Chapter 18
Chapter 18
shiga kallon jama'ar gidan dake kaikawo. Duk yawan mutanen gidan, an rasa wanda zai amsa mata sallama sai Mama Sadiya. Wato matar Kawu Sani ta farko. Ba tare da tace ko ta yi komai ba ta wuce ɗakin 'yan matan gidan. Su huɗu ta samu zazzaune a ɗakin suna sabgarsu. Sallama kawai ta yi ta shiga cikin ɗakin. Kai tsaye ta wuce wurin da take aje kayanta, wato kusa da katifarta ta kwana. Jakarta ta sauƙe. Sannan ta zauna a bakin katifar tata tana jin yunwar dake cikinta na ƙara girmama. “Halima!” Zaliha 'yar Mama Sadiya ta farko ta kira sunanta. Hakan ya sa ta juyo ta kalleta. “Me yake damunki?” Ta shagwaɓe fuska kamar yadda ta saba. Sannan ta nuna mata gefen fuskarta. “Dubi ki ga abin da wani mugun soja ya min yau a boutique. Wai dan kawai mun yi karo fa shi ruwan da yake hannuna ya zube a jikinsa. Shi ne ya sharara min mari! Wallahi yanzu haka ma wurin ciwo yake min. Ji nake kamar ya karya min ƙashin fuska !” Ta ƙarashe ƙwallar shagwaɓa na zubo mata. Ta turo baki gaba. Tana jin kamar ta fashe da kuka. Da ace lokacin iyayenta na raye ne da yanzu wannan abin da ya mata ya sa ta kwanta jinya. Saboda a wancan lokacin ita 'yar gata ce. Shagwaɓiɓiyyar iyarta da babanta, saboda har suka koma ga mahaliccinsu ita kaɗai ce 'yarsu. Mahaifinta Alhaji Auwal Kaska ɗan kasuwa ne me arziƙi dai-dai gwargwado. Matarsa ɗaya, haka kuma 'yarsa ɗaya. Kasancewar tun bayan da aka haifi Halima ba su sake samun wani ɗan ba sai suka shagwaɓata. Gata babu kalar wanda ba su yi mata ba. Shi ya sa ta taso a shagwaɓe. Domin ko me ta nema za ta samu. Ba ta san babu ba. Shi ya sa a sanda Allah ya yi wa iyayenta rasuwa a lokaci guda ta shiga halin ha'u'la'i. Ba'a samu kanta ba sai bayan kwana arba'in da rasuwarsu. Kuma daga lokacin ne ƙalubalen rayuwarta ya fara. Saboda kaf cikin dangin mahaifiyarta babu wanda ya yi ƙoƙarin ɗaukanta dan ya riƙeta. Kowa yana gudun wahala. A cikin dangin mahaifin nata ma da ƙyar aka samu Kawu sani yace zai riƙeta. Saboda a lokacin an raba gado, dan daga ita sai shi ne kaɗai suka ci gadon mahaifinta. A sanda ta dawo wurinsa ya lallaɓata da daɗin baki ya ƙwace duk wani abu da aka mallaka mata ya cinye. Sai da kuɗaɗe da kadarorinta na hannunsa suka ƙare sannan ta fara fuskantar taskun rayuwa a gidansa. Dan gaba ɗaya Kawu Sani rikiɗewa ya yi ya sauya mata. A farkon zuwanta gidan ba ta cin abinci ɗaya da sauran iyalansa. Saboda ita ba ta saba da cin abinci mara kyau da daɗi ba, shi kuma taƙonsa ya sa gidansa babu kyakkyawan abinci. Amma bayan kuɗaɗen sun ƙare sai ita ma ta dawo tana cin abinci ɗaya da na yaran gidan. Sai kuma tsangwamar da matar Kawu Sani ta farko wato Mama Zulai ke mata. Aikin wahala babu wanda ba ta sakata, kowa na gidan ya rainta. Shi ya sa gaba ɗaya ta tsani rayuwar gidan. Idan ta tuna da yankan ƙaunar da mutuwar iyayenta ta mata. A rayuwar Kawu Sani, idan kana da kuɗi kai ne mutum. Shi ya sa gaba ɗaya 'ya'yansa mata suke fita domin nemo masa kuɗi. Wasu ma ta hanyar da bata dace ba suke samowa kuɗin. Amma shi bai damu ba, in har za'a kawo masa kuɗi to su bi kowace hanya ma. To Halima bata shiga tara ba sai da Kawu Sani ya bijiro mata da zancen