Chapter 19
Chapter 19
yake cewa ya makantar daga kuskuren aikin ido. A kunnen sa yaji Sumayyah ta rada masa cewa. Tabarakallah-masha Allah, Subhanallah Ahsanal Khaliqeen da wadannan idanuwa na Hauwau. Bhaiya, ashe dai Hauwa-Jidda beauty ce, irin kalar dana ke so na koma (kasancewar Sumayyah fara ce tas). Sarham ya juya ya galla mata harara don ya ji ta sarai. Yace wallahi zaki koma yanzunnan in baki yi min shiru ba”. Inna ta leko jin maganganun su tana maraba da bakuwa, nan da nan ta saki fara tace Sumayyatu ce ko? Sumayyah ta washe baki jin farad daya Inna ta kama sunan ta, ko da wannan ta san tana da matsayi mai girma a gun Bhaiya, tunda har wadanda yake muamala da su sun san da zaman ta. Ta ce ni ce Inna ina wuni? Inna ta bata shimfidar karaunin ta ta zauna, inda Hauwa ta tashi, a lokacin ta gama alwalarta ta juyo tana tafe zuwa inda suke kanta tsaye babu ko lalube, tsabar ta dade da sanin kowanne lungu da kowanne sako na gidan su. Sumayyah ta kamo hannunta ta zaunar da ita a kusa da ita, cikin girmamawa Hauwa tace da Sarham Ina wuni likita, yaya aiki? Ya dan dubeta kadan kafin yace an gode Allah Maijidda, ga Yayarki Sumayyah na kawo miki Sumayyah ta saka hannunta cikin na Hauwa, sai Hauwata rike hannayen nata sosai a cikin nata tana murmushi tace sannu da zuwa. Basu jima suna hira ba Inna ta kammala girkin ta na dambun shinkafa da yaji zogale da soyayyen mangyada ta zubo musu a kwano guda, sannan ta zubawa Sarham yadda ta saba zuba masa a kwanon sa da ta ware masa na samira wanda sabida shi ta dauko shi daga cikin samirunta, shikadai take zubawa abinci a ciki. Ga yaji da yaji tafarnuwa a gefen abincin. Kamar ta san shi da son tafarnuwa, Sumayya ta hadiyi miyau tun kan ta kai loma abincin ya gama yi mata, sannan tsaftar masu gidan ta gamshe ta. Hauwa kasa cin abincin tayi da Inna ta hada musu itada Sumayyah don bata sakewa da baki amma Sumayyah sosai take kai loma, nan da nan ta tashi da dambunnan. Shima Sarham tuni ya tada nasa sai kwanuka aka direwa Inna. A ranta Sumayya ta ce eh, wato dole Bhaiya yayiwa abincin gidan su kaura, yana nan an gargajiyantar da shi da wannan girki mai motsa kunnuwa. Basu jima ba sosai don zasu gidan Hajiya Kulu, Sumayya ta baiwa Hauwa sayayyar a hannun ta inda ta saka mata ledojin a cikin hannun ta ta ce, ga nan gift dinki ne inji Bhaiya, ki cigaba da dauko na daya kin ji Hauwan Inna, shi kuma yayi ta kawo additional gift, duk karshen shekara. Murmushi Hauwa tayi, tana shafa kayan da ledojin, murmushin na karuwa a fuskar ta, kanta a kasa ta ce kice masa nagode, Allah ya saka da alkhairi, kema na gode da ziyara Anti Sumayyah. Bayan fitar su da kadan itada Inna shiru suka yi. Hauwa tace Inna ni bazan taba komai ba, don bana son abinda zaa zo ace muna kwadayi. Inna tace to ban ki ta taki ba Kulu, amma shima ya san bamu kwadayin komai nasa tunda baki roke shi ba kuma ba yau ya fara ba, saidai na yau nima ya tsorata ni, don kayan sun ci kudi da yawa da alama. “To Inna ki ajiye ni dai bazan taba ba Inna tace “tsahon shekara guda kenan muna tare da yaron nan, in da wata manufa a tare da shi ko da wani hali nasa mara kyau zuwa yanzu ya kamata in sani, to ban taba