Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 24

Chapter 24

Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel – Maimuna’s Painful Story 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

sun koma ɗin. Amma a wanan karon da shirinsu suka tafi, ta yanda ko da za'a kawo musu hari za su iya kare kansu. Amma kuma rasa makama ya sa shi da Ali yin cirko-cirko a cikin layin da Munira ta bi sanda motar nan ta biyota. Saboda tun da suka shigo ba su ga wani me tallah ko me abin siyarwa ba. Hatta da masu wucewa sai dai ka gansu jifa-jifa. Shi ya sa ya faɗawa kansa cewar dole ne ma a sace mutum a wannan layin, saboda babu zirga-zirga a layin. Sai dai idan har Allah ya hukunta faruwar abu a lokaci, to ba makawa sai ya faru. Dan har sun riga sun cire rai da samun wani abu. Sai Allah ya jefo da dalilin tonuwar asirin da suka daɗe da son ya tonu. Saboda a sanda suke da niyyar juyawa su koma inda suka fito. Muktar ya yi arba da wata mabaraciya ta shigo layin. Hakan ya sa ya yi wa Ali magana kan ya tsaya. Tsayawar suka yi. Kuma a kan idonsu matar ta tsaya a jikin wata bishiya. Ta shimfiɗa buhu, ta zauna a kai, sana ta aje wani kwano a gabanta ta fara barar da ta saba yi kullum a layin. Muktar bai san sanda murmushi ya suɓuce masa ba. “Ali mu je” Yace kawai. Sannan ya nufi wurin matar. Ali ya bi bayansa kamar kullum, zuwa jikin bishiyar da matar ke zaune a ƙarkashinta. Har ƙasa suka durƙusa suka gaisheta. Sannan Muktar ya fara tambayarta. “Iya. Mu jami'an 'yan sanda ne. Kuma muna bincike a kan ɓatan wata matashiya. A cikin binciken mu mun yi karo da wani bayani da yace an ga sanda ita wadda aka sace ɗin ta shigo layin nan. Dan haka muke so mu tambayeki ko kin ga sanda ta shigo!” Iya me bara ta jinjina kai. Sannan tace. “To yaro, faɗa min rana da kuma lokacin da aka ga ta biyo ta nan ɗin. Idan zai iyu ma ku faɗa min har da kalar tufafin jikinta. Saboda idan har nan layin ta iyo to tabbas zan ganta. Dan ni nan da kuka ganni kullum nan nake zama ina bara, sai dai idan da magariba ko da sassafe ta shigo layin. To shi ne dai ba zan sani ba!” “To Iya. Yanzu za'a iya kaiwa kimanin wata ɗaya da kwanaki da faruwar abin. Kuma ranar asabat ne da yamma. Sannan tana sanye da jallabiya kalar ruwan goro. Haka fara ce, me ɗan siririn jiki!” Muktar na kaiwa aya Iya me Bara na buɗe bakinta. “Ƙwarai kuwa yara. Na ga sanda ta wuce ta nan. Kuma ka ga can...” Ta ɗan yi fasali tana nuna musu ƙofar wani gida, Muktar da Ali suka juya suka kalli gidan, sannan suka sake kallonta a tare, sanda ta ci gaba da faɗin. “... A ƙofar gidan can wata baƙar mota ta tsaya. Wasu mutum biyu mace da na miji da baƙaƙen kaya suka fito daga ciki, sannan suka ɗauketa suka jefa cikin motar!... Ni kuma ganin hakan ya sa na tsorata, shi ya sa na yi gum da bakina ban taɓa faɗawa kowa ba” “To iya shin kin iya ganin fuskokin waɗan da suka ɗauketa?” Muktar ya tambaya da sauri. Iya me bara ta girgiza kanta. “A'a. Ban gani ba. Amma ranar da aka saceta akwai wani matashi ɗan can gidan da shi ma ya ga sanda suka saceta, kuma har hoto me motsi ya ɗauke su a wayarsa. Da yace zai faɗawa 'yan sanda, amma sai mahaifinsa ya hana shi!” Muktar