Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 26

Chapter 26

Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel – Maimuna’s Painful Story 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ta murɗe hannun har sai da Vishal ya yi ƙara. Sannan ta sa ƙafarta ta daki ƙafarsa. Kafin ta sa hannunta ta riƙo gashin ƙeyarsa, ta ɗaga ɗaga kansa sama yana kallonta. A hankali ta kai hannunta da bata riƙe gashin kansa da shi ba, ta ɗaga harshenta kaɗan, ta ɗauko wata sabuwar reza da har ɗaukan ido take a cikin hasken ɗakin. Ta ɗaga sama, sannan ta yanka wuyan Vishal da ita. A dai-dai lokacin Munira da ta fito daga ɗakin Mubarak da gudu ta dakata a ƙofar ɗakin. Ganin an yi kisan kai ya sa ta ƙwaka ihu. Ihun da ta ƙwala ya sa Mariya da Lawan juyowa suka kalli bakin ƙofar. Ganin fuskar Mariya ya sa tsoro da tashin hankalin Munira ninkuwa. Hannunta na rawa ta nuna Mariya da shi. Sannan ta kalli gawar Vishal dake ƙasa. Ita ma Mariyan ta ganeta. Kuma ganetan da ta yi ya sa ta nufo bakin ƙofar ɗakin da gudu. Ita ma Munira sai ta ranta a na kare. Ta fita daga hotel ɗin a kiɗime, ko motarta da ta zo da ita bata ɗauka ba. Ganin ta fita ya sa Lawan da Mariya bin bayanta a mota. Amma saboda ta iya gudu sosai ya sa ta musu nisa. Dan har wayarta ta ɗaga ta kira Faruk da ita. Sai dai kafin ta kai ga faɗa masa abin da ke bakinta tunaninta da komai nata ya tsaya cak. Har Mariya da Lawal suka ɗauketa bata cikin hayyacinta... ~~~ Munira ce yashe a tsakiyar wani ɗaki. Hannunta da ƙafarta duka a ɗaure. Sannan idonta a rufe. Idan ka kalleta ba ka ce tana numfashi ba... Daga wajen ɗakin aka turo ƙofar ɗakin ciki, ƙaran buɗewar ƙofar ya sa ta motsa. A hankali kuma sai ta shiga buɗe idonta. Tun tana gani dishi-dishi har ganinta ya dawo dai-dai. Shiru ta yi tana kallon Mariya da ta shigo ɗakin. Da ƙyar ta iya yinƙurawa ta miƙe zaune, duk da ƙafafuwanta da hannayenta a ɗaure suke. A dai-dai lokacin kuma Mariya ta durƙusa a gabanta tana murmushi. Yayin da ita kuma Munira take zubar da hawayen tausayin abokanta. Saboda ita bata ta kanta. Dan ta san ba lalle ta tsira a hannunsu ba. “Mariya me ya sa?. Me ya sa kike cutar da Faruk da kuma MJ? Me ya sa?” Ta tambaya hawaye na ƙara zubo mata. Amma ita Mariyan ba ta yi magana ba. Sai murmushi da take. Duk da haka Munira ba ta haƙura ba ta sake faɗin. “Me zai sa ki kashe rai Mariya?. Mariya me zai sa ki zaɓi rayuwar da ba taki ba?...” “Wa ye yace miki wannan rayuwar ba tawa ba ce?. Wannan rayuwata ce, rayuwa me daɗi a ƙarƙashin gata da tallafin shaiɗan!” Mariya ta katseta tana faɗaɗa murmushinta. Munira ta yi shiru tana son gano inda zancen nata ya dosa. “Mariya ke 'yar cult ce?” Mariya ta lumshe idonta ta buɗe tana gyaɗa kai, hankalinta kwance. “Ƙwarai kuwa Captain Munira Musa. Na bayar da ruhina ga shugaban mu shaiɗan. A yanzu ba ni da abin bauta sama da shaiɗan!...” “Subhannallah! Subhannallah!. A'uzubillah! A'uzubillahi mina shaiɗanir-rajim!” Wani duka da Mariya ta kaiwa bakinta ya sa ta faɗi gefe guda. Bakinta na zubar da jini. Mariya da fuskarta ta rikiɗa zuwa fushi ta sa hannu ta ta riƙo gaban rigar dake jikinta. Sannan ta janyota tana zare idonta a kanta. “Idan kika kuskura kika sake buɗe bakinki kika faɗi wata ƙazamar kalma ɗaya a kan