Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 9

Chapter 9

Hauwa Kulu Book 1 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

zubin jikin sa na Fulani ne, sabida sirantar sa da ta zabge masa cika ido kai bazaka ce yayi shekaru ashirin da takwas din da yake da su bama. Sister Saratu ta hau raba ido tsakanin Innar Hauwa da Likita Sarham, ta ki cewa komai, don a dan zamansa da su na dan gajeren lokacin da bai wuce sati biyu ba da aka yi masa transfer daga asibitin Abdullahi Wase (Nassarawa hospital) zuwa nan wajen su, sun fahimci halinsa na kirki yayi yawa a kan marassa lafiyan sa, (hes very compassionate and caring to his patients), shi yasa a halin rashin mutunci irin nasu suke cewa ya fiya iyayi da kidifiri. Ilai kuwa ya fahimci komai tun ma kafin su bashi amsa, don ya san ba yau suka fara ba, wulakanta marassa lafiyan da suka rainawa ajawali halin maaikatan su ne, daga zuwan sa zuwa yanzu ya gama shaidar hakan, kuma yana cikin sahun likitocin da suka san darajar dan adam, basa yarda da hakan, sai dai in an yi ne a bayan idon su. A fusace ya soma fadin wato Metron Maria, Sister Saratu, Nos Mairo ba zaku daina wulakanta bayin Allah ba ko? Shin anya kun san aikin ku? Wannan ba shine halin da aka san maaikacin jinya na hakika da shi ba, hakan cin amanar aiki ne babba, kuma tozarta dan adam ne. Ina humanity din ku da aka hore ku da shi matsayin ku na maaikatan jinya, dana kiwon lafiya? A gaskiya na gaji da halin ku, ko jiya na raba ku fada da patient. Idan baku yi hankali kun yi aikin da ya kawo ku yadda ya kamata ba wallahi duk sai na yi reporting din ku. Ya dubi Innar Hauwa data sunkuyar da kai kasa tana tsane ido, yace. Baiwar Allah me ya faru? Waye babu lafiyan? Innar Hauwa ta ji dan kwarin guiwa ya shige ta, saboda a cikin muryar sa mai dushewa da rashin karsashi saboda mura, akwai (caring) wato kulawa da darajja dan Adam, ta rausayar da kai gefe ta ce, dama yarinya ce na kawo tana ciwon ido, to sun ce ban zo da wuri bane shiyasa bazan ga likita ba, shine dalilin da nake ta basu hakuri”. Tausayin matar ya kama shi, ya dubi yarinyar da take rike da hannun ta, yadda hakiya ta cinye rabin idon sai da tsigar jikin sa ta tashi, zuciyar sa ta tashi, ga kwantsa babu kyawun gani, da sauri ya dauke idon sa daga kallon yarinyar, ga kafafun su futu-futu da kura tabbacin sun sha tafiyar kasa mai nisa kafin su iso asibiti, sai ya karbi katin su daga hannun maaikaciyar jinyar da katin ke hannun ta wato Nos Maria, ya kuma yiwa Inna umarnin su biyo shi a baya zuwa cikin ofis din. Sai lokacin Inna ta gane shine likitan da ake musu rowar gani. “Iya yaya aka yi aka bar idon yaci hakiya sosai har haka? Dr. Sarham ya tambayi Innar Hauwa, yana haska cikin idanun Hauwa da yar tocilan din sa mai tsananin haske, yana magana cikin tsantsar damuwar da ta kasa boyuwa a muryar sa, yana cigaba da haska cikin idanun bayan ya gwale su sosai, Inna bata iya ta ce komai ba amma guilt ya bayyana akan dattijiyar fuskar ta ainun. Dr. Sarham ya gama duba idon Hauwa da tocilan din sa, ya kuma gama nazarin sa gabadaya duk cikin dan lokaci, sai ya koma ya zauna a bakar kujerar sa mai juyawa, itama yace ta zauna a kan kujerar zaman maras lafiya da ke fuskantar sa, ya bude