da Ali suka dubi juna. Sannan suka jinjina kai a tare. “Iya me nene sunan matashin?” “Audil” Iya ta amsa. Yanda ta kira sunan Audil ɗin instead of Abdul ya sa su yin dariya. Kafin Muktar ya ɗebo kuɗi ya bata. Har suka bar wurin tana saka musu albarka. A ƙofar gidan da ta nuna musu suka tsaya. Ali ya yi sallama. Sannan suka tsaya jiran fitowar masu gidan. Da farko mahaifin Abdul ɗin ne ya fito. Sai da suka masa bayanin abin da ke tafe da su, sannan ya kira Abdul ɗin. Ya saka su a gaba yana son ganin abin da zai faru. Dan ko sama da ƙasa za su haɗe ba zai bari su tafi da ɗansa headquarter ba. Idan videon suke son kallo shi bai hana ya nuna musu ba. Za ma su iya turawa a nasu wayoyin, amma su tafi da ɗansa shi ne abin da ba zai lamunta ba. “Abdul. Idan har ka san kana da videon nan a wayarka. Ka daure ka nuna mana. Saboda idan har ba ka nuna mana ba rayuwar sauran al'ummar gari tana cikin haɗari!” Abdul da ya sunkuyar da kansa ya ɗago ya kali babansa. Wanda ya harɗe hannaye a ƙirji yana kallon kowa cikinsu. Sannan ya kalle su. “Idan da akwai a wayarka ka nuna musu. Ni ban hana ba, amma fa daga nan babu inda za ka ƙara ɗaga ƙafarka. Ba zan bari ka tafi ko ina ba Wallahi!” Faɗin baban Abdul. Kuma kalamansa suka sa Abdul ya sa hannu a aljihun wandon jikinsa. Ya ɗauko wayarsa ya cire password. Sannan ya nemo videon a inda ya ɓoye. Ya kunna, ya miƙawa Muktar. Muktar ya karɓi wayar da dukkan zumuɗin duniya. A zatonsa zai ga abin da zai kawo ƙarshen matsalar ne. Bai sani ba cewa yanzu ne ma matsalar za ta soma. Saboda tonuwar asirin makashin ba ya nufin zuwan ƙarshen matsalar. Sai dai ma ya zama wani sabon mafarin tarin matsaloli. Da farko da ya ga videon da fuskar macen dake cikinsu bai yarda ba. Sai da ya dawo da shi baya ya sake kalla, ya sake sakewa, wai dan ya tabbatar da abin da yake gani ko gaskiya ne. Duk da sau ɗaya ya taɓa ganin matar Faruk ya ganeta. Saboda kwanaki da yake ta neman layin Faruk ɗin ba ya samu ya sa ya tafi gidansa. Kuma a nan ya fara ganinta. Duk da ba wai ya tsaya ya ƙare mata kallo ba ne a wancan lokacin ya ganeta a nan. Kuma idan zai iya tunawa, Faruk ya sanar da shi cewar Mariya matarsa ƙanwar Mu'azzam Gimba ce. Kuma ya san waye Alhaji Jibrin Gimba Gashuwa GG. Mutumin arziƙi me halin ƙwarai. Me dattaku da halin girmamawa ga naƙasansa ba ma ga wanda ke samansa ba. Lalle akwai magana!. Yanzu me zai sa matar soja. Ƙanwar soja, 'yar babban mutum kamar GG ta aikata garkuwa da ɗan adam, da kuma kisan kai?. Gaba ɗaya ya kasa ganewa. Idonsa ya ɗaga ya kalli Abdul dake faɗin. “Lokacin da suka tsayar da motarsu a ƙofar gidan nan na fito. Ganin suna shirin saceta ya sa na yi saurin komawa gida, na ɓuya a bayan ƙofa na naɗi wannan videon...” Idonsa ya sake ɗaukewa daga kan Abdul ɗin. Sannan ya mayar da shi kan wayar ya na kallon bidiyon a karo na barkatai. Kansa ya jinjina yana miƙawa Ali wayar. Wai ko shi ma zai kalli videon dan ya tabbatar da fuskar wa cece a videon. MARIYA POV. Kamar yanda ta saba damawa Hilal custard haka yau ma shi ta dama masa. Sannan ta haɗa shi da shi. Wai ko ya yi shiru kunnuwanta su huta

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});