Chapter 2
Chapter 2
ta taso da cutar sickler wanda aka haifeta da ita. Ita kuma cutar sickler cuta ce da take buƙatar kulawa da kuma bin doka da ƙa'idojin da cutar bata so. Amma sai ga shi ta taso a hannun matar da bata sonta, ballantana har ta bata wata kulawa da me cuta irin tata ke buƙata. Hakan ya sa cutar ta kassarata sosai. Dan babu ta yanda za ayi ka ganta ka kasa sanin cewa tana da sickler. A hankali ta share ƙwallar da ta gama ɓata mata fuska. Sannan ta kai hannunta na dama ta ɗauki ledar kukar da ta siyo ɗazu kafin ta tafi tallar kunu. Ta yi amfani da hannunta na hagu da yake zugo ta kunce laidar. Sannan ta saka ludayi a cikin miyar, ta shiga kaɗa miyar da ta san bata isa cinta ba a yau. Dan tun tana ƙarama ta saba da horon yunwa. Shi ya sa kullum take ƙarewa kamar tsinken kwakwa. Sai da ta gama haɗa miyar, sannan ta sauƙe tukunyar. Ta faɗawa Auwwa cewar ta gama haɗa miyar. Auwwa tace mata to ta kashe wutar, dan kada ta mata asarar ice. Duk da ita ta so ta zauna ta ɗan ji ɗumin wutar haka ta kashe. Sannan ta koma ɗan ƙaramin ɗakin da yake a matsayin nata. Ta ɗauko ledar magungunanta da kawunta ƙanin mahaifinta kan sai mata idan dama ta samu. Ta ɗauki palludrine da folic acid. Magunguna biyu da sukafi sauƙin kuɗi na masu sickler. Ita palludrine aikinta shi ne sace sefar cikin me sickler. Abinda ya kan kawowa masu ciwon sickler ƙaton ciki shi ne kumburar sefa. Kuma ita ce takan jawowa masu sickler ciwon cikin ɓari guda. Sannan idan sefar me sickler ta kumbura ne zai sa ta janye jinin jikin me sickler, ta yanda sai an ƙara musu jini. Ita kuma folic acid amfaninta shi ne hana daskarewar ɓargon me sickler. Daskarewar ɓargo shi kan haddasawa masu sickler ciwon jiki da kuma na ƙafafu a wasu lokutan. Shi ya sa ake sanar da masu ciwon sickler su riƙa shan ta kullum sau ɗaya a rana. Bisa ga mamakinta sai ta ga folic asid ɗin ta kare. Palludrine ɗin ma saura ɗaya. Zama ta yi ta ɗauki palludrine ɗin. Ta jefa a bakinta ta fara taunawa ba tare da ruwa ko wani abun da zai taimaka mata wurin haɗiye ƙwayar ba. Saboda irin waɗanan abubuwan ta saba musu. Har gwanda ma folic asid, wata tana da zaƙi, wata kuma bata da ɗanɗano, amma palludrine tana da ɗaci. Sai dai kuma ita sabo ya cire mata wannan abin. Kwanciya ta yi hannunta na hagu na ci gaba da mata zugi, ga yanda sanyi yake ƙara ratsa ƙashin jikinta. Zanin atamfar da kakarta ta bata domin rufuwa ta ɗauko ta lulluɓa tana jiran ɗaukewar ƙafar mutanen gidan. Tana nan kwance ta ji sanda Gambo yayanta, kuma tilon ɗan Auwwa ya shigo gidan. Tana jin sanda ya ɗauki abincinsa ya fita daga gidan, saboda shi ba ya kwana a gidan. Sannan tana jin sanda Auwwa ta gama cin nata abincin ta koma ɗaki ta kwanta. Sai da ta tabbatar da Auwwa ta wuce birnin sin a duniyar bacci, sannan ta saci ƙafa ta fito daga ɗakinta. Ta ɗauki takalmanta ta fita daga gidan. Sai da ta yi nisa da layinsu ta saka takalmanta. Sannan ta ci gaba da ɗingisa ƙafarta ta nufi unguwar Fanisau dake haɗe da unguwarsu. Dan ba wani banbanci tsakanin unguwar Fantai da Fanisau ɗin, kawai dai an raba unguwar ne. Kuma ita unguwar Fanisau ta fi unguwar Fantai kyawawan gidaje. Wani babban layi ta nufa. Inda ta tsaya a bakin gate ɗin gidan da ya fi ko wanne girma