Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 27

Chapter 27

Hauwa Kulu Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

bata shayin a baki har ta koshi, ta debo naman da zafin sa a faranti irin gasashshen naman nan ne na babbar tukuba mai ruwa-ruwa wanda da kasa a bakin ka ka tauna zaka ji ya baje tsabar laushin sa, wanda yaji yajin citta, Hauwa duk da jikin ta na ciwo taji dadin cin naman nan, don baza ta iya tuna yaushe rabon ta da cin nama ba, tun zamanin Likita Sarham na zuwa gidan su! Balle mai dadi da laushi irin wannnan ai sai zamanin Dr. Sarham. Daga nan ta koma barci har dare bata tashi ba, Inna ta sallami Salele ya tafi gida bayan ta masa sautun abubuwan bukata da zai zo musu da su washegari har da filas din ruwan zafin su da hita. Washegari yan dubiya fululu daga kofar Naisa, Salele ya barabada musu mota ta kade Hauwar Inna. Hauwar Inna mai jamaa kowa na son ta, koda makanta ta same ta jamaar unguwar su kowa kokari yake ya kyautata musu, musamman da aka san mahaifin ta ya bata, kuma Innar ta bata da matallafi sai Allah. Makwabta na ta tururuwar zuwa duba Hauwa kullum, koda Inna ta aika Salele don ya fada a makarantar su Hauwa kada aga bata zuwa, sai ga Malaman su Hauwa sun yo kungiya a motar makarantar su a washegari daga ‘special school Kano’, suka zo suka duba ta da kayan dubiya niki-niki, kasan yaro mai kokari da shiga ran malamai. Don haka a wannan jinya su Hauwa sun samu alheri sosai, don Jamilu ma kullum yana tafe, abin arzikin da zai kawo na yau daban na gobe daban. Tun Inna na daure masa fuska tana korar sa a wayance, har ta fara gane Jamilu neman shiri yake yi sosai dasu, rannan ya kawo dafaffen abinci yace mata inji Hajiyar sa, da yake bata gidan mahaifin sa ita kuma tare suka yi yanmatanci da Inna, kusan lokaci daya Bilyaminu da Zakari suka aure su. Ta manta rabon ta da Rumanatu don tun Jamilu na yaro Zakari ya aunata gaba. Daga baya ma ya dauko Innar tasa ya kawo dubiya, nan suka baje ita da Inna a kan tabarma ana labarin yaushe gamo da tuna baya. A bakin Hajiya Rumanatu Inna ta ji cewa Jamilu yayi karatun shi mai zurfi har digiri a hannun ita mahaifiyar shi a boye, ba tareda Baabnsa ya san yana yi ba, tace yanzu haka Jamilu aikin Banki yake da bankin Afrika (United Bank of Africa) da akafi sani da UBA. Kuma da wannan aikin har yana taimakawa kannensa sosai da suke garari da gararramba a gari, matan yawanci an sako su suna gidan uban suna zawarci, tace yayan Zakari mata basa jimawa a gidan miji zaki ji an sako su, uban duk kudin da ya tara baya iya saya musu ko gasarar koko, sai dai ya je tukubar mai shayi a lafta masa kwai da shayi mai kauri, ta ce ai ita kam Allah ya cece ta da ya raba ta da gidan su Jamilu. Ta shiga lissafo wa Inna yawan matan da Zakari ya aura bayan ita yana shika musamman bayan yayi kudi abun babu ko dadin ji. Tace bayan rabuwar ta da Zakari ta yi aure ta haifi wasu yayan mata guda biyu Hansatu da Lami, duk ta aurar dasu. Shekarar baya Allah ya yiwa mijin ta rasuwa wanda ya rike mata Jamilu kaamr shi ya haife shi. Har yamma kafin Jamilu ya zo daukar Hajiyar sa, suna tafe a hanya Hajiyarsa na bashi labarin irin mutuncin Inna Safiya tun suna yammata. Jamilu ya sosa kai, da damuwa