Chapter 15
Chapter 15
na so ka cika zurfafawa a tunani. Dan haka ka kwanta ka huta” Ta faɗa tana shafa sumar kansa. Yanzu ma bai musa mata ba. Kansa kawai ya gyaɗa sannan ya kwanta a kan gadon ba tare da ya sauya kayan da ya fita da su ba. Ba ta bar ɗakin ba sai da ta tabbatar da ya yi bacci. Sannan ta sumbaci goshinsa, ta miƙe ta fita. A yanzu ba ta shirya rabuwa da Faruk ba, saboda har yanzu tana sonsa, kuma bata jin za ta iya rabuwa da shi, sai dai idan har shugaban bayin shaiɗan ya buƙaci ta sadaukar da shi ne. To a nan fa ba makawa za ta bayar da shi. Amma yanzu dai kama bata shirya ba. (Aikin ɓirr! In ji tusa🧐) *Daga alƙalamin Salma Ahmad Isah✍️.* *CANDY CE🦋.* _Share fi sabillilah❤️_ ------------------------ _A halin yanzu mun yi rabin free pages, dan haka sai ku shirya domin fara biyan kuɗin littafi, tun da idan baku manta ba na ce muku isn't free._ _Ga duk wanda ya shirya biya, sai ya biya ₦300 to_ 5487270431 Salma Isah Monie point FCMB Shaidar biya kuma ta wannan numbern wayar. 08130172702. Ku tabbatar wannan tafiyar bata wuce ku ba, dan har yanzu ba ayi komai ba a tafiyar. #Candy °°°°°°°°°°°°°°°°°° *ƘADDARA CE!* *©SALMA AHMAD ISAH.* *CANDY🦋* _ArewaBooks @SalmaAhmad_ _Wattpad @Salma_Ahmad_Isah_ *06* *BB paradise hotel.* MUKTAR POV. Muktar da abokin aikinsa ne tsaye a gaban ginin hotel ɗin ‘BB paradise’. Binciken hanyar da Munira ta bi a sanda ta fito daga ginin hotel ɗin shi ne ya sa suka buga uban sammako. “Sir!” Muktar ya juyo ya kalli Ali, abokin aikin nasa da ya kirashi. “Me zai hana mu binciki CCTV camera footage ɗin wancan super market ɗin?. Ina ga kamar za mu iya samun wani abu” Muktar ya ɗaga kai ya kalli super market ɗin dake opposite da hotel ɗin. Kafin ya duba CCTV cameras ɗinsu dake saƙale a gaban ginin. Ba tare da yace komai ba ya nufi titi da nufin tsallakawa. Ali ya bi bayansa har zuwa cikin super market ɗin. Ko da suka shiga sai suka iske cewa babu ma'aikata sai masu aikin share wurin. “Barkanku da aiki” Mutum biyun dake aiki a wurin suka amsa. “Dan Allah zan iya ganin ma'aikatan wurin nan?” Suka dubi juna a tare. Kafin suka kuma dubansu. “Eh Abubakar manager ne kaɗai ya zo” Muktar ya gyaɗa kansa. “To ko zan iya ganin shi managern?” Suka kuma diban juna. Alamun dai basu yarda da su ba. Kuma su Muktar ɗin sun gane hakan. “Mu jami'an 'yan sanda ne... Za ku iya yarda da mu” Muktar ya faɗa yana nuna musu ID card ɗinsa. Sai a lokacin suka ɗan yarda da su kaɗan. Kuma da haka ɗaya daga cikinsu ya juya ya nufi ƙofar wani office. Jim kaɗan ya dawo tare da wani mutum, wanda da alama shi ne Abubakar managern. “Salamu alaikum” Faɗin Muktar yana miƙa masa hannu alamun su gaisa. Abubakar ya amsa yana miƙa masa nasa hannun suka gaisa, kafin suka gaisa da Ali. Sai ya ci gaba da kallonsu cikin rashin sani. “Ko zan iya sanin dalilinku na son ganina?” Ya tambayi tambayar dake rubuce a kan fuskarsa. Muktar ya yi murmushi. “Mu jami'an 'yan sanda ne. Kuma muna bincike a kan wani kisa da aka yi wata ɗaya da ya wuce. Binciken mu ne ya biyo ta kan super market ɗinku. Amma fa ba wai abin ɗaga hankali ba ne, taimakonku kawai muke buƙata!” “Allah ya sa za mu iya” “Da yardar Allah ma za