Chapter 22
Chapter 22
ka kawo min matar da kake so ka aura, mai kokari irin Madinah wadda hankalin ka zai kwanta da ita din, tunda kai dai a kan Madina kowa dakiki ne, to ka nemo mai kokari irin nata, kafin shekara daya, amma ni wannan Madinar ko zancenta bana son ji. Sarham idan shekara ta zagayo baka kawomin mata ba na rantse Sadiya zan aura maka, kana so ko baka so, in kuma dauketa in bika da ita har inda kake. Sarham ya ce to Mama addua zaki yi min Allah ya kawo mai kama da Madinah, fara kamar balarabiya, doguwa siririya mai gashi yala-yala har gadon baya, sannan mai asalin kwanya a karatu irin ta Madinah Sorondinki. Tsaki Mama tayi ta tashi ta bar masa dakin don haushi. Ta sani daga Madina har iyayen ta babu wanda ya damu da shi shi, kadai yake kidan sa yake rawar sa a kan ta. Ita kuma bazata taba maraba da inda baa son nata ba. Washegarin ranar Sarham ya ga cewa ya kamata ya je wa su Inna sallama, kai zai yi kewar kawar sa Inna Safiyya… yadda baa zato, tsakanin itada Sumayyah bai san wa zai fi kewa ba. Wata zuciyar a can kasan kirjinsa tayi whisphering a sace, inda tace masa MISKINIYA KULU!” Da sauri Sarham ya kalubalanci zaciyar sa da cewa capital NO! he will never HAUWA_KULU, zai yi kewar kowa tabbas, har Surayyah da basa jituwa, amma ko kadan ba zai yi kewar Maijidda ba, ba don komai ba ko don halin koin kulan ta da miskilancin da take nuna masa, da rashin maganar ta da sakewa da mutane wanda baya bari ayi sabo mai shiga jiki da ita irin wanda har zaayi kewar ta don an daina ganin ta a wuri. Shin wai kodai shi kadai Maijidda take nunawa halin koin kula, da shariya, da miskilanci, da rashin walwala wani lokacin ma sai ya ga kamar sad face a tare da ita idan taji muryarsa a gidan su??? Ya isa gidan ana kiran sallahr Isha, Inna na alwalah Hauwa na cin tuwo. Yayi sallama Inna ta amsa Kulu ko kamar yadda yayi tsammani a cikin cikinta ta amsa masa sannan bacin ran da yake zargin gani ya dan bayyana kansa a kan fuskar ta. Sai Sarham ya lallaba ya dauke kwanon tuwon daga gaban ta ba tare da yayi magana ba, ta shafa gabanta don kara kai loma sai taji wayam, babu kwanon, amma bai sani ba kamshin turaren sa da ya nashi hancinta (Oud Abyad) ya tabbatar mata shine a wurin ya dauke kwanon. Baya jan ta da wasa amma yau da yake sallama ya zo, shiyasa ya ke son ko yaya ta kula shi. Dan murmushi tayi, wani basakkwacen murmushi ta share shi, ta janye hannu ta koma gefe, ai kuma ta mike don wanko hannu, tana tafe kanta tsaye zuwa famfo kamar ba mara ido ba, ba tare da ta nemi Inna tayi mata jagora ba. sai data kai bakin famfon ta kunna sannan tace ka hutar ni dauke kwanon, dama na koshi ai. Mamaki yasa Sarham rufe baki yana dariya yace. Inna ashe idon mu ya bude! Inna tace fata nagari lamiri, me yasa aka ce muyi fatan alkhairi akan komai? Ai don bamu san tasirin bakunan mu ba, mai yuwuwa Allah ya biye bakin ka watarana Likita”. Sarham ya ce haka yake Inna, amma shi ya san da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa, sai dai duk wani mumini yayi amanna da cewa ba abinda ya gagari Allah, suma likitocin lalube suke yi a cikin duhu. Sanin gaibu sai Allah. Ya