Chapter 7
Chapter 7
don ko haihuwar Hauwa data marigayin Yayan ta bata yarda an kaita asibiti ba, don haka hatta yanda ake karbar kati basu sani ba, saida taimakon wata mata da itama ta kawo yar ta ganin likita, suka samu suka karbi kati suka hau dogon layin ganin likitan ido. Don kuwa a makare suka iso. Suka kuma gamu da dogon layi don ranar ganin likitan ido ce wato Alhamis. Sune kusan na karshe a kan layin, suka zauna a kan bencin da aka tanadar wa marassa lafiya masu bin layin ganin likita bayan sun mika katin su, maaikatan jinya da yake akwai marassa kirki cikin su, idan suka juya suka kalli idanun Hauwa sai suyi tsaki, su hau maganganu na gugar zana cikin zagin jahilcin mutanen kauye wajen sakaci da zuwa asibiti, sai ciwo ya ci ya cinye a kwaso jiki hajaran majaran wai an zo asibiti, sun dauka daga kauye suke don sun fi musu kama da kauyawa. Inna na jin su, ta yi shiru ta sadda kai, bata tanka musu ba. Wata metron zaqaqura a cikin su, ta kasa gugar zanar ma, sai da ta fito fili ta dubi tsakiyar idon Inna ta ce. To yanzu saboda Allah baiwar Allah me likita zai iya muku a wadannan matattun-rubabbun idanun da hakiya ta riga ta cinye? Allah wadaran bakauyen mutum wajen wasa da lafiyar sa!. Da sauri Inna ta dago ta dube ta, kafin ta rufe baki dayar ta amshe. “Taya ni gani, tun dazu nake kus-kus din hakan a raina kika riga ni furtawa, saboda Allah dubi yarinyar nan sai da Hakiya ta gama cinye idon tas, sannan zasu wani dauko kafa budu-budu dasu su zo asibiti, yo wannan ai ta gama makancewa da lasisi, ko me likita zai iya musu a wannan lokacin ina ce aikin banza ne?. Inna dai na jin su, amma bata tankawa, duk da ta yarda basu da mutunci kuma basu girmama furfura, amma ita da kanta ta yarda har da sakacin ta wajen lalacewar idon Hauwa-Kulu. Ta sunkuyar da kai kasa sosai, hawaye fal idon ta, amma bata bar su sun zubo ba. Ta dago ta dube su, su duka basu fi a kira su yayan cikin ta ba amma suke mata wannan tanadin. Kodayake kowa ya san yadda maaikatan jinya na gwamnati suke, daidaiku ne masu jin kai da kirki ga marar lafiya, musamman ga mutanen kauye da talakawan da suka raina wa ajawali kamar yadda suka raina Inna din, don sun ganta da kodaddiyar atamfa mai barewa, kuma tayi abunda a wurin su jahilci ne da gidadanci. Sanin halin malaman asibiti da sau tari ake bata labari tuntuni, yau da suka gwada mata sai bata yi mamaki ba kuma bata ji zafi sosai ba, shiyasa ta daure taki damuwa da su, fatan ta kawai su mika katin su ko sa samu ganin likita. In ya so shima ko me zai ce mata yace mata a shirye take da daukan laifin ta. Fada ne dai ta san zata sha shi har a wurin likitan shima, to in dai a karshe zai baiwa Hauwa magani, ganin ta ya gyaru, ta rabu da wannan hakiya, to babu komai, shima zata jure nasa. Ba abinda malaman jinya basu ce mata ba na raini da wulakanci, da suka tambaye ta ko tun yaushe Hauwa ta fara hakiya? Ta ce an fi wata uku, suka ce to tun yaushe suke ganin likita? Nan kuma ta sunkuyar da kai ta ce basu taba zuwa ba sai yau. Sai wata maaikaciyar jinyar mara kunyar gaske tayi kamar ta doke ta, yadda ta rufe Innar da fada duk da ta girme ta, ta ce to ba zata mika katin nata ga