Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 13

Chapter 13

Hauwa Kulu Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

su bi jami tare, ba zasu shigo gida ba sai bayan laasar. Amma sabanin kullum yau har aka idar da sallah bai ga Sarham ba. Wannan abu ya dugunzuma shi, don ya jima rabon da yaga ranar da yana gida bai je masallaci haka kawai ba. Mama ta gaya masa yau sun rasa gane kan sa, ya shigo cikin damuwa daga wajen aiki, ya kulle kan sa tun dazu, har ya kusa dukan Sumayya da ta dame shi sai ya bude ya dauki abinci. Bata kai ga rufe bakin ta ba sai ga Dr. Sarham ya fito daga dakin sa da saurin sa da hanzari, da mukullin motar sa a hannun sa, tun kayan dazun ne a jikin sa bai canza su ba, (which was unlike him) ya wuni da kayan da ya je asibiti dasu, idanun sa duk sun tasa kamar na wanda ya yi kuka ko ya kwana ido biyu da nannauyan barci. Ya gaida Daddy da Mama cikin sauri zai wuce, sannan kafin a yi masa kowacce tambaya Sarham ya kama hanyar fita, sai da ya kai bakin kofa sannan yace musu zai koma asibiti ya dawo yayi mantuwa ne ba jimawa zai yi ba. Ya kara da cewa kada su damu ba wani abu ne ya same shi ba, lafiyar sa kalau. Ya dubi Sumayyah yace ki je ki dauke farantin da kika tokaremin kofa da shi. Daga haka ya fice. Duk suka bishi da ido har ya fice daga main falon, sun kasa dakatar da shi. Yana tafe cikin yar karamar motar sa Honda Prelude ta yayin samari yan gata mai kofa daya, wadda Abba Prof. yayi masa kyautar ta, bayan kammala karatun sa da dawowar sa gida daga kasa mai tsarki matsayin cikakken likitan ido (at a very young age), yana tafe yana tunanin makasudin sake fitowar sa daga gida yanzu menene? Tunani kawai ya yi bai kamata ya bar Hauwa da Innar ta su tafi gida ba su ko yi sallama ba, don haka ya baro su a asibitin dazu (absent-minded) ya tafi gida don ya samu nutsuwar ran sa, bayan sallamar da asibiti yayi musu a yau (wato discharge). Son samu ma ya tambayi inda suke, don watan watarana. A fahimtar sa dai, idanun Hauwa ya gama tafiya kuma ta sanadin sa. Wannan tunanin kadai yana matukar daga hankalin Dr. Sarham kamar ba likita ba, yana kuma azabtar da zuciyar sa, kasancewar bai taba aikin da bai yi nasara ba sai wannnan karon kan na Hauwa, shi ko kiyashi baya so ya ji rauni a hannun sa, watakila don wannan ne karo na farko da yayi aikin cataract ya kuma fara da rashin nasara. Har ya iso asibitin Murtala yana share zufa daga kan goshin sa da farin hankacin sa, da zara-zaran yatsunsa. Ya karya kan motar zai shiga asibitin kenan sai ya hango Innar Hauwa dauke da dan kunshin kayansu a kan ta, ta kamo hannun Hauwa suna fitowa daga cikin asibitin. Don haka da hanzari Sarham ya juya kan motar sa zuwa inda ya hange su, yayi gaba da su kadan ya tsaya, sannan ya fito daga motar ya nufe su. Inna har kun fito ne? Sarham ya fada da karyayyar muryar data idasa karyewa a wannan lokacin, idanun sa fal kulawa da damuwa, bayan ya fito daga motar sa, ya maida kofar ya rufe ya tako a hankali zuwa inda suke a bakin titi suna jiran motar haya. Da fara Inna ta amsa Mun fito likita, zamu taka zuwa gida, gashi har ka je gida ka dawo bamu