a layin. Tana hawayen famun ƙunan hannunta da ta yi ta ɗaga hannunta ta ƙwanƙwasa ƙaramar ƙofar shiga gidan. Tana tsaye a wurin ta ji muryar ne gadin gidan daga ciki yana faɗin. “Waye a nan?” Ta goge hawayenta tana faɗin. “Baba Habu Maimuna ce!” “Ah-ah! Maimunatu? Me ya faru?” Baba Habu ya buɗe ƙofar yana faɗa. Hasken fitilun dake ƙofar gida suka haske masa fuskarta. Ya dubeta yana mamakin abin da ya fito da ita da wannan daren. “Baba Auwwa ce ta ƙonani. Shi ne na zo wurin Mummy!” Ta faɗi tana nuna masa hannunta da ya ƙone. Baba Habu ya kama baki cike da tausayawa marainiyar Allahn yace. “Assha! Assha! An ya kuwa Auwwa tana so ta gama da duniya lafiya?” Ita dai bata sake ce masa komai ba, sai zubar hawaye da take. Saboda ji take ma kamar yanzu ta yi raunin. Baba Habu ya buɗe mata ƙofar tare da faɗin. “Shigo Maimunatu! Sannu!” Ta shiga cikin katafaren gidan tana ɗingisa ƙafarta ta hagu. “Ita kuma ƙafar me ya sameta?” Baba Habu dake rufe ƙofa ya tambaya. Sai ta tsaya tana faɗin. “Yau da safe na tashi tana min ciwo!” “Sannu kin ji” Sai ta gyaɗa kanta tana nufar cikin gidan. Da ƙyar ta iya buɗe ƙofar falon shiga cikin gidan, sannan ta shiga da sallama. Mutum ukun dake cikin falon suka amsa sallamar suna dubanta. Matar gidan Mummy ce da yaranta biyu, Sadiq da Maryam. “Mummy ina wuni” Ta gaidata tana durƙusawa. Cike da mamaki Mummy ta aje wayarta a kan sofa tana kallon Maimuna ƙawar 'yarta Maryam. “Lafiya kalau Maimuna. Me ya faru da hannunki?” Mummy ta tambaya tana duban hannunta na hagu da ta riƙe. Maimuna ta ja hanci tana faɗin. “Auwwa ce ta ƙona min hannuna, saboda na bayar da kunu bashi!” “Allah ya saka miki!” Faɗin Maryam tana nufar ƙawarta. Mummy kuma ta miƙe ta isa gaban Maimunan tana duban hannun nata, kasancewarta nurse a general hospital Haɗejia. “Mts ba zan iya treating wannan raunin naki ba Maimuna. Abin da za ayi gobe idan kin fita tallar safe, sai ki bawa wata daga cikin abokan tallar taki ta jire miki kayanki, ki je asibiti ki sameni a can!” Maimuna ta jinjina kai tana faɗin. “To Mummy. Na gode” Mummy ta ci gaba da kallon yarinyar cike da tausayawa. “Kin ci abinci?” Mummy ta tambaya tana kallon idonta da ya yi ja alamun tana jin yunwa. Maimuna ta sunkuyar da kanta ƙasa tana girgiza shi. “Maryam ki je ki zubo mata abinci” Mummy ta bawa Maryam dake dafe da kafaɗun Maimuna umarnin tana zaunawa. Maryam ta gyaɗa kai tana jan hannun Maimuna zuwa jikin kujera. “Zauna a nan na je na zubo miki” Maimuna ta zauna. Kuma da ma haka aka saba. Tun bayan fara ƙawancensu da Maryam ta fara zuwa gidan. Har ta kai ga ta saba da mahaifiyarsu da kuma yayan Maryam ɗin wato Sadiq. Kasancewar Mummy mace ce me tausayi ya sa take tallafawa Maimunan. Tun da ta fahimci cewa tana cikin matsatsin rayuwa. Hakan ya sa a duk sanda rayuwa za ta mata zafi babu inda take kai kukanta da ta wuce gidan su Maryam ɗin. Kakarta Hajja wadda ta haifi mahaifinta kuwa ta tsufa sosai, idan tana zuwa mata da ƙorafi a kan Auwwa zai iya sawa ciwon Hajja ta tashi ta hawan jini. Kawunta ƙanin mahaifinta kuwa ba sosai ta cika ganinsa ba. Dan idan ba gidan kakar tata dake unguwar Chadi nan kusa da Fantai ta yi ba, ba ganinsa take ba. A wasu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31