Chapter 7
Chapter 7
sanar da ku cewar lokacin sadaukarwa ya kusa. Dan haka sai ku shirya domin sadaukar da ɗaya daga cikin waɗan da kuke so ga shugabanku shaiɗan. Sannan kuma ku sani cewa duk wanda ya kuskura ya tsallake sharuɗanmu to zai mutu, kamar dai yanda Kunda ya mutu. Duk wanda muka nuna cewa shaiɗan na so a cikin ahalinku, dole a sadaukar da jininsa. Ƙin amincewa da hakan na nufin barin mutum duniya. Dan za ku mutu ku je ku faɗa wuta tare da shaiɗan!” (Wa'iyazubillah.!) “Mun ji mun amince shugaban bayin shaiɗan!” Suka amsa da babbar murya. Ciki har da RAZOR. “Sai kuma batu a kan wanda zai maye kujerar Kunda!...” Sai ya dakata yana kallon Razor da ta maida hankali kansa. “Razor!” Razor ta zabura ta miƙe tsaye, daga ciki ban da tsallen murna babu abin da zuciyarta ke yi. Dan da alama mafakin da ta ci burin cimmawa ne ya zamto gaske. Mafarkin da ya samu muhalli a cikin rayuwarta tun bayan mutuwar Kunda na hannun daman shugaban bayin shaiɗan. Wato maye kujerar Kunda ɗin. Shugaban bayin shaiɗan me suna Wahash ya kalli sauran bayin shaiɗan, sannan ya nuna Razor da hannunsa yana faɗin. “Razor ita ce wadda za ta maye wurin Kunda!” Cike da farin cikin wannan batu na Wahash Razor ta zube ƙasa, ta yi wa wutar shaiɗan sujjada tana masa godiya. Kafin ta miƙe tana yi wa Wahash godiya. “Amma kafin faruwar hakan, dole ki sadaukar mana da ɗanki Haruna Faruk Kaigama. Hilal nake nufi!” Wahash ya faɗi abin da suke buƙata a maimakon wannan kujera. Ba tare da tsoro, shakku, ko ɗar ba Razor ta amince cike da farin ciki. Ta sadaukar da abubuwa da dama kafin ta kawo yanzu. Na farko sai da ta fita daga musulunci, dan sam a yanzu bata sallah ballantana azumi a watan ramadan, ko wata ibada da ta kasance wajib a kan ko wani musulmi na mai imani. Sannan ta sadaukar da mahaifarta bayan ta haifi Hilal. Ta kuma ƙauracewa haɗa shimfiɗa da mijinta tsawon shekara guda duka a kan wannan ƙungiya. Abubuwan da ta sadaukar ba za su ƙirgu ba. Dan haka ko da mahaifinta Alhaji Jibrin Gimba Gashuwa GG suka buƙata za ta sadaukar da shi, ballantana Hilal ƙaramin alhaki. Da wannan batun taron nasu ya waste. Amma kafin Razor ta tafi sai da suka yi tattaunawar sirri ita da Wahash. “Razor!” Ta kalle shi cikin girmamawa. “Mun gano cewa mijinki da yayanki suna bincike a kan mutuwar Munira abokiyar aikinsu da kika kashe. Sakamakon ganinki da ta yi a lokacin da muka aikeku ku kashe Kunda a BB Paradise hotel!” Nan take yanayin bugun da ƙirjinta yake ya sauya salo. Daga na farin ciki zuwa na tashin hankali. Daga Mu'az har Faruk babu wanda ta yi wa ƙaramin sani. Ta san halinsu kamar yunwar cikinta. Idan har suka gano gaskiyarta ba za su yi la'akari da alaƙarta da su ba za su hukuntata. Ganin kamar ta tsorata ya sa Wahash faɗin. “Babu buƙatar ki ɗaga hankalinki. Domin mun yi wa tufkar hanci, ta hanyar goge duk wani CCTV footage na ranar da kuka haɗu da Munira a hotel ɗin!” Idonta ta lusmhe tana jin bugun zuciyarta na dai-daita. Sannan ta buɗe idon nata. “Wahash yaushe zan sadaukar da Hilal ɗin?!” Ta tambayi abin da ya fiye mata muhummanci. Dan ita a yanzu babu abin da take buƙata da ya wuce maye kujerar Kunda. Kuma ita ta ƙagu ta sadaukar da Hilal ta huta. Tun da da ma shi da ubansa duka ba sa gabanta. Wahash