Chapter 21
Chapter 21
rajaa wajen lallashin su da karfafa musu gwiwa kan tafiyar Sarham din da cewa, menene abun damuwa don Sarhamu ya tafi? Tunda ga waya yanzu, ta fara zama abu mai sauki, kuma dukkan ku zaku so ganin ranar da Sarhamu zai zamowa kasar sa abin alfahari inace, wanda zai zo a dama da shi a harkar kiwon lafiya a Arewacin Najeriya”. Amma fa shima Abban a ran sa ya fi kowa damuwa, ya fi su shiga kewar Sarhamu, tun ma kafin ya tafi, saboda yadda Sarham yake tsaye kullum kan hidimar sa data gidan sa, wani abun ko labari baya ji sai zance ya shigo da zance, Mama zata ce ai Sarham yayi kaza, kamar misali cefanen gidan sa, yana dadewa bai yi ba. Haka maganin da kowa yake sha idan rashin lafiya ta samu dayan su, Sarham da bai da iyali ya daukewa Abban su kananan abubuwa irin wadannan, su petrol din tada janerato, har ila yau, yana matukar taimakawa shi kansa Abban da nasa ayyukan ofis din kasancewar Allah yayiwa Sarham baiwar ilmi da sanin hikimar koyarwa, kuma da yake a fanni guda suke shi da Abban. Don haka shima yana cikin kewar Lelen Abba! Shima Sarham din karfin hali yake yi, musamman in ya dubi Sumayyah, da kukan da take yi. Sai Abba Prof. yace tayi hakuri yayi mata alkawarin bin bayan Sarham da zarar ta kammala sakandire itama zata je ta yi MBBS a can inda yake. Kasancewar Abba Prof. yana da hanyar tagomashin karatu a kasar Saudiyyah (scholarship) na Jamiar KING ABDULAZEEZ UNIVERSITY domin akwai abokan karatun sa da yawa da suke aiki a jamiar, tun bayan bude tsangayar likitanci a jamiar. Da an samu rarar gurbin karatu su kan bashi. Mama bayan Sarham ya shiga dakin sa yana hada kayan tafiyarsa, sai ta zare jiki ta bishi a baya, kujerar karatunsa dake dakin guda daya ta samu ta zauna, Mama ta ce, “Sarham haka muka yi da kai? Ya bar abinda yake yi ya bata hankalin sa ya ce akan me Mama? Tace maganar diyar Barr. Hannatu da na gaya maka muna so muyi muku yar gida don kara karfafa zumuncin dake tsakanin mu ni da mahaifiyar ta, mun yi da kai kafin ka tafi ko sau daya ne za kaje ku gaisa da ita Sadiya din, amma har yau ban ji ka kara tada zancen ba, gashi har zaka tafi. Kasan dai yadda nake da Barr. Hannatu, babu wasa ko rainin hankali tsakanina da ita, bana so ka je ka shantake a Jeddah babu aure, so nake da ka samu good two or three years ka dawo gida kayi auren ka in ya so in ma komawar zaka yi ka koma da matar sai hankali na yafi kwanciya da zaman ka a koina ne, tunda na fahimci kafi son rayuwar Jeddah banda haka da ka zauna ka cigaba da aikin ka kawai. Duk da nasan baka da matsala Sarham, tarbiyyah ta Allah bazan ce ni na baka ita ba, amma Allah ya yi maka tarbiyyar da kowacce uwa zata yi alfahari da ita, saidai kwanciyar hankalin iyaye a kullum shine ace yaran su sun yi aure a lokacin da ya dace. Sarham ya nisa, ya ajiye rigar da zai saka a cikin trolley a gefe, kafin yace cikin lallashi Mama bana so kisa ran ki a irin wannan hade-haden auren na favouritism domin ki dadadawa wasu, wanda a karshe maimakon ku gyara zumunci sai dai ku kai ga lalata shi, saboda ni gaskiya Mama bana raayin macen da iyayen ta ke nemo mata miji daga yayan kawaye. Yau da a ce ke da kan ki kika yi wannan raayin, zan iya bi, koda kuwa bana so, amma daga sanda kika gaya min Barr. Hannatu ce ta nemi alfarmar nace a raina yar ta ta rasa miji ne take nema mata, gashi ni ba rasa mata nayi ba, na tabbata lokaci ne. Mama kin san da labarin “Madinah” ba tun yau ba, to wallahi Mama har gobe tana raina, don nina gan ta naji ina so saboda wasu dalilai, amma na gwammace in hakura da ita tunda ubanta baya kaunata, kuma daga kanta bana jin zan kara son wata ya mace, daga kanta kuma na tsani soyayyar bakidayanta. Mama weve had a wonderful time together nida Madinah, for as long as four years muna tare cikin kauna da fahitar juna, mun yi wa juna alkawura masu yawa amma Madinah ta saka kafa ta take su tayi fatali dasu rana daya, don haka daga kanta na daina bata lokaci na a kan yammata wallahi. Duk marasa amana ne. Madinah ta dusar da hasken sauran mata daga idanuna Mama, ba wadda nake ganin farin ta. In fact, Mama bani da niyyar aure nan kusa. Ban san me kaddara ta tanadar min gobe ba!. Mama ta ce in uban Madina baya son ka sabida ya raina ajin uban ka, su wadannan uwa da uban duka sun zo da kan su sun ce ka yi musu, suna son hada jini da ni, saboda sun san darajar mu da martabar mu, ni kuwa bana tulawa masoyi na kasa a ido. Amma ban isa in maka dole ba. Duk abinda uban Madina ke takama da shi na tarin arziki da ilmi da har yake ganin baka isa auren diyar sa ba, uban Sadiya ya mallaki goman sa, Da sauri Sarham yace ko ita Madinah ba dalilin da yasa na so ta ba kenan Mama, na rantse ban taba sanin waye ubanta ba har sai bayan ya yanke alaqar mu. Na so Madinah ne akan wani dalili Mama. dalilin kuma shine. kokarin ta a karatu. zai fara bata labarin irin kokarin Madinah da yadda take ‘excelling with high grades a kowacce jarrabawa Mama ta katse shi da karfi, inda tace bana bukatar ji, na gaji da zancen Madinah Attahiru Sarham tunda ba itace autar mata ba. Ka karbi masu son ka, ka rabu da tsammanin warabbuka. In dai labarin nan ne ka bani shi yafi sau shurin masaki, yafi cikin carbi, har na riga na haddace shi, kana son Madina saboda kokarin ta akan karatu, na gaji da jin wannan, abinda baka sani ba, Madina ba itace karshen masu kokari ba, Sadiya ma tana da irin nata domin kuwa Quantity Surveyor ce. Kuma uwarta ta tabbatar min tana son ka sosai, ba wai ita ta ga dacewar abin ba Sadiyar ce da kanta tace tana son ka. “Ahap! Anzo wurin. Mama ta bare ta gabadaya. Sarham ya fada kasa kasa su Mama an kara bare ta, to ai ni Mama bazan taba auren macen da ta ganni wai ta ce na yi mata ba, komai lalacewar zamani akwai mata masu aji, wadda ba ni na ce ina son ta ba in the first place hankalina bazai taba kwanciya da ita ba”. Duk ta inda Mama ta bullo don Sarham ya karbi tayin yar aminiyar ta Sadiya Sarham sai ya zuqe, amma fa cikin lallami da dabara yake bin Mama don su yi rabuwar salama. Ya san kan Maman sa sarai, yana yi yana dariya da hilatar ta yadda bazai bata mata rai ba. A karshe Mama ta gaji da jainjar, ta sakar masa inda ta ce Sarham! Na baka shekara daya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31