Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 8

Chapter 8

Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel – Maimuna’s Painful Story 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

fisu muƙami shi da Munira da suka fara zuwa a farko. Wani abu da ya ƙarawa abotarsu ƙarfi shi ne lokacin da aka yi posting kowwane a cikinsu sai aka turasu gari ɗaya. Da haka suka ci gaba da aiki tare har zuwa lokacin da ko wanne a cikinsu ya samu ƙarin girma. Da kuma nasarorin rayuwa. Kafin komai ya tarwatse a lokaci guda. Saurin aje frame ɗin ya yi, saboda hoton gawar Munira da ya haska a cikin idonsa. A hankali ya kwanta a kan gadonsa. Ya yi rigingine. Yana kallon p.o.p ɗin dake saman ɗakin. Hannunsa na dama ya dunƙule, sannan ya ɗora tsintsiyar hannun nasa a bisa goshinsa yana tunani. Can kuma sai yajuyar da kansa ya kalli makwancin Mariya a da. Kafin ta nemi raba ɗaki da shi. Ya ɗauke kansa yana tuna adadin lokutan da ya mata magana kan hakan. Amma sai tace masa ita bata da lafiya. Tun yana haƙuri har ya gaji ya daina mata maganar. Kuma babban abin da yake damunsa da ita shi ne rashin kula da Hilal da take. Kamar ba ita ta haife shi ba. A ganinsa ko da ba ita ta haifi Hilal ba in dai ya kasance ɗansa bai kamata ta masa irin ruƙon da take masa a yanzu ba. Cike da saƙe-saƙen goma da ashirin ɗin da suka haɗe masa bacci ya ɗauke shi. Amma bai kai ga barin Nigeria ba a duniyar baccin nasa kukan Hilal daga ɗakin Mariya ya tasheshi. Ya buɗe idonsa da ƙyar. Saboda bala'in baccin dake cin idonsa. Tun da ya fara aikin soja baya jin akwai ranar da ta zo ya rama tarin bashin baccin da ake binsa. Dan a ko da yaushe a gajiye yake dawowa gida. Idan kuma an tura shi wani aiki ne ma kwana yake idonsa biyu. Wani lokacin kuma sai ya samu baccin. Amma rashin baccin yana yawan damusa. Jin kukan Hilal ɗin ya ƙi ƙarewa ya sa ya miƙe zaune yana yin hailala. Ya saka takalmansa dake ƙasan gadon. Sannan ya fita daga nasa ɗakin ya shiga na Mariya. Ganin Hilal ɗin kwance a gefen Mariya yana kuka bai bashi mamaki ba. Dan ya ga abin da ya fi hakan ma. Shi dai a rayuwarsa bai san Mariya wata kala ba ce. Cikin ɗakin ya ƙarasa, sannan ya kai hannu ya ɗauki yaron da yake ta kuka har da hawaye. Ganin yana gwagwiuyar hannunsa yasa ya fahimci cewa yunwa yake ji. Dan haka ya zagaya ta ɗayan ɓangaren ya tashi Mariya a bacci. Duk da bata yi nisa a baccin ba amma da ƙyar ta buɗe ido ta kalle shi. “Mary Hilal yana ta kuka. Kuma da alama yunwa yake ji. Ki tashi ki shayar da shi.” Mariya ta mayar da idonta ta rufe, kamar ba za ta yi magana ba, can kuma sai tace. “Ka duba kitchen akwai kayan abincinsa sai ka dama ka ba shi idan kukan nasa ya dameka!” Cike da takaici Faruk ya girgiza kansa yana kallon yaronsa. Ɓacin rai ya sa bai sake cewa Mariya komai ba ya fice daga ɗakin. Ya nufi kitchen da Hilal ɗin a hannunsa, kuma har zuwa lokacin bai yi shiru ba. Shi kuma sai faman jijjiga shi yake alamun rarrashi. Da Allah ya taimake shi sai ya samu bottle ɗin Hilal ɗin akwai damammen custard a ciki. Shi ya ɗauka ya dawo ɗakinsa da shi. Ya shiga ba shi yana masa kallon tausayi. Dan yanda yake zuƙar bakin bottle ɗin da ƙarfi zai sa ka fahimci cewa yinwa yake ji. Hilal