Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 5

Chapter 5

Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel – Maimuna’s Painful Story 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

gano wuri na ƙarshe da ta halarta kafin ta ɓata. Kuma abin da muke ta ƙoƙarin yia yanzu shi ne gano wanda ta haɗu da shi a wurin. Saboda mun gano wani saƙo a wayarta dake nuna cewa wani ne ya kirata zuwa wurin domin su haɗu. Daga zarar mun samu damar gane wanda ya aiko mata da saƙon za mu iya cewa mun kama me laifin. Saboda shi ne abin zargi na farko!” Mu'az da Faruk suka dubi juna a tare. Kafin suka kalli Muktar ɗin da ya gama zayyano musu bayanin. “Lord have mercy!” Faɗin Mu'az yana furzar da iska ta bakinsa. Yayin da Faruk da ya fi kowa shiga damuwa a kan case ɗin ne ya shafa kansa cike da damuwa. Saboda ɓatan abokiyar aikin nasu me suna Munira tashi ɗaya ya basu mamaki. Hakan ya sa suka bazama nemanta a ko ina. Bayan sati ɗaya da ɓatanta kuma suka samu labarin tsintar gawarta a wani layi. Babban abin tashin hankalin ma shi ne an tsinci gawar tata ne ba tare da wasu sassa na jikinta ba. Saboda tsabar yanda makashin ya bata wahala wurin kasheta ya sa su kansu ba su tabbatar da cewa gawarta ba ce sai da iyayenta suka zo suka tabbatar da cewa ita ce. Kuma tun bayan rasuwarta da Mu'az Faruk ba su huta a kan binciken wanda ya kasheta ba. “Ka yi haƙuri Kaigama. Da yardar Allah za'a kama mai laifin” Faɗin Mu'az a ƙoƙarinsa na kwantarwa da Faruk hankali. Ganin yanda suka fito daga headquartern duka a dame. Cike da damuwa Faruk ya dube shi yana faɗin. “Har yanzu na kasa mantawa da hoton gawarta da na gani a idona MJ. Kuma hoton tashin hankalin da ahalinta suka shiga lokacin mutuwar ya kasa fita daga kaina. Ba na jin hankalina zai kwanta idan har ban kamo me laifin nan ba MJ!” Mu'az ya dafa kafaɗarsa. “Insha'Allah za mu kamo shi!” “Allah ya yarda” MAIMUNA POV. Kamar yanda ta saba farkawa sassafe haka ta farka a asubar yau ma. Abu na farko da ta fara yi shi ne alwalal sallahr asuba. Ta dawo ɗakinta ta tada sallahr. Kuma bayan ta idar ta fita tsakar gidan ta fara aikinta na safiya kamar yanda ta saba. Duk da yanda sanyin safiyar yake sauƙa a kanta bata haƙura da aikin ba. To da ta isa ma ta haƙura da aikin?. Ita a wa?, Kare da gudun layya?. Sai da ta yi shara. Sannan ta wanke kwanukan da aka ɓata a daren jiya. Kafin ta zauna ta fara firar doyar da za ta dafa ta kuma soya domin kai wa makarantun safe dake kusa da su. A lokacin Auwwa ta fito daga ɗakinta tana hamma. Kanta ta ɗaga ta kalli Auwwan. Sannan ta gaisheta a ɗarare. A ranta take ƙiyasta lokacin da Auwwan ta tashi. Dan ta san lokacin dai ƙarfe bakwai za ta yi. Kuma ita ba ta isa ta tasheta a bacci ba. Saboda kyakkyawan warning ne daga Auwwan, kan kada ta kuskura ta tasheta idan tana bacci. A kan idonta Auwwan ta ɗauki buta ta yi alwala. Sannan ta shiga ɗaki domin yin sallah. Sai da a kammala fere doyar sannan Gambo yayanta ya shigo gidan. Kallonsa ta yi tana gaishe shi. Ko kallon arziƙi bata samu daga gare shi ba. Ballantana har ta yi zaton zai amsa gaisuwar tata. A tasowarta a gidan bata jin akwai rana ɗaya da suka taɓa yin magana da ɗan uwan nata ta minti biyar ta arziƙi. Ko kalo bata