Chapter 31
Chapter 31
kuma san wacece ita. Amma abin da bai gane ba shi ne, me ya sa Mariya za ta sace Munira, har ta kai ga kasheta?. Sannan wannan mutumin da suke tare da shi, waye shi?. Me zai sa matarsa da ba za ka yi tunanin idan ka sa mata hannu a baki ba za ta ciza ba ta yi kisan kai?... Yanzu har Mariya za ta iya kashe wani?. Me ya sa?. Me zai sa ta kashe Munira?. A tare suka sake kallon juna, sannan suka kalli Muktar da shi ma yake kallonsu. “Na san kallon wannan videon zai sa tarin tambayoyi a cikin kawunanku... Tabbas wannan Mariya ce. Matarka Kaigama, ƙanwarka MJ. Kuma...” Bai kai ga ƙarasawa ba. Mu'az ya miƙe tsaye, sannan ya shaƙo wuyansa ya miƙar da shi tsaye yana jin kamar ya kashe shi ya huta. Sai huci yake yana jin zuciyarsa na zafi. "How dare you talk about my sister in that tone!?” Ya faɗi a kausashe. Muktar bai ce komai ba, kuma bai yi yunƙurin ƙwatar kansa ba. Saboda ya san ko shi aka zo aka samu da zancen cewa Walid ya yi kisan kai zai iya shiga cikin halin. Da ƙyar Faruk ya cire hannun Mu'az a wuyan Muktar, ya ja shi baya ba tare da ya ce masa komai ba. “I can't believe he thinks Mariya is responsible for Munira's death!... And... and!” Ya kasa ƙarasawa yana jin idonsa na cika da ƙwalla. Amma kuma ba ta zubo ba. Har ji yake numfashinsa na shirin ɗaukewa. Ya yi shiru kawai, yana fitar da iska daga huhunsa da ƙyar, kamar me ciwon zuciya. “Get seated” Faɗin Faruk yana zaunar da shi a kan kujera. Zaman ya yi yana dafe kansa da ya fara sarawa. Da ma shi haka yake, daga zarar ransa ya ɓaci zai fita hayyacinsa gaba ɗaya, idan bai yi sa'a ba ma sai ya kwanta jinya. “Ina jinka Muktar” Faruk ya haɗe kalaman yana haɗiyar yawu da ƙyar. Saboda jin wani abu ya toshe masa maƙoshi. Shi bai faɗa cikinsa ba, kuma bai fito ta bakinsa ba. Muktar ya zauna, sannan ya ci gaba da faɗin. “... Na samo wannan videon ne a unguwar da aka sace Munira. Na same shi ne daga wurin wani yaro da a lokacin da aka sace Munira ya yi recording videon... A lokacin da na samu vedion ban yi ƙoƙarin sanar da kowa ba face Ali mataimakina, wanda tare da shi muka je. Abin da ya ba ni mamaki shi ne a wannan ranar wani ya biyoni gida yana ƙoƙarin kasheni. Amma Allah ya taimakeni na tsira. Sai dai kuma a daren jiya Mariya da wannan mutumin na cikin videon ne suka zo har unguwar mu. Kuma na gansu, sannan su ne suka bigeni da mota. Har na samu waɗannan raunikan na jikina... Shi ya sa na ce ba zan yi ƙasa a gwuiwa wurin sanar da ku wannan gaskiyar ba!” Faruk ya dafe kansa. Tunanin abin da ya faru tsakaninsu jiya ya dawo masa. Ke nan jiya da daddare kashe Muktar ta tafi?. Innalillahi wa inna ialaihi raji'un. Ya furta yana murza goshinsa. Mu'az kuwa bai sake cewa uffan ba. Sai yatsun hannunsa da yake murzawa idonsa na sauya kala zuwa ja. ------------------------------- _Wato a wasu lokutan. Abubuwan da ba mu yi zato ba su ne suka cika faruwa da mu._ _Irin haka ce ta faru ga Faruk da Mu'az._ _Shin! Wani dabi ne zai ɓarke a haɗejia, tsakanin Gambo da Maimuna da kuma Auwwa?._ _Shin, wani hali kuke tunanin Halima za ta shiga idan aka sallameta a aiki?._ _Me zai faru tsakanin Mariya da Faruk?._ _Sannan Mu'az, dan shi kam ya fi Faruk fusata._ _Yaya Mariya za ta yi domin wanke kanta a idon yayanta da kuma mijinta, da ma sauran jama'ar duniya da za su sani?._ _Shin, kuna ganin cewa, kisan Munira zai zama kisa na ƙarshe da Mariya za ta aikata?. Ko za ta ci gaba da zama a ƙungiyarsu ta bayin Shaiɗan!?._ _Hummm!_ _Akwai magana. To, ga duk wanda yake son sanin amsoshin waɗannan tambayoyin, sai ya biya ₦300. Tun kafin tafiyar nan ta wuce ku._ _Kun san daga ganin tafiyar nan ba ta wasa ba ce, dan har yanzu ba mu yi komai ba. Kuma ina me muku tabbacin ba za ku yi da na sanin siyan wanna littafi ba. Kun san alƙalamin Candy akwai suger._ ••• ••• ••• *Zan yi amfai da wannan damar, wurin gode muku, SALMANIANS. Kun san da cewa ku ne on top a ƙalbina. I love you like wujiga-wujiga. Ina sonku fiye da irin son da kuke min* Ga duk wanda ya shirya dan ayi tafiyar nan da shi, zai ₦300 kacal. Ta wannan account details ɗin da zan rubuta. Idan kuma har ya zama complete document sai dai ku biya ₦500. 5487270431 Salma Isah Moniepoint Shaidar biya kuma via. 08130172702. Sai na ji ku SALMANIANS. Best regards. *SALMA AHMAD ISAH* *(CANDY🦋)* 2024...
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31