likita ba, su tattara su tashi su tafi, in yaso su je su karata da farin kwallin da take rambada mata kamar idanun kwatami. Inna ta kauda kai ta rabu da su. Amma bata yarda ta tafi ba, duk da sun kore ta. sun kuma tabbatar mata bazasu mika katin nata ba. Sai suka rabu da ita suka koma hirar da ta shafe su, suka manta da su a wurin. Lokaci lokaci suna kiran sunan marasa lafiya suna shiga ofishin likita amma basu kara bi ta kan su Hauwa ba, don a wurin su sun gama da babin su. Hirarrakin da suke yi duk a kan matashin likitan su ne, wanda aka kawo musu ya maye gurbin kwararren tsohon likitan ido wato Dr. Barde Abba, wanda shi kowa ya san kwararre ne. Inna na ganin hirar tasu a matsayin cin naman abokin aikin su. Don a cikin hirar tasu ta ji suna fadin. “Ai tsautsayi ne kadai zai sa mutum ya fada hannun sa, da sunan wai yayi masa aikin fidar ido, yayi yarinta kwarai da gaske da zama likitan ido, a ganin su baa taba yin yaron likita a tsangayar ido mai kananan shekaru, kuma mai jarumtar hali da karfin hali kamar sa ba, a dai tarihin asibitin Murtala bakidaya da suka jima da sani, don sun dade suna aiki anan. Dayar tace ai hatta sauran likitocin duka asibitocin da ke cikin kwaryar birnin Kano a yanzu, bata jin akwai karamin yaro kamar wannan da kwalin likitanci, bama na MBBS kadai ba, wai har consultancy ya gama, wanda bai wuce ace masa saurayi dan tashen balaga ba, watakila dai zuqen karatu aka yi tayi masa, saboda yana da uwa a gindin murhu, tunda Baban sa wato mahaifin sa Farfesa ne (Prof.) na tsangayar likitancin ido, a jami’ar koyarwa ta Abdullahi Bayero. Gulma tayi dadi sosai a tsakanin su. Daya daga cikin su kuma ta ce, aah fah, ku daina Magana akan abinda baku da tabbas, ai an ce baa jamiar Bayero yayi karatun likitancin nasa ba, a can Jeddah ne, ta kasar Saudi-Arabia. Wato alumnae ne na Jamiar Sarki Abdulaziz. Can kuma kun san baa dadewa ana karatun likitanci kamar yadda ake dadewa a nan Kano da sauran garuruwan Arewacin Najeriya, idan muka auna a hankali, a bisa maauni na adalci, zamu ga cewa in har ya bar sakandire a shekaru goma sha shidda, ya shiga jamia a shekarar da ya bar sakandire zai iya yin MBBS na tsahon shekaru biyar acan, ya kuma dora da consultancy shima na shekaru biyar zuwa shidda, zaku ga cewa babu zuke cikin ilmin sa har kuwa da hidimar kasa”, inji mai dan hankalin cikin su. Ta kare zancen ta da cewa. Don haka ba abun mamaki bane don ya zama likitan fidar ido a shekaru ashirin da bakwai zuwa da takwas da haihuwa, in dai har da gaske ya fara karatun da wuri, ya kuma gama karatun sakandire a shekaru akalla 16-17, kuma dai yana da gatan sa a fannin karatun nan kowa ya sani”. “Sai shegen iyayi da uban tsayi kamar karan raken takanda, dan sirit da shi kamar ka bushe shi ya fadi amma sai iyayi, ga dan banzan manyance kamar gyambo a kafa. Karambanin irin su ya wuce shekarun su, don ko ni nan na tabbata na girme mishi wallahi”. In ji wadda ta fi sauran rashin ta ido wai ita Nos Saratu. Duk suka sa dariyar maganar tata, Nos Maria har da kyalkyalawa da sukuyawa da rike ciki, irin ta wadanda dariyar gulma tayiwa dadi. Zaka yi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31