Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 13

Chapter 13

Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel – Maimuna’s Painful Story 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Tana gama faɗin hakan ta ja siraran ƙafafunta ta yi gaba. Abin da Abba ya yi bai bata mamaki ba. Saboda Allah ne kaɗai ya san adadin samarin da suka so lalata rayuwarta. Samari da dama sun sha cewa suna sonta, amma ita ta san ba soyyayar gaskiya ba ce. Ƙawayenta na makaranta sun faɗa mata cewar a halin rayuwar yanzu babu namijin da zai iya aureta, saboda tana da sickler. Duk wanda zai zo yace yana sonta raina mata hankali kawai zai yi. Kuma ita ma ta yarda da wannan batun nasu, shi ya sa bata sa a ka ba, in ji ɓarawon tagiya. Bata takurawa kanta cewar sai ta yi aure ba. Tun da ta kammala secondary school bata sake sakawa kanta wani buri ba. Saboda ita ma secondary school ɗin da ƙyar da fama Auwwa ta barta ta ƙarasa. Shi ya sa ta ture ko wani irin buri da ta san tana da shi. Ta fawallawa sarkin sammai da ƙassai duka lamuranta. Kuma ta san zai kawo mata ƙarshen wahalar nan da take sha. “Salamu alaikum” Ta yi sallama daga soron gidan. Jin muryoyi uku sun amsa sallamar ya sa ta fahimci cewa ba Auwwa ba ce kaɗai a gidan. Ilai kuwa, kusan su huɗu ta samu a tsakar gida. Kuma ta san su waye, ƙannen Auwwan ne daga cikin gari. “Anti Kubura ina wuninku!” Ta gaishe su tana tsuggunawa. Ciki-ciki suka amsa. Kuma ita bata damu ba, dan idan da sabo ta saba. Tana shirin miƙewa Auwwa ta dakatar a ita da faɗin. “In ji dai kunu bai ƙare ba?” Ta sauƙe ajiyar zuciyar kwanciyar hankali. Dan ta san tun da su Kubura suka zo su za'a bawa sauran kunun. Da ace ba su zo ba kuwa yau da ta yabawa aya zaƙinta a hannun Auwwa. Da sauri ta gyaɗa kai tana aje bokitin. “Akwai saura” “Shiga kitchen ki ɗauko kofuna ki zubawa su Kubura!” “To” Maimuna ta amsa da sauri. Sannan ta miƙe ta shiga ɗan ƙaramin kitchen ɗin gidan. Ta ɗauko kofuna huɗu. Ta zube kunun da ya yi saura a bokitinta, ta miƙawa ƙannen Auwwa. Daga nan ta shiga banɗaki ta ɗauro alwala. Sannan ta shiga ɗakinta ta yi sallah. Ta fito ta zauna tana jin yunwa, a gefe guda kuma tana jin tsoron tambayar Auwwa abinci. “Ub*n miye za ki zo ki zauna ki samu a gaba kina jin zancen da muke?” Auwwa ta faɗi cike da hantara. Maimuna ta sinne kai tana faɗin. “Yun... Yunwa nake ji!” “Saboda ub*nki ne yake kawowa abincin da zan girka ai dole ki ce min kina jin yunwa. To na yi na bawa 'yan uwana sun cinye... Sai a tashi a kaini gaba” Ta sunkuyar da kanta, ƙwalla na taruwa mata a cikin ido. Kafin ta miƙe ta fita daga gidan. Da ta rasa inda za ta je sai ta nufi unguwar Chadi a cikin wannan daren. Dan ba ta son ta cika kaiwa Mummyn su Maryam matsalolinta. Jiki da jini, wata rana za ta iya gajiyawa da ita. Dan haka gwanda ta je wurin dolenta, wato gidan kakarta. Da yake tsakanin unguwar Fantai da Chadi ba nisa sai bata sha wahala wurin isa ba. Tun daga soro ta fara shagwaɓe fuska, dan ta san ta zo inda za'a share mata hawaye. Sallamar ma a shagwaɓe ta yi, ta shiga cikin gidan tana wani bubbuga ƙafa a ƙasa. “Wani irin iskanci ne kuma wannan Maimuna?” Hajja dake zaune a cikin ɗakinta ta tambaya. Maimuna ta ƙarasa cikin ɗakin tana turo baki gaba. “Hajja” Ta kira tana zama