Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 11

Chapter 11

Hauwa Kulu Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

soma warware bandejin da aka nannade idanun Hauwa da shi da dan almakashin da ke hannun su. Aka warware bandejin tsaf. Sai ga kyawawan idanun Hauwa tsaf da su garai-garai dasu kamar a wanke babu hakiya, aiki yayi kyau kenan. Amma me? Dr. Sarham ya tambayi Hauwa su nawa ne a tsaye a gaban ta? Hauwa ta shafa idanun ta ta kyafta su, ta sake kyaftawa kafin ta girgiza kai tace, LIKITA AI BANA GANIN KOMAI A GABANA SAI DUHU! In kin ji faduwar gaba da tashin hankali a wurin su su duka dake wurin abin baa cewa komai. Amma shi Dr. Sarham ba faduwa kawai gaban sa ya yi ba, yankowa yayi daga zuciyar sa ya tsinko daga kirjin sa ya fado kasa yana majaujawa a dandaryar kasa.. Ko dama ya dade cikin wannan zullumin tun ranar da ya yi wa Hauwa aikin. Jikin say a gama bashi bai yi nasara ba. Ya tabbata yayi kuskure a cikin aikin domin a lokacin da yake mata aikin ya samu kansa cikin wani bakon yanayi na rashin yarda da kai, wanda zai iya cewa ya gusar da consciousness din sa (hayyacin sa) na dan wani lokaci. Yanayi ne da bai taba samun sa ba a yayin ‘surgery’, ya sha yin aikin da yafi wannan hatsari na glaucoma amma bai taba sarewa ba sai a kan wannan, yafi danganta abinda ya same shi a lokacin da fargaba da tsoron rashin yin nasara sakamakon abinda ya tsinkaya ana cewa a kan sa, wanda ya jefa shi a halin rashin yarda da kwarewar sa akan karan kansa, amma ba don bai iya ba din, dadin dadawa bai taba yin aikin hakiya ba sai wannan karon akan idon Hauwa, ya kuma ga yadda hakiyar tayi zurfi sosai taci idanun ta lalata maganan ta, wannan ya jefa shi a fargaba mai yawa ta aikin bazai yi nasara ba wadda bai kamata ta zo masa a lokacin ba a matsayin sa na likita. Tunda ya koma gida kuma da wannan tunanin ya kasa dawowa asibiti, don ya tabbatar bai yi aikin yadda ya kamata ba, ko yace yayi kuskure a aikin da ya yiwa Hauwa, ko yace kamar hakiyar da ragowa a ciki bai cireta duka ba, a sakamakon gushewar hayyaci da ya samu na dan wani lokaci (at the said moment). A karshe ya tabbata garesu dai bakidayan su babu ko tantama Hauwa ta makance a dalilin aikin da Dr. Sarham Abbas Shanono yayi mata ba daidai ba, iyakar maganar kenan. Gulmar su ta tabbata aka bai iya di ba. Ga idanun nan tarr a bude, amma Hauwa bata iya ganin ko dan yatsan ta balle inuwar mutum ko hasken rana da take iya gani kafin ayi aikin. **** **** ***** GULMA AJALI A wannan yammacin a Nurses station na sashen ido a asibitin Murtala baa komai sai gulamammaki masu lasisi, na abinda ya faru a kan aikin da sabon likitan ya yiwa maras lafiyar tasa. Su Nos Saratu da Metron Maria an samu abinda ake so, aka maida abin topic of discussion na wannan ranar. Ko aikin su na ranar sun kasa yi yau, tsabar saboda yadda gulmar Sarham ke cin su. Metron Maria wadda ita ta halarci aikin warware idanun Hauwa tare da likitan, ta ce hey! In baku labari dai, kunnen ku nawa? Suka hada baki (in chorused) wajen cewa kunnen mu biyu, to ku kara biyu ku sha labari. Dr. Sarham dai ya karasa makantar da yarinyar nan mai hakiya da yake mana balbali akan su, aikin da yayi mata was not successful