tafi ba muna kailula don tun dazun anka sallame mu. Kulu ce ta ce in bari ta kara jin karfin jikin ta bazata iya doguwar tafiya a dazun ba. Idanun Sarham fal damuwa, ya daga ido ya dubi Hauwan, ga idanu tar a bude, manya dasu, masu haske kamar an wanke su an kuma kara musu lafiya, unfortunately sun koma gululu, kuma ta sanadin aikin hannun sa, sai jujjuyawa kawai suke a kan titi. Shin ta yaya zai yi ya daina damuwa a kan aikin nan da yayi ba nasara? Naturally shi mutum ne mai phobia na gudun zuciyar mutanen da yasan ya batawa, yawan tausayi ga marassa lafiya da masu karamin karfi, balle ga mata da kuma kananan yara. Shiyasa kannen sa mata biyu ke tsananin jin dadin sa da kaunar sa, saboda kulawar sa garesu. Sai ya saka hannu ya karbi kullin kayan su da ke kan Innar Hauwa, ya ce ku yi min alfarma Inna in raka ku zuwa gida, ko don in ga wuri. Ni dan ki ne, wace unguwa kuke? Inna ta ce cikin mamaki anya dan nan ma saka ka wahala haka? Can muke da dan nisa, a can bayan Badalar kofar Naisa. Tuni kafin ta gama fada Sarham ya isa ga motarsa ya saka kayan nasu a bayan motar, ya budewa Inna da Hauwa kofar gidan baya. Babu komai Inna, don Allah ku shigo in kai ku. Inna bata da zabi ban da kama hannun Hauwa ta shigar da ita bayan motar, don ta kasa tankwabe tasirin da kirkin sa da kamalar sa da jin kan sa yayi a ranta. Dr. Sarham ya shigo ya tada motar ya juya ta suka fita daga asibitin Murtala gabadaya. Ba jimawa suka hau titin da zai sada su da Kofar Naisa. Suna tafe a hanya Inna na nuna masa inda zai bi da su, lokacin da suka shiga cikin Ganuwa. Hauwa dai bata cewa ko uffan, abinda ya dameta ya dameta, tana dai jin su jefe-jefi suna hira shi da Inna a kan ta. A surutu irinna Inna har tana gaya masa wai Hauwa yar makaranta ce, tana aji biyu na sakandire a GGSS Shekara, ta yi jarrabawar shiga aji na uku yanzu, suna zaman jiran fitowar ta (jarrabawar) Hauwa ta fara apolo. Can kuma ta nisa tace, umh! Yanzu kuwa Hauwa-Kulu ai sai zaman gida ko? Tunda dai idanu sun tafi?. Ta yi maganar cikin wata irin murya kamar mai neman amsa daga gare shi, a lokacin da bawa ya rasa abinda ya kamata yayi akan wata babbar masala data tunkaro shi ba shiri. Dr. Sarham yayi shiru, yana cigaba da tukin mota, bai ce komai ba don duk wani blame na makancewar Hauwa ya rasa me yasa ya daukeshi bakidaya ya dora shi a kan sa, bayan kuma ba haka aikin likita ya gada ba. A kaidar aikin sa bashi da laifi. Amma a humanity da dattaku irin nasa ji yake shine sila, shine cause kuma shine at fault. Daidai lokacin suka iso lokon gidan su Hauwa. Daga inda mota bazata iya shiga ba, Inna ta nuna masa inda zai iya aje motar ta ce sun gode zasu karasa da kan su a kafa daga nan, don gidan na su can cikin loko ne mota bata kaiwa. “Inna ai har gida zan kai ku, bani kayan in rike miki, zan so ganin gidan naku don watarana in dinga gaishe ki, ina ganin lafiyar idon kanwata. Inna ta ce to likita muna godiya kwarai, kamar ka san bata da dan uwa. Allah ya yi albarka ya baka masu yi maka kai ma. Daga haka Inna ta wuce gaba Dr. Sarham ya bi bayan ta zuwa cikin

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});