mata fayil a take don ya gama gano Hauwa na bukatar aikin ido na gaggawa kawai, don a cire hakiyar. Ya sunkuyar da kai yana rubuce-rubuce a cikin fayil din ta, kafin ya gama ya dago ya dubi Inna. A hankali kuma cikin tsanaki, Dr. Sarham Abbas Shanono, ya shiga yiwa Innar Hauwa bayanin amfanin zuwa asibiti da wuri, da zarar an ga alamun ciwo, ba sai ciwo ya ci ya cinye ba, cikin tausasawa da lallashi da fasahar harshe irin nasa yake mata magana, ya gaya mata yanzu ba abinda zaa iya yiwa Hauwa a ceci idanun ta illa cataract surgery watau (fida don cire hakiya) ta gaggawa. Likitan ya saka musu ranar aiki jibi-jibin nan, ya kuma fada musu kudin aikin. Duk da Innar Hauwa ta tsorata da yawan kudaden bata nuna ba ko a fuska. Duk da ta san kuwa bata da su a ajiye. Da suka koma gida Inna ta shiga cikin matsananciyar damuwa, na farko bata da kudin da likita ya bukata a yanzu, ko jarin wake da shinkafar ta ba zai yi kwatan su ba, abu na biyu tana ganin bazata iya bari a farkawa Hauwan ta ido ba haka kawai. A je garin neman gira a rasa ido. Ko a jangwalo wani abun da yafi karfin su. Amma Hauwa ta dagewa Inna ita dai tana so ayi mata aikin nan. Inna ta gaya mata abinda take tsoro da kuma rashin kudin aikin a hannu, nan Hauwa ta dinga magiya har da kuka, tana rokon Inna ta amince in yaso ko dan taure daya ne cikin dabbobin ta a sayar a biya. Komai ya faru daga Allah ne. Haka kan dole Inna ta amince da shawarar ta, don bata son kukan Hauwa ko bacin ranta. Ta fidda Akuya budurwa aka sayarwa mahauci. Washegari, wato ranar da aka basu, da sassafe suka koma asibitin Murtala. Likita da abokan shiga tiyatar sa suka gama shirin yi wa Hauwa aiki, aka nemi Inna da ta saka hannu, Inna ta saka hannu amma da ganin ta zaka fahimci a matukar firgice take, gani take kamar aka shiga da Hauwa tiyatar nan bazata fito a raye ba, Inna ta soma hawaye tana sharewa da habar zanin ta, tana kankame da hannayen Hauwa. Ganin haka Dr. Sarham ya shiga yi wa Innar Hauwa maganganu na kwantar da rai yana cewa kada ki damu Innar mu, lafiya zan maido miki ita, da iznin Ubangiji, da kiyayewar sa, da albarkar sa zaa yi aikin nan lafiya a fito lafiya, in sha Allahu. Idanun Hauwau su koma tangaras, kamar yadda suke a baya su rabu da hakiyar da ke cikin su, hakiya musiba ce ga ido, kin ji ko Inna?. Ta daga masa kai, ba don ta gamsu ba, amma bata fasa zub da hawayen ba. A haka aka shiga da Hauwa dakin tiyata. Ko kafin masu allura su yi mata allurar tafi-da-ran ka wato (anaesthesia) fuskar Dr. Sarham Hauwa ta kurawa ido tana cewa a ranta inama tana ganin sa tar-tar, domin ta ji dadin abinda ya cewa Inna. Haka ta cigaba da kallon saitin fuskarsa kamar tana ganin sa sosai, alhalin inuwar sa da karshen tsayin sa kawai take iya gani, bata san me yasa take son sanin yaya kamannin sa na halitta suke ba, ko don tausasan kalaman bakin sa ne da yadda yake lallaba mata rikitacciyar Innar ta, domin a lokacin bata ganin komai dadai ama dai tana ganin haske cikin idanun ta. Murmushin da Dr. Sarham yayi mata a lokacin kamar ya san me take ciki da zuciyarta ne, taji sautin murmushinsa a kunnen ta, ji tayi kamar ya fahimci ba abinda take son gani a lokacin

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});