gani ba sai tarin alkhairi da nagarta a tare da shi. Alheri da kyauta wannan na lura halin sa ne na halitta kawai. Don haka ni mahaifiyar ki Safiya na ce ko bayan raina duk abinda Sarhamu ya dauka ya baki da hannun sa ki karba da godiya, ki kuma yi amfani da shi da zuciya daya, wannan yaron bashi da wata manufa akan mu sai zumuncin Allah da ya saka kansa tsakanin sa da mu, don bazan ce wani ne ya saka shi ba ko don neman wani abu daga gare mu”. **** **** **** A cikin mota suna kan hanyar zuwa gadon kaya, Sumayyah ta kasa shiru, abubuwa da yawa sun tsaya mata a rai game da muamalar Sarham da gidan su Hauwa, babu tudu me ya kawo gangare? Ta saci kallon Bhaiya, wanda ke tukinsa hankalin sa a kwance, ta ce, Bhaiya, ina da tambaya, if you permit, may I ask? Tsakani da Allah son Hauwa kake yi? Wani irin wawan burki da Sarham ya ci da motar, saida dukkan su suka wuntsulo gaba, suka kusa ci da baka a gaban motar. Saura kadan ya kwadawa Sumayyah mari, domin ji yayi kamar ta yi sabo, amma ya daure ya rike hannun sa yana cewa ba zai taba dukan mace a rayuwar sa ba in sha Allah, balle Sumayyah, da yafi so duk gidan su, kowacce irin katobara zata yi masa kuwa, ba shiri Sarham yayi parking motar a gefen titi. Cikin matsanancin mamaki da fushin da yake so ya danne yake kallon kanwarsa, yace da Sumayyah ke kuwa me ya kaiki wannan tunanin mai kama da sabo? Sumayya sakewa ta dake har ta kai da ki raina ni irin haka? A duniya mutum bazai yi wata kyakkyawar alakar mutunci da zumunci da mutanen da ya san darajar su, suma suka san tasa ba, kuma yayi sanadin janyo musu lalurar da basu da yadda zasu yi da ita sabida raunin su, da rashin namiji tsayayye a cikin rayuwar su, mutum bazai yi tunanin taimaka musu da faranta musu domin Allah ba sai don wannan shirmen? Sumayyah idon ta ya raina fata da ganin bacin ran Sarham karara, ta ce kayi hakuri Bhaiya, ba raini bane hasashe na ne dana kasa dannewa a rai na, na yi laakari ne da maganar Hausawa da suka ce in kaga kare yana sunsunar takalmi… dauka zai yi.”. Da sauri Sarham yace amma kuwa Allah wadaran wannan bahaushen da a wajen sa babu kowacce alaqa ta mutunci da taimako a tsakanin alumma sai da manufa, babu kyautatawa mara galihu sai a dalilin wani shirmen banza wai SO!”. Yana fadi yana tada motar, da gaske a gareshi so shirme ne, don baiga ranar da so yayi masa ba. Yana tukin yana maida numfashi, fuskar MADINAH ATTAHIRU na gilmawa a idanun sa. Itace silar bacin ran sa ba maganar Sumayyah ba, ita tayi fami ne akan gyambon da aka samu yayi healing ba tare da ta sani ba. Sumayyah jikin ta har rawa yake ganin yadda jikinsa har tsuma yake, ta ce don Allah don Annabi kayi hakuri Bhaiya, ni tambaya kawai nayi bansan ranka zai baci haka ba, kayi hakuri bazan sake shiga abinda ba ruwa na ba. Sai kawai ya fizgi motar ba tare da ya kara ce mata komai ba, amma ya fasa kaita gidan Hajiyar Gadon kaya, kofar gida ya maida ita wato can gidan su, New Site. Tun bai gama tsayawa ba da motar yace, fice min daga mota malama, daga yau bazan kara fita da ke koina daya shafeni baba, uwar kaudi uwar tsugudidi, fadi baa tambaye ki ba.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31