Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 10

Chapter 10

Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel – Maimuna’s Painful Story 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

miki ba. Ko sabulu kika siya kika wanke kayanki ai kin rage” Maimuna ta karɓi kuɗin hanu biyu, tana kallon kawunta da yalayen idanuwanta. “Na gode Kawu. Allah ya ƙara buɗi” Kawu ya yi murmushi. Sannan ya mata sallama ya ɗale kekensa ya nufi gida. Kasancewar tun bayan rasuwar matarsa bai sake yin wani auren ba ya sa yake zaune tare da mahaifiyarsu. A soro ya jingine kekensa, sannan ya yi sallama ya shigo cikin gidan. Inda ya iske mahaifiyarsu Hajja, zaune a tsakar gida, da alamun alwala ta yi, dan ga buta nan aje a gabanta. “Barau an dawo?” “Eh Hajja. Na dawo” Hajja ta miƙe tana faɗin. “To sannu da hanya” “Yauwwa Hajja” Daga haka ta shiga rumfar dake gidan, ta ɗauki hijabinta dake aje a kan sallaya. Ta saka ta tayar da sallah. Yayin da Kawu ya kama ruwa, sannan ya yi alwala ya fita masallaci. Sanda ya dawo Hajja na zaune a nan rumfar tsakar gidan tana jan carbi. Zama ya yi a kan kujera 'yar tsugguno yana jiran ta kammala. Kuma sai da ta kammala ɗin ya faɗi abin da ke bakinsa. “Hajja magana nake so mu yi a kan Me sunanki!” Hajja ta aje carbin hannunta tana tattara hankalinta gare shi, jin batun magana a kan tilon jikarta. “Me ya samu Maimunatun?” Cikin damuwa Kawu ya tsara mata abin da Auwwa ta yi wa Maimuna, sannan ya ƙara da. “... Ni Wallahi dan de kin ƙi ta tawa ne, tun yarinyar nan tana ƙarama na so ta dawo wurinki da zama, amma kika ce can shi ne dolenta, dan haka ba za ta dawo nan ta zauna ba, yanzu bayan talla da Auwwa ke ɗora mata har da su hukunci da wuta take mata, ya kamata mu yi wani abin a kan lamarin me sunanki Hajja. Ko da wannan cutar dake damunta aka barta ya isheta ƙaddara, ballantana a ƙara mata da izayar matar uba!” Hajja ta ci gaba da kallonsa har ya kai aya, sannan tace. “Barau! Ba wai na ƙi amincewa da shawararka ba ne. A'a, ni akwai abin da nake hangowa. Yanda Auwwa take da masifar son abin duniya za ta iya cinyewa wannan gidan. Bayan kuma shi ne kaɗai gadon da mahaifinsu ya bar musu ita da Gambo. Ina da tabbacin idan har Maimuna ta bar gidan nan Auwwa da ɗanta za su iya mallake mata gado. Kuma ko ba komai ɗa a gidan ubansa ya fi daraja, idan tana can ɗin ita kanta sai ta fi jin cewa a gidan ubanta take!” Kawu ya yi shiru. Can kuma yace. “A gaskiya Hajja ni na fara tunanin yi mata aure. Dan na lura da auren shi kaɗai ne zai kuɓutar da ita daga wanna baƙar azabar da take sha!” Hajja ta girgiza kanta. “Barau kenan! A auren yanzu masu lafiya ma ba auruwa suke da daɗin rai ba. Ballantana ita da take da jinya. Jinyar da iyaye ma kan guji 'ya'yansu idan suna ɗauke da ita, saboda gudun wahala, ballantana kuma miji. Kuma a irin auren yanzu ba na jin akwai wanda zai iya kula da Maimuna. Ka sani ba sai na nanata maka ba cewar cutar da Maimuna ke da ita na matuƙar bukatar kulawa. Kuma fa ni tun da nake da ita ban taɓa ji tace yau ga wani saurayi yace yana sonta ba, saboda kawai tana da sickler!” Hajja ta ƙarasa maganarta a raunane. Saboda tausayin jikarta dake ƙara kamata. Shi dai Kawu shiru ya yi kawai, dan a zahirin gaskiya ya fara gajiya da abubuwan da Auwwa takewa 'yar ɗan uwansa. Kuma yana ganin kamar