kusa da kakarta. Hajja ta dubi jikar tata cike da tausayawa. “Na'am mai sunana” “Hajja yunwa nake ji. Rabona da abinci tun safe” Ta faɗi a shagwaɓe tana shafa cikinta. Hajja ta girgiza kanta. “Jeki ki ɗiba abincin a cikin cooler. Yana nan a rumfa” “Da yawa fa zan ɗiba” “Ɗibi wanda zai isheki” Ta miƙe ta fita da murnarta. Ta ɗauki kwano ta zubo tuwon shinkafa da miyar taushen da Hajja ta girka. Ta buɗe ɗan ƙaramin fridge ɗin Hajjan, ta ɗauki pure water. Ta dawo ɗakin ta zauna. Ta shiga ci tana bawa Hajja labarin abin da ya faru da ita yau, ciki har da haɗuwarta da Abba. “To yanzu Maimuna. Da kika masa haka, idan kuma da gaske yake yana sonki fa?” Maimuna ta dakata daga kai loma bakinta. Ta mayar da abincin da ta ɗebo cikin kwano. Sannan ta kalli Hajja. “Hajja ban bari ya kai ga furta min hakan ba. Saboda na san ba zai min soyyaya tsakaninsa da Allah ba. A irin halin da nake ciki bana jin akwai namijin da zai soni” Hajja ta girgiza kai. “Ba komai Maimuna ƙaddara ce!. Ki ci gaba da haƙuri, Allah ya san da ke. Kuma zai kawo miki sauyin rayuwa” Maimuna bata sake cewa komai ba. Har ta kamalla cin tuwonta. Ta fito da kwanon waje. Ta wanke hannunta ta dawo ta zauna kusa da Hajja. “Ina Kawu ne? Tun da na shigo ban ji motsinsa ba” “Ya tafi jajantawa Alhaji Babangida. Saboda asarar da ya yi a satin nan.” Maimuna ta gyaɗa kai. “Ah, Maimuna. Duba cikin jakar can tawa, za ki ga leda ki ɗauko” Cewar Hajja. Maimuna ta miƙe ta nufi jakar. Sannan ta buɗe ta ɗauko ledar dake ciki. Ta dawo kusa da Hajja ta zauna. “Hajja ga ledar” Hajja ta karɓa ta buɗe, sannan ta fito da hijabai biyu dake ciki, da abonaki, da kuma audugar mata. “Gasu nan. Duka naki ne na sai miki a bakin asibiti. Na san yanzu sanyi ya shigo, kina buƙatar abonaki... Kuma idan za ki tafi zan baki kwaki da ƙanzo. Ki ɓoye a ɗakinki idan kin koma. Duk ranar da Auwwa za ta hanaki abinci sai ki ɗauka ki ci” Maimuna ta yi murmushi ta kwanta a jikin kakarta. “Ina sonki Hajja” Hajja na murmushi ta shafa kan gudaliyar jikarta. “Allah ya ji ƙan Muhammadu da Asabe (iyayen Maimuna).” “Amin Hajja” Ta amsa tana jin kewarsu, duk kuwa da kaf cikinsu babu wanda ta sani. Sai dai a hoto ko ta ji labarinsu. FARUK POV. Tsaye ya yi a ƙofar ɗakin Mariya yana kallonta. Yayin da take yafa mayafi a kanta. Alamun ta shirya tsaf domin ziyartar gidansu. Idonsa ya zarce kan Hilal dake zaune a kan gado. A hankali ya saki handle ɗin ƙofar ya shiga ciki. Kallo ɗaya Mariya ta masa ta ɗauke kai. Shi kuma bai ma kalleta ba, Hilal kawai ya ɗauka, sai a sannan ya kalleta. “Kin gama shiryawa ne?” “Umm” Amsarta ta fito a taƙaice kamar kullum. Kansa kawai ya gyaɗa, sannan ya nufi ƙofa yana faɗin. “Ina jiranki a mota” Sannan ya fita daga ɗakin. Kai tsaye ya sauƙa ƙasa, ya shige motarsa dake parking lot. Ya zauna a ciki, tare da zaunar da Hilal a kan cinyarsa. Yana jiran fitowar Mariya. Ido kawai ya tsira mata a sanda ta fito daga ƙofar falo. Saboda kalar kwalliyar da ta yi. Wata kyakkyawar atamfa ce da ya sai mata a Khadeeja Candy store a jikinta. Atamfar me ratsin orange ta bala'in dacewa da fatar jikinta da take wani abu tsakani fari da baƙi. Ta yafa wani orange gyale, fuskarta babu wata kwalliya ta a zo a

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});