Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 2

Chapter 2

Hauwa Kulu Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da ake ciki a lokacin shine; al'ummar 70s da 80s basa cin bashin bankuna don su rayu, irin yadda ake ci a zamanin yanzu kamar yadda ake cin dussa, wai don biyan bukatun yau da kullum wadanda ba masu karewa bane. Ga daukar zunubin kudin ruwa. Shiyasa zaka ga duk tsananin talauci a lokacin iyayenmu basa cikin fargaba da zullumi, irin wanda tunanin bashi ke haddasawa magidantan yanzu, mai haifar da cututtukan kwakwalwa irin na damuwa da akeyi a zamanin yanzu wanda yake yiwa magidanta illa. Hakan ya faru ne sakamakon cewa kowa yana da abin yi daga (sana'ar data karbe shi), ta kuma ishe shi rufawa kansa asiri, da biyan bukatun sa na yau da kullum batare da ya ci bashi ba. Kuma ba tareda yayi rayuwar dage ba. Kusan kowanne mutum a cikin Badalar birnin Kano da kewaye (kauyuka da kananan hukumomi) yana rayuwa ne daidai shi kuma cikin farin ciki, yalwa da wadatar zucci, domin kullum cikin sa a koshe yake da *Gurasa* Tuwo, Dumame, Kunu, da Koko da Kosai (manyan abincin Kanawa). A takaice, ko da a ce kai ne beran masallaci sabida talauci a zamanin can da nake yarintata a gaban Innata da Babana, zuwa balagata (‘yammatancina) nayi rantsuwa bazaka rasa abincin da zaka ci sau uku a rana ba. A kullum ranar Allah tunanin Babana wanda anan unguwarmu ake kira "Baban Hauwa, dama na kowanne magidanci kamarsa na jama'ar dake zaune cikin kwaryar gidajen Badala da ganuwoyin garin Kano, shine; na yadda gobe idan garin Allah ya waye, karfe nawa zai yi sammako ya fita kasuwa ko wajen sana’ar sa?? Ba kuma don komai ba sai don samowa cikinsa dana iyalinsa abincin da zasu ci a yinin ranar. Kowa ya san a lokacin fiye da rabin Kanawa yan kasuwar saye da sayarwa ne. Wannan ne yasa ba'a kwana ana jin yunwa, sannan za'a wuni a koshe. Kuma ba'a tara komai a banki ba, sannan hakan baisa sai an ci bashin kowa ba. Duk da hakan kuma ana zaune lafiya cikin farin ciki. Wannan ita ce hakikanin rayuwar da ake yi a gidanmu. Ina farawa da baku labarina ni HAUWA_KULU tun daga tushena, ta hanyar dora shi akan katangar zamantakewar gidajenmu na Kanawa, wadanda aka fi sani da 'yan kwaryar BADALA, yanayin rayuwar iyayenmu na cikin Badala wata irin rayuwa ce irin mai ban sha'awa ga wanda ba Bakano ba. Rayuwa ce wadda bako zai tafi gaba ya bada labara, tunda an ce wai Allah daya gari bambam. **** **** **** GIDAN MALAM BILYAMINU T sakar gidanmu mai fadi da yalwa ne sosai, irin ginin nan ne tun na 70s wato ginin Kanawan zamanin da, Gidan namu yana nan a bayan tsohuwar Badalar nan mai tsohon tarihi daga cikin Badalolin Kano, wato bayan Badalar Kofar Naisa, a lokacin nan ni Hauwa-Kulu, zan kimanta shekaru na da cewa ina yar shekaru goma. Yalwataccen gidan namu duk da cewa a can cikin surkukin lungu yake, wanda ainahi mahaifina Malam Bilyaminu ya gaje shi ne shida dan uwan sa Malam Zakari, daga baya rigima ta hada shi da Zakari a kan gidan, wadda har ta kaisu gun mai unguwar kofar Naisa, aka ce zaaje kotu, inda mai unguwa ya hana, ta hanyar kawo shawarar bai kamata su je kotu alhalin sun fito gida daya ba akan abin duniya kararre, duk da ya san cewa Zakari ne mara gaskiya, don so yake ya gaje gidan shikadai, mai unguwa ya kawo shawarar daya ya sayarwa daya gidan, don a samu maslaha a tsakanin su. Don ya gaji da rabon fada tsakanin Bilyaminu da Zakari