Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 6

Chapter 6

Hauwa Kulu Book 1 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da kan sa sai kaga yana washewa. Daga nan kuma sai labari ko ba a saka masa maganin komai ba. Don haka babu wani mataki da Innar Hauwa ta dauka baya ga tunanin cewa in an kwana biyu idon zai washe dan kan sa, kamar yadda yake yiwa 'ya'yan kowa. Ciwon idon ya ritsa dani Hauwa-Kulu ina yar shekaru goma sha biyu da haihuwa. Aji biyu na karamar sakandire a GGSS Shekara. Wasa-wasa abin da ake zaton kwana biyu ko uku zai washe sai gashi ya dauki wata biyu ba abinda ya canza, sai ma idon ya koma ya cabalbale da kwantsa ba kyawun gani, ko buduwa baya yi idan gari ya waye wato na tashi daga barci, in kai mai kyankyami ne kaga idona a lokacin bazaka iya cin abinci ba, kullum kuma ciwon karuwa yake ta yi kamar ana rura shi maimakon ya ragu ko yayi sauki, na kan cewa Innata idan na yi sujjadah ji take kamar kwayan idon zata zazzago (fado kasa). Daga baya idon ya koma tsiyayar da ruwa da hawaye ko buduwa ya daina yi sosai, yayi jawur yayi luhu-luhu gwanin ban tausayi. Innata, wato Innar Hauwa na daga cikin mutanennan yan gargajiya da a rayuwar su basu bada yarda da maganin asibiti ba, kai ita ko sunan likita ta ji an ambata sai ta yi tsaki, don haka kullum saidai ta gasa min idon da ruwan zafi da dan gishiri, ta rambade min shi da farin kwalli, in yi ta kuka don azaba, wanda hakan yasa ciwon idon kullum sai karuwa da cigaba da taazzara yake ta kara yi. Watanni uku da fara ciwon, idon ya rikide ya koma min wata kebantacciyar cutar idanu da ake kira hakiya’ (cataract) ta fito ta kwanta tayi babakere a tsakiyar duka idanun guda biyu. Lokacin ne hankalin Innata ya fara tashi, ganin wadannan Hakiya cikin kwayar idona sun fara girma, kowa ya ganni sai yayi fadan don me Inna ta ki kai ni asibiti? Meyasa ta bar idon ya zama haka? Ayi ta mata fada kamar a ari baki. A kuma gaya mata ai Innar Hauwa hakiya baa wasa da ita fa”. Amma Inna tayi funfurus. Sai da ta kai na daina fita don zuwa makaranta don fadan da malamai ke yi akan a kaini asibiti amma Inna ta ki ji, sai cewa take ai tana saka min farin kwalli shine babban maganin ciwon ido, a hankali zai tsotse hakiyar gabadaya, amma ina! Abu kullum kamar ana kara iza shi. Har sai da ta kai ta kawo idanuwan nawa gabadaya sun yi fari tas, sabida yadda hakiya ta mamaye su. Yau muna tsakar gida ina zaune bisa tabarma da littafin makaranta a hannuna, ba tun yau ba na fahimci na daina ganin abubuwa da kyau, yadda suke a zahirin kamanninsu, amma duk da haka na dage ni a dole karatu zan yi wanda ya wuce ni a makaranta, duk da idanuna dake neman zagwanyewa yau don zafi, amma me? Ko da na bude cikin shafukan takardar sai na ga bana banbance duk wani rubutu dake cikin littafin sai hasken takardar kadai. Sai wasu taurari suna gilmawa ta gaban idona. Wannan ya tabbatar min, kodai ganina ya tafi, ko yana gab da tafiya ya barni. Cikin tsorata da alamarin na kwalawa Innata dake madafi tana kwashe tuwo kira, nace, Inna ki zo, watakila fa Inna NA MAKANCE!!! Inna na daina ganin komai a cikin littafi na komai ma bana ganewa. Mummunar faduwar gaban da ta samu Innar Hauwa a wannan lokacin bata taba jin irin ta a rayuwar ta ba, ko lokacin data gane batan Baban Hauwa, da sanda aka shigo mata da gawar