ya goya hannayensa a bayansa yana murmushi. “Me kike ci na baka na zuba Razor?. Ai daga zarar lokacin ya yi za mu sanar da ke. Yanzu dai abu ɗaya nake buƙata daga gareki. Shi ne gashin kansa, domin ba za mu sadaukar da jininsa ga shugabanmu shaiɗan ba ba tare da mun tsaface shi ba. Dan haka sai kin jira nan da wasu wattani!” Duk da ba haka ta so ba ta ji daɗi. Da wannan batu ta yi wa Wahash sallama, sannan ta dawo gidanta, cikin ɗakinta. Kuma tana dira a ɗakin Hilal ya zabura ya farka, lokaci guda ya canyara kuka. Amma ko ajikinta an mintsini kakkausa. Dan bathroom ma ta shiga. Ta je ta yi wanka ta dawo ta sauya kaya ta kwanta a kan gadon tana kallon Hilal ɗin dake kuka har zuwa lokacin. Kallonsa da ta yi ya motsa wani abu a cikin zuciyarta. Musamman ma da ta tuna cewa nan da wasu watanni za ta sadaukar da shi ga abin bautarta a yanzu, wato shaiɗan. (Ya ilahi!) Tausayinsa ta ji ya fara shiga zuciyarta, dan haka ta kai hannu za ta taɓa kansa. Amma sai wannan baƙin hayaƙin da ya saba rufe mata ido a duk sanda za ta tuna wani abu na soyyaya tsakaninta da Faruk ko ɗansa ya rufe idonta. Lokaci guda hannunta na dama da ta ɗaga za ta ɗora a kan Hilal ya ƙame a saitin kan nasa. Ƙwayar idonta ta juye zuwa ja. Sannan lokaci guda fushi ya maye fuskarta. Sai ta yi saurin janye hannunta daga kansa. Sannan ta juya masa baya tana huci kamar wadda aka ɓatawa rai. Lokaci guda idonta ya soma zubar da hawayen jini. Ta rintse idonta gam tana karanto wata addua'a tasu ta bayin shaiɗan. Har ta samu ta yi bacci. FARUK POV. Da misalin ƙarfe goma na dare ya fito daga banɗaki. Bayan ya watsa ruwa a jikinsa kasancewar bai jima da dawowa daga wurin aiki ba. Sanye yake da yellow plain T-shirt da baƙin sweat trouser, ƙafafunsa duka na sanye cikin baƙin sliders ɗinsa. A hankali ya kai hannu ta taɓa sumar kansa da take a jiƙe, wadda kuma bata cika tsayi ba kasancewarsa soja ya sa ba ya tara gashi ko da ya so hakan. Shi yasa yake askin high fade tare da buzz cut. Yana shirin kashe hasken dake ɗakinsa, idonsa ya sauƙa a kan wani hoto dake cikin kyakkyawan frame. Wanda ya ƙunshi Mu'az da Munira da kuma shi kansa. Zama ya yi a gefen gadonsa. Ta inda hoton ke aje a kan side drawer. Ya kai hannu ya ɗauki hoton yana kallo. Gaba ɗaya su ukun na sanye cikin korayen kaya ne na sojoji, kuma sai kayan dake jikin nasu ya tuno masa da lokacin da aka ɗauki hoton. Wato ranar da suka yi passing out. Domin NDA Kaduna (National Defense Academy Kaduna) suka fara haɗuwa da Munira a wurin training. Ƙwazonta da kuma nuna jarumtarta duk da kasancewarta mace 'yar arewa yasa suka ƙulla abota da ita. Alaƙarsu da Mu'az kuma ta fara ne tun daga secondary school. Har suka kai ga tertiary school suna tare, kuma burin kowwane a cikinsu tun a wancan lokacin shi ne zama soja. A sanda suka kammala karatu mahaifinsa Alhaji Haruna Aminu Kaigama yana da rai. Kuma shi ne wanda ya nema musu makarantar horar da sojojin ta NDA. Kasancewar Hajiya Batula mahaifiyarsa bata da matsala da aikin da yake son yi sai ya riga Mu'az tafiya. Saboda shi Mu'az Mummynsu bata son ya yi aikin soja. Shi ya sa sai da aka kai ruwa rana kafin ta amince ya tafi. Amma duk da haka sai ya zo ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31