yace. Hajiyata ina da magana, tuntuni, amma ina shakka, kin ga ba don halin Baban mu ba da illar da ya yiwa mutuncin mu gun Inna Safiya ba, me zai hana na auri Hauwa? Da ba sai kawai a yi yar gida ba ni da Hauwau? Rai kwance hankali kwance?” Hajiya Rumana ta ce cikin mamaki wai kana nufin kana son Hauwa din ne? Jamilu ya koma sosa keya da hannun sa daya yace gaskiyar maganar kenan, Hajiyarmu tun ranar da na buge ta, nake fama da zuciyata a kanta, zuciyata bata kara zama lafiya ba a kan tunanin yadda zan yi na mallake ta, kullum tunani na shine yadda alamarin zai yiwu cikin sauki, amma na hanga na duba ta bangaren Babanmu na tabbatar zan samu matsala sosai da shi. Jiya na je gaishe shi, na same shi na gaya masa tsautsayin da ya gifta na kade Hauwa, cewa yayi tun da na kaita asibiti na biya magani kada ya kara jin na koma inda suke. Haj. Rumanatu ta ce umh, ni na rasa irin wannnan yan ubanci da yake yi wa dan uwan sa, shikadai ya rage masa amma ya kasa kaunarsa, wallahi shi bai dauke shi haka ba Bilyaminun, baka ga irin cin kashin da yake masa ba, haka yake masa tun suna yara saboda bakin cikin ya fi shi samu a sanaar sa ta gwanjo. Kaima dai Yayan Hansatu banda kana son taro aradu da ka, ba zaka kaiwa mahaifin ka wannan maganar ba. Jamilu ya ce (with boldness) idan har Hauwa ta amince min in sha Allahu zan yi nasara a kansa. Hakan ne kadai zai gyara wannangurbataccen zumuncin ya rage kiyayyar idan mun haihu nida Hauwa. Ta ce “to idon ta fa? Zaka iya zama da makauniya Jamilu? Ba wai ina kin Hauwa bane saboda lalurar ta, tunda kuwa yar uwar kace jininka ce, amma akwai abun dubawa. Tarbiyyar yaya, dawainiyar cikin gida, abubuwa ne da sai mai ido zai iya yin su. Da aikin banki zaka ji, ko da kula da nakasassar mata a cikin gida musamman in ta fara haihuwa? Kaida in ka fita tun sassafe wani zubin sai dare kake tasowa? Don kuwa Hauwa, kasa a ranka in ka aure ta duk kai zaka yi mata wadannan abubuwan dana fada a can baya tana daga zaune tana fama da kanta. Jamilu ya nisa cikin jin karin kauna da soyayya da tausayin Hauwa, sannan ya ce Hajiyata, a irin son da na samu raina yana yi mata, sam ban hango wadannan kalubalen ba, amma ni Jamil Zakari naji na gani, na yarda in har zan samu auren Hauwa, zan hadasu duka ita da yayanta in raine su in kula dasu har aikin bankin duka bazan kasa ko daya ba. Hajiya Rumanatu tausayi ya cika ta, ta dade da sanin dan ta Jamilu mutum ne har mutum, mai kyakkyawar zuciya akasin ta mahaifinsa, ta dade tana dakacen dama ace Bilyaminu ne ya haife shi, saboda halinsa na yawan kirki da nagarta shiyasa ma mahaifin sa sam bai cika shiri da shi ba don komai nasu Allah daya ne gari banban. Sai ta ce Allah ya tabbatar da alkhari a tsakanin ku idan akwai, ya huwwace maka lamunin mahaifin ka cikin sauki. Auren Hauwa hakika Jihadi ne babba zaka yi, na gyaran zumunci da kuma na taimakon miskinin da baida maraba da maraya. **** **** **** An sallami su Inna daga gadon asibiti bayan an kwance karayar hannun Hauwa ranar wata lahadi, ta dauka shikenan sun rabu da jelen Jamilu. Amma ina! Ashe wasa farin girki, lokacin nema Jamilu ya maida gidan su wajen zuwansa. Aka ce in kaga kare

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});