Zulkiflu daga rafi. Watakila sabida son da take wa Hauwa ne, ko kuma don ta saka buri mai girma a kan Hauwa a ran ta??? Burin ta na Hauwa ta yi maza ta girma ta aurar da ita, burinta na HAUWA ta zamo mai zurfin ilmi a rayuwa, irin wanda basu samu damar yi ba su, itada Malam, kuma basu da wasu yayan da zasu yi shi bayan ita, burin ta na Hauwa ta samu kwakkwaran abun yi da zai rike su a tsufanta nan bada jimawa ba, koda ta zama malamar makaranta ne. Ta kuma yi aure ta hayayyafa, yayan ta su maye mata gurbin yaya masu yawa da Allah bai bata ba a rayuwar ta? Ko kuwa don ita kadai ta rage mata matsayin sanyin idaniya a halin yanzu, amma ace yau idanun ta babu? Ba karamin fadar da gabanta hakan yayi ba. Sai Inna ta bar abinda take yi, ta taso zani na kwancewa ya kusa faduwa ya barta, ta yo kan Hauwa da gudu, tana ambaton "bana son fatan tsiya HAUWA. INNALILLAHI WAINNA ILAIHI RAJIOUN. **** **** **** Wannan shine labarin da Barr. Hauwa Bilyaminu ta bayar a safiyar yau a dakin taron da aka hada mata na 'meet and greet,' tsakanin ta da kungiyoyin da take da alaqa dasu, kungiyoyi ne da suka tsayawa rayuwarta har ta kawo wannan matsayin, da sauran masoyanta mutanen arewa wato masu nakasa iri daban daban maza da mata wanda yau yayi quenching curiousity da jita-jitar kowa cewa HAUWA BILYAMINU IS A PHYSICALLY CHALLENGED PERSON. Kuma a ranar ne Hauwa take murnar cika shekaru hamsin da haihuwa, sannan a ranar ne ta karbi jagorancin Nigerian Bar Association. Wanda yayi daidai da ranar anniversary din aurenta da "HER PACE-SETTER..." shekaru dai-dai har talatin da daya. Barr. Hauwa Bilyaminu Kofar Naisa, ta bamu labarin asalinta da tushenta ne a wannan muhimmiyar ranar mai tarin achievements a gareta daga hakikanin bakinta, da asalin lalurar ta. Daga nan na kasa hakura da jin me ya faru da sauran rayuwar HAUWA-KULU? Ni Sumayyah Abdulkadir (Takori) na bibiyi labarin Barr. Bilyaminu bayan taron nan, zan kuma labartawa Takorites labarin HAUWA-KULU daga ranar data rasa abu mafi muhimmanci ga rayuwar bil adama har zuwa yau da take bikin murnar zagayowar cikar shekarun haihuwarta hamsin a duniya. **** ***** ***** M afarin makancewar Hauwa-Kulu kenan. Makanta mai sunan hakiya da akafi sani da (cataract blindness), ko a ce makanta mai lasisi, tunda kuwa Innar ta ce ta sayo mata da kudin ta. Don da farko Inna ta dauka Hauwa wasa take yi, amma cikin kwana biyun da Hauwa ta koma lalube da tsakar rana ko da daddare ta fahimci cewa Hauwa da gaske take, tana gab da daina gani, amma dai tana ganin haske da inuwar mutum in ya tsaya a kan ta, dan ko daki sai da lalube take kai kan ta, ko Innar ta kama hannunta ta kai ta don kada ta buge goshi. Saboda haka ne wannan karon Innar ta tsorata. Dole kanwar na ki, ta tambayi inda zata kai Hauwa aka ce mata ta kaita bangaren ido a Murtala (Murtala Mohammed Specialists Hospital), washe gari tasa ta a gaba sai asibitin Murtala. Da tambaya suka isa bangaren ido, a kafa suka tako suka taho tun daga kofar Naisa har zuwa bakin asibitin Murtala. Kusan wannan shine karon Inna na uku da zuwa asibiti a rayuwar ta, sauran biyun duk dubiya ta zo, don ita ba mai yawan ciwuwwuka bace sabida yadda ta tsaya da shan magungunan gargajiya da jike-jiken saiwoyi akai-akai bata yarda tayi wasa da su,

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});