Chapter 27
Chapter 27
motar da gudu suka bar unguwar, sun ɗauka cewa shikenan kuma, matsala ta mutu tare da mutuwar Muktar. Sai da motasu ta bar unguwar, Sannan Muktar da ya kaucewa motar tasu ya tashi zaune da ƙyar. Dan a sanda suka bige shi bai kwanta a wurin ba. Ƙarfin hali ya yi ya murgina gefe. Su kuma suka taka dutse, har suna tunanin cewa shi suka taka. Hannunsa da yake da tabbacin ya karye ya riƙe yana jin raɗaɗin azaba. Sannan ya yi ƙarfin halin ɗaukar wayarsa, ya kira Ali ya sanar masa da halin da yake ciki, sannan ya kira ƙaninsa Walid. “Walid kana gida?” Ya faɗi da ƙyar yana rsinte idonsa. Saboda yanda yake jin ko ina na jikinsa na ciwo, gaba ɗaya ma ya rasa takamemen ina ne yake masa ciwo. Daga ɗayan ɓangaren Walid yace. “Eh Ya Mukhy. Ina nan, lafiya?” “Ka fito ka zo kwanar gidan Alhaji Sadam. Ina wurin, na ɗan samu wani haɗari ne?” Walid dake zaune a falo ya miƙe zumbur yana tambayarsa. “Haɗari? Yaushe? A ina?” “Stop asking just come and help me!” “Okay” Ya kashe wayar, sannan ya nufi ƙofar falo da gudu. “Kai Walid! Ina za ka je?” Mamansu da ta fito daga kitchen ta tambaya. Sai ya dakata, sannan ya juyo. “Ya Mukhy ne ya kirani yace ya samu haɗari a kan kwanar gidan Alhaji Sadam. Shi ne zan je na duba” “Haɗari?” Mama ta tambaya a hargitse. “Eh Mama. Bari in je na duba shi” “To ka kula. Allah ya sa ba wani mummunan abin ne ya same shi ba.” “Amin” Ya amsa yana fita daga falon. Da yake shi ya fi kusa da Muktar ɗin sai ya riga Ali isa. Dan gidan Alhaji Sadam ɗin ɗan gaba kaɗan ne da nasu. Sai da Ali ya zo, tukkuna suka ɗauke shi zuwa asibiti. ------------------- _Na lura da bana letter (M) ce ke zamani_ _Rabin 'yan wasanmu duka sunansu da ‘M’ ya fara_ _To gaba ɗaya babin yau ma a kan M ɗin ya ƙare. Ga Mariya fa Muktar._ _Sannan kun ji abin da ya faru tsakanin Munira da Mubarak_ _Kun kuma ji yanda aka yi Munira ta mutu_ _Mu je zuwa. Saboda yanzu muka fara sharar hanya😉_ _Share fi sabillilah❤️_ *Daga alƙalamin Salma Ahmad Isah✍️.* *CANDY CE🦋.* -------------------- _Kada a manta da biyan kuɗin littafi. Dan free page zai ƙare daga gobe in Allah ya kaimu. To subscribe pay ₦300 to._ 5487270431 Salma Isah Monie point. And send the evidence of payment via. 08130172702 #Candy #SalmaAhmadIsah °°°°°°°°°°°°°°°°°° *ƘADDARA CE!* *©SALMA AHMAD ISAH.* *CANDY🦋* _ArewaBooks @SalmaAhmad_ _Wattpad @Salma_Ahmad_Isah_ *10* MU'AZ POV. Zaune suke a falo shi da, Mummy, Mima da Na'im. Abinci yake ci yana latsa wayarsa. A jima kaɗan sai ya yi murmushi. Kuma ba komai ke janyo hakan ba face cry cry baby Leemat da yake tunowa. A duk sanda zai tuno haɗuwarsa da ita a yau sai ya yi murmushi me faɗi. Bai san me ya sa ba, amma haka kawai yanayin shagwaɓarta ke burge shi, da yanda take magana, da yanda kuka ba ya mata wuya. Kuma hakan ke nuna masa cewar shagwaɓa ɗabi'arta ce. Mima da tun ɗazu take satar kallonsa ta gyara zama tana leƙa cikin wayarsa. Wai ko za ta ga abin da yake saka shi murmushi. Amma ba ta ga ba, dan chat kawai yake. Sai ta ƙara matsawa kusa da shi tana faɗin. “Ya Mu'az!” Kallonta ya yi ba tare da ya amsa ba. “Ko dai da Yasmin kake chat?” Nan da nan ya murtuke fuska ya soma harararta. “Saboda Yasmin ce kaɗai mace a