ishe shi ba ballantana har su samu damar yin hira. Kuma da ma shi ba zama yake a gidan ba. Kullum yana waje wurin abokansa masu hayar napep. “Ke Maimuna!” Auwwa ta ƙwala mata kira daga cikin ɗakinta bayan Gambo ya shiga ɗakin. “Na'am” “Ki yi maza ki ɗora ɗumamen tuwo yanzu. Gambo yace yunwa yake ji” “Auwwa na ɗora tukunyar doya fa” Tsautsayin shan zagi ya sa bakinta ya suɓuta wurin faɗar hakan. Ai ko an danƙaro mata zagin. Dan sai da Auwwa ta zaɓo wani zagi tun na zamanin maguzawa ta makawa uwarta dake cikin ƙasa. “...Gidana ko gidanki?. Da har zan ce ki yi abu ki kawo son ranki” “Allah ya baki haƙuri” Maimuna ta faɗi. Tana nadamar maganarta ta farko. Jiki na rawa ta sauƙe ƙatuwar tukunyar doyar da ta ɗora. Sannan ta ɗora ta ɗumame. “Kuma ki cire bayan tuwon da ya bushe” Ta ji Auwwa ta sake faɗi daga cikin ɗakin. “To” Ta amsa wani sashi na zuciyarta na farin ciki. Dan ta riga da ta san yau babu rabonta a ɗumamen nan. Kuma tun da Auwwa tace ta ɓare bayan tuwon tana nufin ta zubar bata so. To ita kuma da wannan damar take amfani wurin rage yunwar da take damun cikinta. Dan idan ta ɓare bayan wankewa take, sai ta ɗan saka yaji ta ci. Yau ɗin ma haka aka yi. Tana ɓarewa bayan tuwon shinkafar da ya bushe ta saka musu tuwon a cikin miyar dake kan wuta. Yayin da ta zube bayan tuwon da ya bushe a roba, ta wanke shi, tafaki ido ta zuba yaji a ciki. Ta koma gefe ta cinye. Sannan ta wanke robar ta aje. Ta dawo ta sauƙe tukunyar ɗumamen. Ta sanar da Auwwa cewa ɗumamen ya kammala. Kafin ta mayar da tukunyar doyar kan wuta. Tana zaune a wurin. Auwwa ta fito ta zuba ɗumamen a kwanika biyu, ɗaya nata ɗaya kuma na Gambo. Maimuna bata ta shi daga gindin murhun nan ba sai da ta gama dafa doyar, sannan ta soyeta da fulawa tas. Ta faɗawa Auwwa cewa ta gama. Auwwan ta zo ta zauna ta lissafa kuɗin doyar. Sannan ta saka mata a cikin bokiti fallasa. “Ta dubu uku da ɗari biyar ce. Saura kuma yau ma ki bada bashin” Faɗin Auwwa tana hararta. Maimuna ta gyaɗa kai tana nufar randa. “Ub*n me za ki yi kuma?” Ta juyo a tsorace tana faɗin. “Na ga hantsi ya fara ɗagawa ne. Shi ne zan zuba ruwa a bokita na aje a rana. Kafin na dawo daga talla na san ya yi ɗumi sai na ɗan yi wanka da shi!” Auwwa ta maka mata harara haɗi da jan tsaki. Sannan ta miƙe ta ja tulelen jikinta ta shiga ɗaki. Maimuna ta zuba ruwa a bokita. Ta aje a rana. Sannan ta shiga ɗakinta ta saka hijabina ta fito tana ɓoye kuɗin babur ɗin da Mummy ta bata. Ta ɗauki bokitin doya da fulawar ta fita. Kasancewar yau ƙafar tata bata ciwo ya sa ta isa makarantar Famfo goma da ta fi kusa da su da wuri. Dan a yankin unguwar tasu kusan makarantu shida ne. Kuma duk ciki babu wadda bata kaiwa tallahr doya da fulawa da safe. Tana isa makarantar ta wuce sashin da 'yan tallah ke taruwa a babbar makarantar ta 'yan mata. Kasancewar government school ce ya sa masu kawowa tallar kayan suke taruwa da yawa. A kusa da wadda ta fi sani cikin 'yan tallar me suba Rahina ta aje bokitinta. “Yau kin zo da wuri Maimuna. Dan sauraminti goma a fito tara” Faɗin Rahina. Mamuna ta yi murmushi. “Dan Allah Rahina so nake ki jire min kayana zan je asibiti a dubani!” Rahina ta dubeta.

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});