bai kai ga shanye custard ɗin ba ya yi bacci. Cike da tausayin ɗansa Faruk ya kwantar da shi a kan gadonsa. Dan ba yau suka fara kwana tare ba. Ɗan karamin ɗa da uwarsa a raye amma ya zama kamar maraya. Sanyin AC ya rage. Sanna ya ɗauki duvet ɗan ƙarami ya masa rufa. Kafin ya kwanta a gefensa yana kallonsa cike da so da kuma tausayi. Addu'a ya masa, shi ma ya yi, har Allah ya sa bacci ya sace shi. MU'AZ POV. “Mima ƙara min” Ya faɗa yana miƙawa Mima dake serving kowa na gidan dake zaune a dinning table, kasancewar suna shirin yin karin kumallo ne. Mima ta kalli plate ɗin da ya miƙo mata. Cike da mamaki ta karɓi plate ɗin. “Yanzu Ya Mu'az a ina zan ƙara maka wani abincin? Ji fa yanda plate ɗin ya cika da abinci, baka ci ba amma ka na neman ƙari!...” Wani kallo ya mata yana faɗin. “Miƙo min na coolern duka. Tun da ke baki da dabarar sauya plate!” Mima ta aje plate ɗin tana ɓata rai. Mu'az ya miƙe ya zagaya ta inda take yana faɗin. “Matsa ki bani wuri ko na sauya miki kammani yanzu!” Mima ta turo baki gaba tana matsawa. Ta kalli Mummy da ke kallonsu, dan wannan faɗan nasu sun saba yinsa kullum a kan abinci. Tun ana saka musu baki har kowa ya ƙyalesu da halinsu. Cikin ƙunƙuni Mima tace. “Mutum sai ci kamar gara!” Mu'az dake shirin zama a kan kujerar da ya miƙe ɗazu, bayan ya sauya plate ya cika shi da abinci ya kalleta. “Magana kika yi?” Mima ta sosa wuyanta tana faɗin. “A'a fa. Ni ban ce komai ba” Ta faɗi ƙwaƙwalwarta na faɗa mata amsar da zai bata. Dan tun ba yau ba sun saba, ta riga ya haddace kalmar kamar sunanta. Mu'az ya yi ƙwafa yana jan kujerarsa, tare da zaunawa. Sannan ya furta abin da Mima ke zaton zai faɗa ɗin. “Ƙaramar mara kunya!” Cike da mamakin halin yayan nata Mima ta yi serving Daddy. Ita ta rasa sai zuwa yaushe za ta girma a rashin kunyar nan. Kullum a ƙarama take, daga ta masa abu zai ce mata ƙaramar mara kunya, ko yace zai sauya mata kammani. Words ɗinsa ke nan. “Daddy zan iya ganinka a falonka?” Faɗin Mu'az yana miƙewa tsaye. Bayan da ya tashi plate ɗin da ya cika da boiled yam da kuma egg sauce daga aiki. Idan har abinci ya yi daɗi ba za ka samu ragowarsa a plate ɗin Oga me cika aiki ba. Daddy ya dube shi. “Maganar na buƙatar privacy?” “Yeah Daddy” Ya amsa yana wanke hannunsa a sink. Kafin ya juyo yana kallon Mummy dake kallonsa. “A kan mi ye?” Mummy ta tambaya. Kafin ya kai ga bata amsa Daddy ya amsa mata. “Ya ce maganar tana buƙatar sirri. Idan ba haka ba ai kin san da ya faɗeta a nan ko?” Mummy ta yi wa Mu'az kallon ban yarda da kai ba!. Kafin takalli Daddy ta taɓe baki tana juya spoon a cikin teacup ɗinta. “Mu'azzam ka je falon ka jirani. Yanzu zan kammala na zo” “Okay” Ya faɗi yana nufar ƙofar falo. Fita ya yi, inda ya bi ta compound ya nufi sashin Daddy. A falon farko ya zauna yana jiran zuwan Daddy. Kuma Daddyn bai jima ba sai ga shi ya zo. “Wace magana ce that needs privacy Mu'zzam?” Daddy ya tambaya while sitting. Mu'az ya gyara zamansa yana faɗin. “Daddy a kan Mariya da Faruk ne?” Naman goshin Daddy ya tattare wuri guda cike da mamaki, sannan yace. “Mariya da Faruk kuma? Me yake faruwa? Ko wata matsalar suka samu?” “Ban sani ba

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});