russuna har kasa ya gaida Inna, ta kawo masa darduma ta shimfida, sai ya ce, “tunda sallah za kuyi, muyi jami gaba daya kawai, ban taba jan ku sallah ba Inna. Maijidda dauro alwallah. Daga inda take tsaye a jikin famfo tayi dan sakale! Bata ce toh ko aah ba, don jiya ta fara ganin jinin alada a rayuwar ta, itama bata sani ba, Inna ce ta gani a jikin zanin ta ta gaya mata, ta kuma taimaka mata wajen kunzugu, ta koya mata yadda zata dinga killace kanta da tsaftataccen tsumma, dankwalin sabuwar atamfarta mai tsafta ta dauko ta tsaga shi gida biyar ta koya mata amfani da shi, ta kuma gaya mata baa sallah da komai na ibada sai an samu tsarki, koda yake duk ta sani a makaranta tun kafin ta fara din Duk da cewa ta tsorata da Inna ta gaya mata ta fara alada, ta kuma tabbatar mata yanzu ta girma dole ta kula da kanta da tsare mutuncin ta daga wannan lokacin, da kuma koyon yadda zata ke muamala da maza daga yanzu. Inna ta zaunar da ita ta ja kunnen ta sosai, ta gaya mata yanzu da girman nan ya hau kan ta ko hannun ta namiji ya kama cikin shege ne zai shiga jikin ta kuma haramun ne. ta tsoratar da ita sosai akan maza ko yaya take dasu. Yinin jiya zungur laccar da Inna ta wuni tana yi mata kenan. Sarham ya gaji da jiran Kulu ta zo su tada sallah, don tunda ta shige daki ta ki fitowa ya dauka hijabi zata shiga ta dauko amma shiru kake ji. Sai Inna ce ta sadda kai ta ce, ja mu sallahr ka ji! Kuluwa girma ya zo!. Sarham cikin rashin fahimta ya tambayeta girma kamar yaya?. Duk surutun Inna da yadda ta ke sakewa da Sarham wannan karon kasa fada masa Hauwa ta fara alada tayi, ta hau inda-inda, har ya gaji ya tada sallah, amma daga karshe a matsayin sa na likita malamin kiwon lafiya sai ya dago su. Abu daya zai hana mace sallah uwarta ta bi bayan ta shine idan tana fashin sallah. Ikon Allah, har nawa Hauwa-Kulu take? Maiyuwuwa kuma irin jikin ta kenan. Irin su kuma sune masu haihuwar wurwuri. Koda yake kanwarsa Sumayyah ma haka ta fara da wuri, kuma shi ta fara gayawa tana kuka, don ta kasa gayawa Mama da Surayyah, tana ganin wani mugun abu ne ya faru da ita, ba zai manta ba shi ya fara saiwa Sumayya always pad ko Mama sai da Sumayya tayi wajen sau uku kafin ta sani. Bayan sun idar da sallah shi da Inna, kasa gaya mata tafiyar sa Saudi yayi, saboda sabo, da wata irin kewar su da tazo ta rufe shi, Inna kuwa tana ta hidimar hada masa tuwon masara miyar kuka da manshanu, ga yajin daddawa a gefe, ta kawo ta aje masa da ruwan randar ta mai sanyin dadi. Taga yayi shiru ya kasa cin abincin da doki kamar yadda ya saba, cikin kulawa Inna ta ce, likita ya dai? Jikin ko garin?” Ya nisa, kafin yayi kundumbala ya ce babu ko daya. Inna sallama na zo muku, zan bar kasar nan!. Ba Inna kadai ba hatta Kulu da ke daki fitowa tayi da sauri daga uwar dakin data je ta boye jin abinda Dr. Sarham yake cewa. Tafiya ta same ni zuwa kasa mai tsarki, zan tafi karo karatu na akalla shekaru uku, Inna ina fatan zaki cigaba da tayani kula da karatun Maijidda har ta kammala, alkawari ne na dauka tsakanina da Ubangiji sai na ga ta kammala sakandire hankali
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31