Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 15

Chapter 15

Hauwa Kulu Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

zamo shine babban abokin sa (Abban), saboda gudun kada abokai su bata masa shi. Abba Prof. akwai saka ido akan tarbiyyar yaransa kamar baida wani aiki a duniya sai kula da su, sai ko abokanan aikinsa a Murtala, wadanda yanayin aiki kan hada su akan dole. Maman sa kan ce he is very anti-social, yet a parrot”, bashi da saurin yarda da sakin jiki da kowa, sai ko autar su Sumayyah, ko ita kan ta Maman ba komai yake iya gaya mata ba, da ya shafi sirrikan shi, amma tsaf zai iya gayawa kanwar sa Sumayyah komai su kashe su rufe ba tare da iyayensu sun sani ba. Babu shakuwa mai yawa tsakanin Barr. Maimuna da daukacin yaranta, wannan ya faru kasancewar gabadaya rayuwarta ta sadaukar da ita ga aikin ta na Lauya da zurfafa karatu, don haka su Sarham sun taso kusan a gaban Kakar su ne Hajiya Kulu. Sun fi shakuwa da Hajiyar Gadon Kaya fiye da Maman su, wadda a can baya a gidan su take zaune. Lokacin da aka maido Prof. cikin gidajen malamai na sabuwar jamiar Bayero sai Hajiyar Gadon Kaya tace ba zata biyo su ba, domin bazata iya zaman wajen gari ba, a cewar ta a cikin Badala aka haifeta don haka a kwaryar badala take so ta mutu a binneta, don haka Prof. ya samar mata mai aiki mai suna Gambo, ta zame mata abokiyar zama suke zaune tare a gidan sa na Gadon Kaya wanda mallakin sa ne da ya gina da gumin sa. Lokaci-lokaci yana sabunta shi zuwa ginin zamani irin na wancan lokacin daidai da yawan iyalin sa. Har yanzu Hajiyar gadon kaya na can amma ta tsufa ainun, sun yi sun yi ta dawo ta zauna tare da su ta ki, don haka kusan koyaushe kafar su bata rabo da gidan Hajiya musamman Surayyah, saboda yadda Hajiya ta shagwaba ta, kuma tafi jan ta a jiki duk cikin su. Wannan ya samo asali ne daga sanda aka haife ta bada jimawa ba Mama tayi wani dogon rashin lafiya mai tsanani na lokaci mai tsaho wanda yasa dole aka dauke Surayyah a nono ba tare da ta isa yaye ba, Hajiya ce ta cigaba da rainon ta a dakin ta da madarar yara har ta yaye ta, sai ta cigaba da zama a wurin ta har bayan da Maman ta samu sauki, aka zo aka haifi auta Sumayyah, amma Hajiya ta rike Surayyah, bata kara bari ta dawo wajen Maman su ba, saidai ta zo da yawo har girma. Ita kuma Sumayya dalilin shakuwar su itada Sarham ya samo asali da cewa kusan Sarham shi yayi rainon ta, domin akwai rata ta kusan shekaru goma sha biyu a tsakanin su. In Mama na wajen aiki shi yake kula da Sumayya su tafi makarantar islamiyyar sa tare, har zuwa sanda itama ta isa shiga makaranta, malamai na hanawa azo da kananan yara amma Sarham ba ya jin Magana, gobe sai ya dawo tare da kanwar sa, in har ba za’a bar shi ya shiga aji da Sumayyah ba tofa zai koma bayan tagar ajin su ne shi da ita su make su yi ta leke, korar duniya malamai zasu yi masa ba zai tafi ba, har suka gaji suka kyale shi yake zuwa aji tare da ita, don Mama bata da lokacin kula da ita. Inda Mama ta zama akasin Prof. Kenan, shi kam yanada lokacin yaran sa no matter what, yana jan yaran uku a jiki, daga yamma zuwa lokacin barci idan ya dawo daga cikin makaranta suma suka dawo makarantar islamiyya zai kasance tare da