abin bautata shaiɗan sai na cinye namanki ɗanye!” Bakin Munira na fitar da jini, idonta na zubar da ƙwalla ta girgiza kai. “Ba ke ba ce Mariya!. Wallahi ba ke ba ce. Kowa ya na yabon kyan hali irin naki, kina da nutsuwa da kamala. Kina da sanin ya kamata da haƙuri, me ya sa yanzu kika sauya? Me ya sa? Innalillahi wa inna ialaihi raji'un!...” Mariya ta saki gaban rigar tata. Sannan ta miƙe ta fice daga ɗakin a fusace. A wani ɗaki ta je ta samu Wahash. “Shugaba! Wani kalar hukunci ya kamata mu mata?” Mariya ta tambaya tana huci. Saboda an taɓa abin bautarta. Wahash ya dubeta. (Wahalallu😒) “Yanzu kun kashe Kunda (Vishal). Kuma za'a yi bincike a kai. Idan har aka kasheta ita ma zargi ne zai ƙara yawa. Dan haka dole mu jinkirta wurin kasheta!” Mariya ta jinjina kai. “Dole mutuwarta ta zama me tada hankali. Saboda ta taɓa abin bautarmu Wahash” Wahash ya yi murmushi. “Zamu ba ta irin mutuwar da hatta ahalinta ba lalle su ganeta ba” Mariya ta jinjina kai. Kamar yanda suka tsara ba su kasheta a lokacin ba. Sun ajeta a masarautar shaiɗan na wasu satuka. Kuma a duk kwanan duniya da kalar azabar da ake ganawa Munira. Da haka har lokacin da za su sadaukar da jininta ga shiaɗan ya zo. Sai da suka mata kisa irin na wulaƙanci. Kisan da duk wani me imani idan ya gani sai ya zubar da hawaye. Sun bata mutuwa irin wanda ko da fasiƙin mutum ne ba'a so ya yi. Haka suka cillar da abin da ya yi saura na gawarta a wata unguwa. Hankalinsu kwance... *Present Day...* MUKTAR POV. Kamar kullum. Yau ma haka Ali ya sauƙe shi a unguwarsu. Sannan ya juya ya tafi da motar tasa. Saboda shi sam ba ya zama da motar a wurinsa. A ko da yaushe tana wurin Ali. Sai idan yana buƙatar zuwa wani wurin shi kaɗai zai sa Alin ya kawo masa ita. Kamar jiya. Haka yau ma aka dalle shi da hasken fitilar mota, saɓanin jiya da ya kasance mashin. Cak ya tsaya da tafiyar da yake. Sannan a hankali ya juya bayansa ya kalli motar dake bayansa. Duk da yanda aka haske shi da fitilar motar ya iya gane motar, har ma da mutum biyun dake cikin motar. Wannan motar ce da aka sace Munira a cikinta, sannan Mariya da crime partner ɗinta da ba su san sunansa ba ne zaune a ciki. Kamar yanda yake tsaye haka ma motar tasu take tsaye a wuri ɗaya, duk da a kunne take. A hankali ya ja ƙafarsa ɗaya baya. Hakan ya bawa Lawan damar jan motar ma zuwa gaba kaɗan. Ganin haka ya sa Muktar ya sake jan ƙafarsa baya, Lawal ma ya ƙara jan motar gaba. Muktar ya juya bayansa. Sannan ya ci gaba da tafiya a nutse, saboda ya ga abubuwan da suka ɗara wannan tayar da hankali. Ƙarewa har kan gadon baccinsa an zo an saka masa wuƙa a wuya an yi barazanar kasheshi. To ai su su Mariya ƙananun 'yan iska ne. Kamar yadda yake tafiya a hankali, haka ma motar ta ci gaba da binsa a hankali. Can kuma sai ya fara tafiya da sauri, hakan ya sa Lawan ma ƙara gudun motar. Ganin haka ya sa Muktar ya fara gudu. Lawan ma ya taka motar da gudun bala'i. Kuma ba'a je ko ina ba ya buge Muktar da motar. Ya faɗi ƙasa, hatta daƙaran da ya yi sun ji shi da Mariya. Kuma ya na buge shi sai ya tsayar da motar. Mariya ta dube shi. “Ka taka shi ka bi ta kansa mana” Ya kuwa taka motar, har sai da suka ji motar ta taka shi. Sannan suka ja

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});