at all. Kuma ya kama bakin sa salin-alin bai ce komai akai ba ya bar asibiti, ba tareda kowa ya san taasar da yayi ba, ya ja bakinsa ya tsuke ko sum utu ko suyi rai oho musu. Nos Gambo tace ki bari don Allah? Saratu ta yi rantsuwa ta labarta musu abinda ya faru, ta ce yo dama idon ya gama rubewa fa, maganin su kenan suma, da sun lallaba sun tafi da muka kore su da ta ci gaba da morar dan wani abun a idon, aa su ga sarakan naci dambun kuturu, ni dama na san idon kiris yake jira a taba shi, shikuma karambanin sa kenan, an ce musu sawun su a likkafa su koma gida su cigaba da barbada farin kwallin su da suke barbadawa suka ki ji, wanda bai ji bari ba ai ya ji hoho, yanzu da ya maidata totally blind ai sa hakura. Ni ai dama na fada muku tsautsayi ne kadai zai saka ni baiwa wannnan yaron idanuna ya saka musu wuka, har yaushe ya bar sakandire ko ince ya bar shan nono a cinyar uwar sa? Da zan bari ya fede min ido? Ai yafi kama da Romeo (Uban soyayya) fiyeda consultatant. Ban da ilmi a Najeriya ya zama sabatta-juyatta, ya zama abinda ya zama wajen tabarbarewa, ban taba ganin inda dan kasa da shekaru talatin ya zama surgeon ba” wata bakuwa a cikin su mai hankali ta ce, ku kuwa ku daina abinda kuke yi bai kamata ba, shi aikin fida ai haka ya gada, ko ayi nasara, ko akasin ta, kafin ayi aikin mara lafiya ya san da haka saboda haka nema ake saka hannu bisa yarjejeniyar amincewar iyaye da makusan ta, so ko mutuwa ta yi bashi da alhakin hakan. Yayi iya kokarin sa Allah ne bai yi ba. Idan fitsari banza ne kaza ta yi mana? Kuna ta zagin sa da kushe shi alhalin bai ci muku ba bai sha muku ba, ku ku je kuyi karatun fidar idon mana? Shin wai kyawun Dr. Sarham da gayunsa ne ya koma masa abin hassada a bakunan ku ko me?. Da wannan ta kashe bakin su murus, bayan sun musa da cewa ina abin yake da zasuyiwa hassada abu tsololo kamar karan raken takanda. Wata kuma mara kunya a cikinsu ta kada baki tace ai irinsa sun fi dadin shaani a gado, baa dakin tiyatar ido ba. suka kwashe da dariya. Har suka tashi aikin ranar basu bar wadannan zantukan ba na shegantaka har daya na cewa ya kamata a kwace licence din sa na aikin likitanci tunda daga zuwa ya fara da makantar da yayan mutane, saboda rashin iya aiki. (Ni kuma nace gulma-ajali mai yin ki kadai zaki kashe). ***** ***** ***** DESTINY TORMENTS.” (DA KARFE SHIDDA NA YAMMA A GIDAN PROF. ABBAS SHANONO) M awakin ya sake cewa Destiny torments my heart… cikin baitin wata waka ne da Dr. Sarham yake saurare daga kwancen da yake a yammacin ranar, bayan komawarsa gida daga kwace idon Hauwa. Yana kwance har kusan magriba a rigingine a tsakiyar matsakaicin gadon dakin sa. Sai ya ji shahararren mawakin zamanin wato R-Kelly kamar dashi yake. Don zuciyar sa duk ta takura. Ya shiga kunci na babu gaira babu dalili. Ya yarda abinda ya faru dashi a kan aikin da ya yiwa Hauwa Bilyaminu kaddara ne, wadda ta rigayi fata, ba don haka ba ai yaji ‘warning alarm’ a cikin kansa, mai cewa ya bari kada yayi aikin nan babu nasara a cikin sa sam, don haka tunanin sa yafi karkata ga cewa sakacin sa ne ko gangancinsa. Amma kuma da aikin kaddara ai, altogether. Allah ya riga ya rubuta

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});