yana yin ta ne a doron KADDARA. KADDARA na ɗaya daga cikin manya manyan siffoffin Allah subhanahu wata'ala. Domin duk abin da ya samu bawa a rayuwa muƙaddari ne daga wurinsa. Wa lau me kyau, ko akasinsa. بسم الله الرحمن الرحيم *01* *Unguwar Fantai, Haɗejia local government, Jigawa state.* *Da misalin 08:20 na dare.* Matashiyar yarinya ce tafe a gefen hanya. Hannunta na dama riƙe da farin bokitin fenti. Yanyin yanda doguwar rigar atamfar robar da take sanye da ita ke mannewa a jikinta zai sa ka fahimci cewa ana cikin yanayin hunturu ne. A hankali take ɗingisa ƙafarta ta hagu wadda daga gani bata da lafiya tun asali. A kallo ɗaya da za ka mata za ka san cewa tana ɗauke da ciwon sickler. Saboda kalar idonta da yake yalo. Da cikinta da ya tashi kamar na me jaririn ciki. Da kuma yanda yanayin jikinta yake nuna cewa tana da sickler. Damuwa ce kwance a kan allon fuskarta dake nuna nau'in jinyar da take fama da ita. Kuma damuwar tata ta samo asali ne sakamakon wani da ya karɓi kunun ɗari biyu a wurinta ya sha. Ya tashi ya tafi ba tare da ya bata kuɗi ba. Ba wai wannan ne ya jefata cikin damuwa ba. Fargaba take na yanda za su kwashe da matar babanta Auwwa. Saboda kunun nata ne, ita ce take mata shi dan ta je ta siyar ta kawo mata kuɗi. Kuma a kullum cikin gargaɗarta take kan kada ta kuskura ta bada bashi ko da kuwa kunun zai yi jangwaɓo ne. Jiki a sanyaye ta dakata a ƙofar gidansu na masu ƙaramin ƙarfi. Ta ɗaga kai ta kalli gidan tana jin yanda iskar da ake a garin take shiga har cikin ƙasusuwan jikinta da ba su da ƙwari. Ga kuma yanda ƙafarta ta hagu ke mata ciwo tun a safiyar yau da ta tashi. Kasancewar lokacin sanyi shi ne lokacin da ciwon sickler ya fi zaɓar ya dinga tashi a-kai-a-kai. Yawu ta haɗiye a sanda ta hasaso irin azabar dake jiranta a cikin gidan. Ko da rantsuwa za ta yi ba za ta yi kaffara ba kan cewar yau sai ta yabawa aya zaƙinta. Dan Auwwa ba ƙyaleta za ta yi ba. Cikin saddaƙarwa da sallamawa rayuwa ta shiga gidan, bakinta ɗauke da sallama. A tsakiyar gidan ta ci birki. Sakamakon arba da Auwwa da ta yi, zaune a tsakar gida tana firfita murhu. Wutar dake cikin murhun ta kalla. Sannan ta faɗawa kanta cewar sai an ɗana mata wannan wutar a fatar jikinta. Saboda tsabar Auwwa muguwa ce. Ba ta hukuntata da komai sai da wuta. Hantar cikinta ce ta kaɗa, a sanda hankalin Auwwan ya kai kanta. Wata uwar harara ta watsa mata tana faɗin. “Kunu ya ƙare yau?” Cikin fargaba ta gyaɗa kanta tana aje bokitin hannunta a tsorace. Auwwa ta harerata tana faɗin. “Miƙo min kuɗin nan na lissafa shi.” A hankali ta matsa kusa da Auwwan tana jin ƙamshin azabar da za'a mata na kusantota. Ta tsugguna a ƙasa. Sannan ta sa hannu ta ciro cinikin da ta yi a cikin jaka. Ta miƙawa Auwwan tana jin ƙwallar azabar da ba'a mata ba na cika idonta. Auwwa ta karɓi kuɗin. Sannan ta shiga lissafawa. Har zuwa lokacin matashiyar na tsugunne tana sauraron hukuncinta. Cike da masifa Auwwa tace. “Ina kika kai ɗari biyu?” Matashiryar da ƙwallar idonta ta fara zubowa ta ɗaga kai ta kalli Auwwa. Sannan ta girgiza kanta tana faɗin. “Salisu osi ne ya karɓi kunun na ɗari biyu ya sha. Da zai tafi nace ya bani kuɗin... Shi ne yace... Ya ce wai sai gobe zai bada, yanzu babu canji a wurinsa!...” Ba ta kai ga rufe bakinta ba wani mari me ƙarfi ya sauƙa a kan kuncinta. Ta fashe da kuka tana dafe wurin. Cikin ƙanƙace ido Auwwa tace. “Maimuna sau nawa nake ja miki kunne kan bada kayana bashi?. Saboda irin wannan ya sa sai na auna kununa ko na nawa ne, sannan nake baki ki fita da shi... Amma sai da kika ha'ince ni. To ba ki sha ba!” Auwwa ta kai ƙarshe tana rarumar bakin wutar dake cikin murhu, sannan ta kamo hannun Maimuna ta ɗora mata shi a kan tafin hannunta. Haka ta dinga ƙwalla ihu tana kuka tana faɗin ba za ta sake ba. Amma Auwwa bata ƙyaleta ba sai da ta tabbatar da ta ɗauke mata fatar tsintsiyar hannun sannan ta saketa. “Gobe ma ki sake bawa wani bashin kayana kin ji?... Kuma ki zo ki zauna ki kaɗa min miya” Cike da jin raɗaɗin da hannunta yake mata. Maimuna ta gyaɗa kai. Tana jin yanda fatar wurin da Auwwa ta ɗora mata wuta ke tashi. Auwwa ta miƙe daga kan kujerar da take zaune. Sannan ta shige ɗakinta. Yayin da ita kuma Maimuna ta ja jikinta ta zauna a kan kujerar tana kukan da ya zama abokin rayuwarta tun tasowarta. Saboda a rayuwa ba ta jin tana haura sati ɗaya ba tare da ta yi kuka ba tun da ta zo duniya kuwa. Iyaye su ne bango kuma abin jinginar 'ya'yansu masu rauni. Ita bata ta so ta ga iyayenta a raye ba. A lokacin haihuwarta mahaifiyarta ta rasu. Kasancewar mahaifinta direban tirela ne ya sa lokacin da aka haifeta yana garin Lagos. Labarin samun ƙaruwa tare da rashin da aka masa lokaci guda ya sa ya ɗauko motarsa domin dawowa gida. Sai dai kuma cikin nufin Allah sai ya gamu da haɗari a hanyarsa ta Kano zuwa Haɗejia. Hakan ya sa ta taso a wurin matar babanta ta farko wato Hauwa, wanda ake kira da Auwwa. Duk da kakarta ta wurin uba tama da rai, amma haka aka barta a wurin Auwwa tana gasa mata aya a hannu tun tana ƙarama. Da Allah ya so jarrabarta sai ya sa

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});