su. Ita Mama zaka samu ko ta dawo aiki zata ce ta dawo da muhimmin (case) a hannunta zata yi nazari, tace su zauna a falo kada su dame ta. A haka Sarham da kannen sa biyu mata suka rayu tsakanin yan bokon iyayen su. Sai ya zama cewa a girman su ma Surayya ta fi shakuwa da Kakar su, itada Sarham basa ga maciji, sai fadan sako da sakuwa, yayin da Sumayyah kuma tafi shakuwa da shiri da shi fiyeda Mama. Ya iso gida wajen karfe tara na dare. Jamaar gidan su dama ga aladar su karfe tara na dare na yi sun baje daga falo kowa ya nufi makwancin sa. Amma Abba na nan bai tashi ba, yana nan zaune a kujerar da yake zama a falon yana jiran ganin dawowar sa, yana sauraron labaran kasa da ake yi a gidan talbijin na NTA yana kuma duba tangamemen agogon dake like a bango. Sarham yayi sallama a babban falon mahaifin sa, inda Abba Prof. ya amsa masa, ya shigo ya zauna daga kasan kafafun Abban, ya ce Abba sannu da gida Abba yace yawwa, kai kuma sannu da yawon dare, daga ina kake haka? Ka bar yan kannen ka cikin damuwa, ka birkice musu wuni guda, me ke faruwa da kai yau? Sarham ya yi ajiyar zuciya ya ce Abba ina kofar Naisa, wata marainiyar yarinya na yi wa aikin ido, Abba cikin rashin saa zan ce ko kaddara ko tsautsayi ko gangancina ne ban sani ba, ta makance gabadaya, maimakon a samu lafiyar da ake nema. Muryar Sarham kamar zai fashe da kuka don damuwa, zaka iya karantar tsantsar karaya da sarewar da yake ciki a cikin sautin nasa. Prof. Abbas Shanono, ya dubi babban dan nasa Sarham cikin kulawa, yace haba Muhammad Sarhamu! Be a man mana! Sai kace ba likita ba? Da haka zaka cigaba da aikin likita kana karaya akan rashin nasarar aiki irin haka? Ai dama aikin likita ba a hannun ku yake ba, a hannun Allah yake, sai abinda ya hukunta ga marar lafiya. Never blame yourself a kan duk wani unsuccessful surgery. Ka sa a ranka ka yi iya yin ka, sauran, wato samun lafiya ko akasin ta, yana hannun Ubangijin halitta. Maganar mahaifin nasa ta dan kwantar masa da hankali, at least shi bai ce masa bai iya ba, bai ce don shekarunsa ba masu yawa bane, bai kuma ce laifin sa bane this is soothing, a hankali Sarham ya ce. Abba kuma shikenan idan yaro ya makance wato ya samu nakasar ido ba zai yi karatu ba sai ‘bara?’ Abba Prof. yace in ji wa? Ai akwai cigaba yanzu sosai akan ilmin masu nakasar ido, akwai makarantu na musamman da gwamnati ta bude domin koyar da su kyauta (public special schools) can ya kamata iyayen ta su kai ta, har anan Kano akwai special school dominyara mau nakasa daban-daban. Sai Sarham ya ji tamkar Abban sa ya bashi amsar ‘assignment’ din da ya baiwa kansa, ko yace Inna ta bashi, na yaya zai yi Hauwa tayi karatu, sannan kuma Abba ya bashi mafita akan damuwar sa kan matsalar Hauwa, at least zai iya taimaka musu da wannan wato ya tsaya a kan karatun ta, nan take ya yi wani kuduri mai girma ga zuciyar sa shi kadai; na daukan nauyi da takalihun alhakin ilmin Hauwa Blyaminu na sakandire har sai ta kammala in har yana raye, in dai da gaske makafi suna iya yin karatu da rubutu su samu ilmi kamar kowa, da yardar Allah zai tsayawa Hauwa, tunda shi ya samu yayi har gashi ya tsaya da kafafun sa yana kuma

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});