dole ta fara fita neman kuɗi kamar sauran 'ya'yansa. A lokacin ta sha kuka sosai, duk da da ma can ita kuka ba ya mata wahala. Sai dai ta riga tasa a ranta cewa ba za ta taɓa yin abin da su Jidda babbar 'yar Mama Zulai ke yi ba, na bin maza domin samun kuɗi. Shi ya sa ta naimi taimakon Zaliha kan ta tayata naiman aiki. Shi ne har ta samu aiki a Ummul Banat boutique. To da wannan aikin ne take samun kuɗin da take bawa kawu Sani, dan ta samu ta zauna a gidansa. Amma duk da haka ba ta da kwanciyar hankali, saboda masifar Mama Zulai ba ta barinta ta huta. “Ayya. Sannu, kuma wurin ya yi ja sosai, bari in shafa miki man zafi!” Faɗin Zaliha cikin tausayawa. Halima ta gyaɗa kai tana jin tausayin kanta, saboda yanzu haka ma kanta ciwo yake. Zaliha ta miƙe ta nufi jakarta ta kaya, ta ɗauko man zafin. Sannan ta dawo ta zauna kusa da Halima, ta shafa mata a gefen fuskar tata da ya kumbura. “Kin yi sallah?” Zaliha ta tambaya. Halima ta gyaɗa mata kai a shagwaɓe. “To Mama ta kusa gama girki, idan ta gama sai na zubo mana mu ci” Ta kuma gyaɗa kai, sanna ta kwanta tana jin kanta na ƙara mata ciwo. Idonta ta lumshe, fuskar wannan mugun sojan ta shigo cikin tunaninta, dan haka ta yi saurin buɗe idonta gabanta na faɗuwa. Dan haka kawai take ganinsa kamar wani dodo. Ƙwafa ta yi, sannan ta cije leɓenta na kasa. Ta juya kwanciyarta tana ja masa Allah ya isa. “Insha Allah ba za ka samu sukuni ba tun da ka ɗaga hannunka ka mareni. Mugu me jar fuska kawai... Banza ƙatoto!” Ta faɗi a zahiri, zuciyata na zafi da abin da ya mata. Kamar daga sama ta ji Mama Zulai na ƙwala mata kira. “Ke Halima!. Halima!” Idonta ta rintse. Ko wani ɗan ƙaniyar ne ya faɗawa wannan masiffafiyar matar ta dawo?. Miƙewa ta yi zane, tana faɗawa zuciyarta cewa yanzu za'a haɗata da wani aikin. Ba'a barta ta huta da gajiyar da ta kwaso a wurin aiki ba, an zo za'a ƙara mata da wani aikin. Tana tura baki gaba tana shagwaɓe fuska ta ɗaga labulen ɗakin da suke ciki, tana amsa kiran 'yan farautar da Mama Zulai ke mata. Tsaye ta hangeta a bakin rumfar da ake girki a gidan. Ta haɗe girar sama da ta ƙasa, tana mata wani kallon tara saura kwata. “Ub*n me kika shiga yi a ɗakin?. Bayan kin san cewa yau girki na ne?” ‘Aikin ƙaniya na shiga yi a ɗakin. Masifaffiya kawai! Ni na saki yin girkin dole?, Da za ki zo ki takurawa rayuwar marainiyar Allah?. Muguwa Azzaluma’ Ta yi maganar duka a zuciyarta. A fili kuma sai wani tsuke baki take tana rau-rau da ido. Tana wani karkata kai, wai duk dan a ji tausayinta. Amma ta san ba za'a ji tausayi nata ba. Tana yi ne kawai dan ya zame mata jiki. “Ki fito ki zo ki ƙarasa tuƙa tuwon nan... Kuma in kin gama ki rabawa yara... Mtsuww!” Mama Zulai ta ƙarashe da tsaki. Sannan ta juya zuwa ɗakinta. Jiki a saɓule Halima ta fito daga ɗakin. Tana tafe hawaye na mata zuba. Tana shirin zama a gaban murhun dake ɗauke da tukunya lamba goma. Mama Sadiya ta fito daga ɗakinta tana faɗin. “A'a me sunana. Ta shi ki je ki kwanta ki huta. Ni zan tuƙa tuwon!” Halima ta girgiza kai. Sannan ta zauna a kan kujera tana faɗin. “Ba komai Mama. Zan yi” “Da dai kin kawo na tuƙa”
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31