lokacin da zai ɗauki mataki ya yi. MARIYA POV. Zaune take a kan kujerar falo. Ta saka Hilal dake wasa a cikin car toy ɗinsa a gaba tana kallo. Kamar ta samu tv, a hankali ta ciro yatsun hannunta biyu da ta cusa a cikin gashin kanta. Sannan ta gyara zamanta tana kallon yaron, sai kuma ta kai hannunta saitin da motar wasan nasa take. Sannan ta motsa hanun nata. Na take motar ta iyo gabanta kamar yanda ta motsa hanun nata. Kallon yaron ta ci gaba da yi, kamar yanda shi ma yake kallonta. Sannan a hankali ta ɗaga hannunta na dama, ta saka a cikin sumar kansa me laushi, sannan ta ciro gashin kansa da mugun ƙarfi. Amma kuma ko gezau yaron bai yi ba. Ya yi shiru kawai yana kallonta, hannunsa riƙe da rattle yana karkaɗawa. Gashin ta ɗaga tana kallo. A take ƙwayar idonta ta sauya kala zuwa ja. Sannan ta kalli Hilal, ta buɗe baki da shirin yin magana, fiƙoƙin haƙwaranta na sama suka ɗan ƙara tsayi kaɗan. “Na gode Hilal. Saboda da ban haifeka ba da ba zan zama ta hannun daman shugaban bayin shaiɗan ba. Ina sonka!” Ta ƙarashe tana shafa gefen fuskarsa. Shi dai kallonta yake kawai, kamar me fahimtar abin da take faɗi. Mariya ta janye hannunta daga kansa, sannan ta yi amfani da ƙarfin tsafinta ta tura car toy ɗin nasa inda take da. Ta miƙe ta fita daga falo, ta zagaya bayan gidan, sai ta tsaya ta waiga hagu da dama, sanna ta rufe idonta, ta ɗora hannunta a bayan wuyanta, inda tambarin ƙungiyarsu ta bayin shaiɗan ke zane a wurin. Sannan ta furta. “Mishk baksh hushk!” Bata kai ga rufe bakinta ba wani farin matashi ya bayyana a gabanta, sanye da jajayen kaya. Idonta ta buɗe ta kalle shi, sannan ta miƙa masa gashin Hilal. “Saƙo ne zuwa wurin Wahash!” Matashin ya karɓi silin gashin guda ɗaya. Sannan ya kalleta. “Saƙo zai isa ga shugaban bayin shaɗan!” Yana gama faɗin hakan ya ɓace ɓat kamar almara. Tunawa da cewar yanzu haka ta kusa zama ta hannun daman Wahash ya sa ta yi murmushi. Sannan ta saka yatsun hannunta biyu cikin bakinta, ta fito da reza sabuwa daga ƙasan harshenta. Cike da nishaɗi ta shiga juya rezar tana murmushi. Har ta koma falon ta zauna. Bata daɗe da zama ba wayarta ta shiga ringing, ganin Daddy ne me kiran ya sa ta ɗaga tana saita nustuwarta. “Barka da safiya Daddy. Ina kwana!” Ta gaida shi cikin sanyinta. Kuma cikin kamalarta dake burge kowa da ita. Daga ɗayan bangaren Daddy ya amsa sallamar, sannan ya faɗi abin da ya sa ya kirata. “Yau da daddare ina son ganinku ke da mijinki!” Ta tatare girarta wuri guda. Zuciyarta na raya mata ko dai Faruk ne ya je ya kai ƙararta?. Sanin zurfin ciki irin nasa ya sa ta kore wanna zargin, dan tana da yaƙinin cewa ba lalle ace ko Hajiyarsa ta sani ba ballantana Mu'az ya sani, har a je ga kan Daddy. “To Daddy, bari na sanar da shi” “A'a, ba sai kin yi hakan ba. Dan na faɗawa Mu'az ya sanar masa” Ta gyaɗa kanta. Daga haka suka yi salama. Tunani barkatai a ranta. Dan ta kasa hasaso dalilin da ya sa Daddy ke son ganinta ita da Faruk. *FCID (Force Criminal Investigation Department), Moshood Abiola Road, Garki, Abuja.* MUKTAR POV. “Wallahil azim da gaske nake muku yallaɓai!. Wallahi ba ni na kashe Munira ba!” Faɗin Mubarak saurayin Munira. Yayin da yake zaune a cikin ɗakin tuhuma na headquartern. Muktar da ya sa shi a gaba da tambayoyi, ya

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});