ku iya. A ranar da aka rasa victim ɗin kafin a tsinci gawarta ta ziyarci wannan hotel ɗin dake opposite da super market ɗinku. Kuma da muka duba footage na ranar da ta ɓata ba mu samu komai ba. Hasali ma an goge duk wani footage na ranar. Dan haka muke buƙatar taimakonku. Ta hanyar nuna mana footage ɗin ranar da ta ɓata daga CCTV Cameras ɗinku!” Manager ya yi shiru kawai. Kamar ya yarda kamar kar ya yarda, kuma ba komai ya sa ya ji kamar kada ya yarda ba face jin batun ɓata da kisan kai. “Kaga Abubakar Sadik. Taimakon da za ka mana a wannan case ɗin shi zai sa mu iya kama mai laifin da ya kasheta. Idan har baka taimaka mana ba. Makashin zai ci gaba da yawo a cikin gari, kuma cikin kwanciyar hankali, tunanin cewa ya aikata wani kisa ba tare da an kamashi ba zai ƙara ba shi access na ƙara kashe wani. Kaga hakan ya bawa aikinsa damar ci gaba... Babu wanda ya san gobe, wata ƙila sai ka ga har ya faɗi kan wani naka!” Jikin manager ya yi sanyi. Kuma kalaman Muktar na hikima sun taɓa zuciyarsa. Dan haka ya gyaɗa kansa. Sannan yace su biyo shi zuwa CCTV control room. Shi da kansa ya binciko musu footage ɗin ranar da aka yi kisan. Kuma cikin taimakon Allah sai suka samu abin da suke so. Dan tun daga kan zuwan Mubarak hotel ɗin, da zuwan Munira duk sun gani. Kuma har fitar Munira daga hotel ɗin sun gani. Sannan a cikin footage ɗin suka ga wata baƙar mota ta fito daga hotel ɗin, ta bi bayan Munira. Footage ɗin na zuwa nan ya tsaya... “Daga wannan camerar ta 08 babu wata a gaba?” Muktar ya tambaya. Manager ya gyaɗa kai. “Eh, daga wannan babu wata camera!” Muktar ya gyaɗa kansa. Sannan suka yi wa Abubakar godiya suka fita daga super market ɗin. Jikin motarsu suka koma. Inda Muktar ya tsaya a jikin motar yana nazari. Ganin ya yi shiru ya sa Ali faɗin. “Sir! Yanzu mi ye abin yi na gaba?” “Dole muna buƙatar sanin mutanen cikin motar nan. Sannan bayanai a kan motar, da kuma wuri na gaba da Munira ta je bayan hotel ɗin nan...” Ya ja fasali yana saka hannayensa cikin aljihun wandonsa. Sannan ya juya ya kalli hanyar da suka ga Munira ta bi a footage ɗin da suka kalla. “Wata ƙila waccan kwanar ta kusa da me lemon can ta shiga. Wata ƙila kuma ta miƙe hayar nan ne har zuwa wurin da suka saceta. Wata ƙila kuma tun a sanda ta fito daga hotel ɗin nan suka saceta. Zargin ya taru ya min yawa Ali. Komai zai iya faru” Ya dakata yana rage girman idonsa. A lokacin da wata mata ta tsaya kusa da mai lemon da yake kan wata kwana. “Ali! Mu je” Yana faɗin hakan ya soma tafiya. Ali ya bi bayansa ba tare da neman ba'asi ba. A gaban rumfar me lemon suka tsaya. Sai da suka gaisa da shi sannan Muktar yace. “Baba akwai wani abu da ya faru wata ɗaya da ya wuce. Ban sani ba ko idan na maka tambaya a kai za ka iya tunawa!” Tsoho me lemo yace. “Eh to yaro. Yi tambayarka, idan na iya tunawa in amsa maka, idan kuma na gaza sai a ɗau haƙuri” “Allah ya baka ikon tunawa Baba. Wata ɗaya da ya wuce. A wata ranar asabat, da misalin ƙarfe shida na yammaci. Akwai wata matashiya, fara me ɗan siririn jiki, da ta zo wucewa ta nan hanyar!?” Baba mai lemo ya yi shiru yana son ya tuna. Can
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31