akan gidan gadon sunnan. Don haka Zakari ya sayar masa da gidan, don a lokacin babu ta yi masa yawa yana neman abinda zai ja jari ne, kudin yafi bukata ba wai gidan ba shiyasa yakeso a sayar. Don haka gidan ya zama mallakin Malam Bilyaminu shi kadai bisa shaidar mai unguwa da makwabtansa, bayan ya biya shi kudaden da ya yanka masa da kansa, ko kusa bai zaci Bilyaminu zai iya biyansa wadannan kudin ba, don haka yana karba ya bar masa unguwar, ya koma kofar Dan agundi da zama, inda ya sayi karamin gida a can da rabin kudin, ya cigaba da sanaar sa ta wankin hula. Malam Bilyaminu kuwa saboda kaunarsa da gidan sai ya kara gyare shi daidai bukatar kowanne talakkan badala. Gidanmu, gida ne na kasa da turbaya (gidan da aka gina da Laka), wanda aka bi aka sumunce shi tsaf da suminti, aka kuma shafe shi tas da farar kasa yayi haske gwanin shaawa. Tsafta da iskar shaqa sun wadace shi, kamar yadda tsaftar zuciya ta wadaci jamaar wannan gidan bakidayan su, wato Mallam Bilyaminu da matarsa Inna Safiya. A kowanne wayewar gari ko yammaci, zaka samu iska mai dadi da shiga jiki na kadawa a tsakar gidanmu, musaman a lokacin hunturu, wannan ya samo asali daga manyan bishiyoyin da ke girke a tsakar gidan tun ginashi, na darbejiya dana itacen umbrella, zaka ga reshen bishiyoyin dake tsakiyar gidanmu na rangaji, idan iska na kada su, busassun ganyaryaki na zuba a kas. Amma bazaka gansu sun bata tsakar gidan sosai ba, saidaima ka ga zanen tsintsiya da ya bi nan take ya share su, wanda ke nuna matar gidan, wato Inna (Safiya) wadda kowa ke kiranta da (Innar Hauwa), bata da kyuyar yin shara, abin nufi Innata jaruma ce wurin yawan kauda datti, koina ka shiga a gidanta zaka gan shi tsaf-tsaf gwanin ban kaye da dadin zama, kamar ba gidan dake cikin surkukin lungunan bayan Badala ba. La-shakka ko lomar tuwon ka ce ta fadi kasa a gidanmu, za ka sunkuya ka dau kayar ka, ka jefa a baka ka ci, ba tare da kyankyamin komai ba, duk da rashin sukunin aljihu na jamaar gidanmu wato iyayena tofa suna da wannan dabiar ta cikar Imani wato nazafah. Irin tsaftar da har ake cewa masu ita, ko suna da aljanun tsafta, ba Innar kadai ba, ba Malam din kadai ba har ni dake tasowa sun min wannan horon, kowannenmu ya rike tsafta irin ta malam bahaushe kai har ta zama symbol din gidanmu, bazaka ce ana kiwon dabbobi iri-iri a gidan ba, sabida yadda Innar Hauwa bata gajiya da share shi duk safiya da marece. Innata na kiwon dabbobin gida, tun daga raguna har awaki da tumaki, a can wani bangare na gidanmu da aka zagaye da langa-langa. Da zarar awakin sun fito daga garke sun sakar mata shi a tsakar gida ko a can garken nasu zaka ga tabi ta share. Sau tari zaka samu yayan bishiyar nan ta Umbrella yellow sharr dasu sun zubo a tsakar gidan mu, don haka yaran unguwa da yawansu da sassafe kafin su tafi makarantar boko suna yawan shigowa rokon Inna Innar Hauwa Umbrella ta fado? Nan zaka ga Innar Hauwa ta debo wankakkun yayan umbrella ta babbasu, su yi godiya su tafi suna ci da murna da farin ciki fal a fuskokin su. Yayan bishiyar (umbrella fruit) sunada farin jini a wurin yaran cikin Badala sabida zakin dandanon su. Yadda bishiyoyin suka yiwa gidanmu rumfa da manyan ganyaryakinsu zai matukar baka shaawa, domin ya koma tamkar wani dan karamin lambu, bishiyoyin sun samarwa mamallakan gidan wadattacciyar inuwar hutawa musamman a lokuta na

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});