duniya ko?. Ko kuma saboda an faɗa miki cewar ba ni da wani aiki sai na chat da Yasmin?... Wallahi Mima idan ba ki daina shiga min hanci ba zan fatoki. Kuma a ranar da zan fato ki idan kika duba fuskarki a madubi ba lalle ki gane kanki ba!” Sai ta sosa kai tana zare ido. “Shugaban masifaffu!” Ta faɗi a ƙasan maƙoshi. Mu'az ya kalleta. “Kin yi magana ne?” Sai ta yi saurin girgiza kanta. “Ni kaza?... A'a, komai ban ce ba!” Ya wurga mata harara yana faɗin. “Ƙaramar mara kunya!” Mima ta ɗauki wayarta ta nufi stairs tana faɗin. “Allah ya nuna min ranar da ni ma zan zama babbar mara kunyar nan, matsayina ya ƙaru a idon ya Mu'az!” Kasancewar a hankali ta yi maganar ya sa bai jita ba. “Mummy!” Ya kira Mummy. Mummy ta dube shi tana amsawa. “Ɗazu na je gidan Anti Farida. Kuma tace tana gaisheki” Mummy ta ja tsaki tana mayar da dubanta kan tv. Can kuma tace. “To ina ruwana?” Mu'az ya yi murmushi me sauti. “Mummy! Mummy! Mummy!...” “Kai ni kar ka ƙarar min da suna!” Mummy ta katse shi. “Wai ni Mummy me Anti Farida ta miki ne?” Mummy ta galla masa harara. “Babu abin da ta min... Babana Mu'az” Tana ƙarashewa ita ma ta miƙe ta bar falon. Ya rage daga shi sai Na'im. Shi ma miƙewa ya yi ya kama hanyar fita. “Ya Mu'az wai yaushe za ka siyo min sweatern?” Na'im ya tambaya. Lokaci guda ya saki murmushi. Sannan ya juyo. “Kada ka damu oga tulele. Zan siyo maka gobe. Akwai chocolate a wurinka?” Ya tambaya yana murmushi. Saboda har ya fara hasaso haɗuwarsa da Halima a gobe. “Akwai. Amma sai kinder delice. Kuma ai kai baka shan kinder” “Ba ni zan sha ba, kyautarta zan bawa wata Baby. Ka kawo min guda goma idan akwai m&m's cookies ka ɗauko min guda biyar” Na'im ya miƙe yana faɗin. “Babyn waye?” Mu'az ya kalle shi. “Wata kyakkyawar baby girl ce... Me saurin kuka da fitina” Na'im ya yi dariya kawai. Sannan ya nufi sama. Ɗakinsa ya shiga ya buɗe wardrobe. Ya ɓebo chocolate da cookies ɗinsa, sannan ya saka a cikin wata bag me kyau. Ya sauƙo ƙasa ya iske Mu'az a inda ya barshi. Ya miƙa masa jakar da ya saka chocolate ɗin. “Yauwwa oga tulele. Ka kyauta. Insha'allah gobe zan kawo maka sweaternka. Sannan zan sake siyo maka wasu chocolate ɗin” Mu'az ya faɗa yana karɓar jakar. Na'im ya yi dariya. “A'a. Ba sai ka siyo min wasu ba, ina da wasu kalar da Daddy ya sai min last week” “To Baby ta gode. Yayan baby ma ya gode” Ya faɗa yana juyawa. Fuskarsa ɗauke da murmushi. “Baby!” Ya furta sunan yana nufar part ɗinsa. Kuma har ya shige bai bar murmushin ba. FARUK POV. Zaune suke a falo shi da Hilal da ya yi bacci tun wuraren ƙarfe 8. Kwance Hilal ɗin yake a kan cikinsa. Yayin da shi kuma yake zaune a kan kujera, yana jiran dawowar Mariya gidan. Shi ya rasa wannan wata kalar rayuwa suke shi da Mariya. Matar aurensa ta sunna ce za ta sa ƙafa ta bar gidan aurenta ba tare da ta nemi izinin mijinta ba?. Ba kuma hakan ne ya sa shi mamaki ba. Saboda ta saba fita ba tare da ta tambaye shi ba. Mamakinsa shi ne barin ƙaramin yaro da ta yi a gida shi kaɗai. Idan bai ɓata a ƙirgen watan haihuwar Hilal ba, dudu yanzu ba zai wuce wata goma sha ɗaya ba. Amma har ta kan iya tafiya ta bar shi a gida shi kaɗai. Ko
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31